Aminiya:
2025-11-22@15:58:08 GMT

Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya

Published: 22nd, November 2025 GMT

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro.

Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja

Mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba.

Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar kowane bayani kafin su yaɗa shi domin kauce wa yaɗs labarun ƙarya.

Wannan bayani ya biyo bayan umarnin Gwamnatin Tarayya na rufe manyan makarantun sakandare 41 da ke yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro, sakamakon sace ɗalibai a jihohin Neja da Kebbi.

Haka kuma wasu jihohi kamar Kwara, Filato, Katsina da Neja sun rufe makarantunsu saboda matsalar tsaro.

Jihar Taraba ma ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantu da ke jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Ƙaryata Jita jita Labarai Ma aikatar ilimi rahotanni Sace Ɗalibai Tsaro

এছাড়াও পড়ুন:

Tuƙin ganganci: KASTELEA  Ƙaddamar Da gangamin wayar da kai a Zariya

Hukumar Kula da Tsaftace Muhalli da Ababen Hawa ta Jihar Kaduna (KASTELEA) ta ƙaddamar da yaƙin wayar da kan jama’a na watannin ƙarshen shekara na shekarar 2025 a Tashar Motoci ta Malam Nasiru El-Rufa’i da ke ’Yan Ƙarfe, Sabon Gari, Zariya.

Taron yaƙin wayar da kan jama’a na  ‘Watannin Ember’ na shekarar 2025 mai taken: “Tafiyar aminci ana cimma ta ta hanyar tuƙi cikin tsaro,” ya samu halartar hukumomin tsaro daban-daban da ke da ƙudirin rage haɗurra a kan manyan hanyoyin jihar

A wajen taron, Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya jaddada muhimmancin rawar da kowa a cikin al’umma zai taka wajen tabbatar da tsaron hanya da kuma tuƙi cikin natsuwa.

Wakilin Sarkin a taron, Injiniya Ibrahim Balarabe Musa, ya bayyana cewa harkar kula da zirga-zirgar ababen hawa aiki ne da ya haɗa hukumomi da dama.

Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba

“Batun zirga-zirga ba na hukuma ɗaya ba ne. Rundunar ’yan sanda, ma’aikatan kashe gobara, Sibil Difens Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) duk suna da rawar da za su taka wajen cimma manufa ɗaya — tsaro,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa wayar da kan jama’a kan tsaro a hanya aiki ne na kullum, tare da yaba wa jajircewar ma’aikatan tsaro.

‘Watannin Ember’ da cunkoson hanya

A nata jawabin, Shugabar KASTELEA, Karla AbdulMalik, ta bayyana cewa Watannin Ember — daga Satumba zuwa Disamba — sukan fi fuskantar cunkoso sakamakon tafiye-tafiyen al’umma domin bukukuwan ƙarshen shekara.

Ta ce yawan zirga-zirgar ababen hawa a wannan lokaci kan haifar da cunkoso, tuƙin ganganci fa kuma karuwar hadurra, lamarin da ke janyo asarar rayuka da dukiya.

“Mun zo ne domin wayar da kan jama’a su bi ƙa’idojin hanya, tare da ƙarfafa wa fasinjoji gwiwa su tsawatar idan suka ga direba na tuƙi cikin hatsari. Kauce wa haɗurra nauyi ne da ya rataya a kan kowa,” in ji ta.

Ta buƙaci direbobi da ke cikin jihar ko masu wucewa su kiyaye dokokin hanya, su kuma rinƙa tuƙi cikin natsuwa don tsira da rayuwar al’umma.

Kiran FRSC da ƙungiyoyin sufuri

A nasa ɓangaren, Kwamandan Shiyyar Zariya na Hukumar FRSC, Nasiru Abdullahi Falgore, wanda SRC Kabiru Kabiru Mado ya wakilta, ya bayyana wannan lokaci a matsayin na tsananin taka-tsantsan.

Ya nuna damuwa kan yawaitar mutuwar mutane da asarar dukiya, tare da kira ga direbobi su bi doka su kuma ɗauki matakan rage haɗurra.

Daga ɓangaren kungiyoyin sufuri, Mataimakin Shugaban NARTO na Jihar Kaduna, Sa’idu Mustapha Basawa, ya bayyana kyakkyawar hulɗar da ke tsakaninsu da hukumomin tsaro.

Ya kuma buƙaci gwamnati ta ƙara sanya alamun hanya a wurare masu muhimmanci, tare da jaddada buƙatar direbobi su riƙa bin ƙa’idojin hanya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Katsina Ta Umurci a Gaggauta Rufe Dukkan Makarantun Jihar
  • Tuƙin ganganci: KASTELEA  Ƙaddamar Da gangamin wayar da kai a Zariya
  • Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba
  • Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Ba da Umarnin Rufe Makarantu 41 Nan Take
  • Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja
  • ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja
  • Tinubu Ya Jaddada Goyon Bayan Gwamnatin Tarayya Ga Muhimman Tsare-Tsaren Kaduna.
  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro