2025-08-10@11:17:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11
«wayar da kan jama a»:
Don haka, kwamishinan ya gode wa ƙungiyar bisa wannan ziyara tare da bayyana shirin Ma’aikatar na yin haɗin gwiwa da haɗin gwiwa ta fuskar horarwa, wayar da kan jama’a, da wayar da kan jama’a game da SGBƁ. Tun da farko, Misis Achimugu ta bayyana cewa ziyarar bayar da shawarwarin ita ce kashi na biyu na ci gaba da wayar da kan jama’a, da bayar da shawarwari, koyan fasaha, da kuma shirin tallafa wa jama’a, wanda wani ɓangare ne na dabarun yaƙi da cin zarafin mata (SGBƁ) a Jihar Kogi. Ta bayyana muhimmancin haɗa hannu da masu ruwa da tsaki, ma’aikatu, sassa, hukumomi (MDAs), ƙungiyoyi masu zaman kansu, da cibiyoyin gargajiya da na addini domin yaƙar matsalar SGBƁ, musamman a tsakanin...
Wani sojan Amurka ya ba da shaida game da kisan wani yaro da sojojin mamayar Isra’ila suka yi a cibiyar bada agaji ta Rafah Wani sojan Amurka da ke aiki a cibiyar rarraba kayan abinci a zirin Gaza ya yi furuci da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan wani yaro Bafalasdine da ya yi tafiya mai nisan kilomita 12 a karkashin zafin rana, don neman kayan abincin agaji a yankin. A cikin wata sheda mai ratsa jiki da ya bayar a cikin wani dan gajeren faifan bidiyo a Amurka, Private Anthony Aguilar ya ba da labarin wani lokaci da ba za a manta da shi ba cewa: Wani yaro siriri mai suna Amir, babu takalmi a kafarsa, ya...
A yayin da ‘yan sandan ke gudanar da bincike a yankin, rahotanni sun ce jami’an sun gano wata mata ‘yar Nijeriya a Coach A-2, Seat No. 27, tare da wani yaro da wata jakar balaguro kala-kala. Rahoton ya bayyana cewa bayan an yi mata tambayoyi, ta bayyana sunanta Doris daga Nijeriya kuma ta ce yaron da ke tare da ita, wanda ta bayyana sunansa Miracle, nata ne. RPF ta lura cewa “da aka yi mata tambayoyi a gaban shaidu masu zaman kansu, matar ta amsa cewa tana dauke da kayan maye.” Daga baya an kai ta zuwa gidan RPF a Panbel domin cikakken bincike. Rahoton ya lura cewa a cikin jakar balaguron, jami’an sun gano bakaken fakiti guda biyu da...
Hukumar ta NSEMA ta jagoranci gudanar da aikin, tare da tattara kayan aiki gami da tura kungiyoyin bayar da agajin gaggawa tare da hadin gwiwar hukumomin kananan hukumomi.’ Arah, ya bayyana cewa, kafin lokacin damina, hukumar ta NSEMA ta kaddamar da shirin wayar da kan jama’a game da ambaliyar ruwa a duk shekara a matsayin gangamin gargadin farko a ma’aikatun masarautu takwas, da nufin kara wayar da kan jama’a. “NSEMA ta kuma bayar da agaji ga wadanda gobarar gidaje da kasuwanci ta shafa a sassan jihar”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Wutar lantarki ta kashe wani wanda ake zargin ɓarawon wayar rarraba wutar ne a harabar Sabuwar Sakatariyar Jihar Jigawa. ’Yan sanda sun sanar cewa an tsinci gawar mutumin ta maƙale ne a karkashin kankare da manyan wayoyin lantarkin ke ciki. Kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, Shiisu Lawal Adamu ya ce a safiyar ranar Alhamis ne suka samu kira daga Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Jigawa game da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa tuni aka dauke gawar zuwa Babban Asibitin Dutse, domin gudanar da bincike.
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama aƙalla mutane biyu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, wanda suka hada da: Muntari Shu’aibu da Imrana Rabi’u. A wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu waɗanda ake zargin ɗauke da ƙunshi guda shida na miyagun ƙwayoyin Tramadol da aka ƙiyasta kuɗinsu ya haura Dala 92,000 (kimanin Naira miliyan 150m). Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe Gwamnan Kano ya kafa sabbin hukumomi 4 Bakori ya ce, “Rundunar ’yan sandan ta gudanar da wani samame ta hanyar fasaha da bayanan sirri, ta kama waɗanda ake zargin da wannan miyagun ƙwayoyin, biyo bayan wani rahoto da...
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna ta hanyar wayar tarho da takwarorinsa na Switzerland da Pakistan Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi wata ganawa ta hanyar wayar tarho guda biyu a yammacin jiya Lahadi tare da ministocin harkokin wajen kasashen Switzerland da Pakistan. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Switzerland Ignazio Cassis ta hanyar wayar tarho a yammacin jiya Lahadi, inda suka tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwan kasa da kasa tare da yin musayar ra’ayi a kansu. A yayin wannan tattaunawa, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana jin dadinsa ga rawar da kasar Switzerland ta taka a shawarwarin nukiliyar kasar cikin...
Bakori ya ce, makaman da ake zargin an dauko su ne daga jihar Filato, ana shirin kaddamar da wani mugun nufi ne acikin Kano da kuma jihohin da ke makwabtaka da ita. Ya kara da cewa, bisa ga sahihan bayanan sirri, jami’an sun kai samame a wata maboya da ke Kuntau da Gwale, inda suka bankado yadda kungiyar ke gudanar da muggan ayyukanta. A wani samame da jami’an ‘yansandan suka gudanar sun kama wata babbar mota makare da buhunan siminti amma kuma an boye kwalaye shida wanda ake zargin kwayar tramadol ce da kudinsu ya haura Naira miliyan 150. An kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu akan safarar kwayar da aka dauko daga Sokoto...
Domin tabbatar da bin bin doka da oda a tsakanin al’umma, ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta ce za ta fara wani gangamin wayar da kan jama’a na tsawon mako takwas. A cewar kwamishinan, gangamin zai mayar da hankali ne wajen wayar da al’umma, masana’antu, da sauran masu ruwa da tsaki kan sabbin dokokin da kuma muhimmancin kiyaye muhalli mai tsafta. Ya kuma sanar da cewa, za a fitar da dokokin a cikin harsunan Hausa da Ingilishi a cikin mako guda domin inganta yanayin fahimtar dokokin a tsakanin al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
Masu fafutikar kare haƙƙin bil Adama da ƙwararru a fannin kiwon lafiya haɗi da fasihai a ɓangaren shari’a sun buƙaci a tsananta hukunci kan masu yi wa mata kaciya a Nijeriya. Masu ruwa da tsakin sun yi kira da a ƙara wayar da kan al’umma domin ganin an daƙile kaciyar mata gaba ɗaya a ƙasar nan. Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa A yayin wani taro da aka gudanar kan kawo ƙarshen kaciyar mata a Nijeriya, Nora Agbakhamen, wanda ta assasa Pulse Narrative, ta ce fiye da mata miliyan 200 a faɗin duniya sun fuskanci wani nau’i na kaciya, lamarin...
Hukumar kulada jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna ta shirya fara shirin wayar da kai da ilmantarwa ga maniyyata aikin hajjin bana. Shugaban hukumar, Malam Salihu Abubakar, zai kaddamar da shirin ne a Cibiyar Wayar da Kai ta Alhazai da ke Dogarawa, shekkwatar karamar hukumar Sabon Gari. “Shirin horon wayar da kai yana nufin ilmantar da maniyyata kan dukkan muhimman abubuwan da suka shafi aikin hajji,” in ji shi. Wadannan sun haɗa da ilimin sanin ka’idojin shari’ar Musulunci da dokokin aikin hajji, da kuma warware matsalolin da ka iya tasowa domin tabbatar da sauƙi da ingantaccen hajji ga dukkan maniyyata. Ya kuma bayyana cewa dukkan maniyyata, da waɗanda ke son yin rijista kafin ranar karshe...