Ganduje ya gindaya wa Kwankwaso sharadin shiga APC
Published: 26th, September 2025 GMT
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ba su da matsala da yunkurin da aka ce tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na yi na komawa jam’iyyar.
Sai dai Ganduje ya ce suna da sharadin da dole sai Kwankwason ya amince da shi kafin ya shiga jam’iyyar.
Aminiya ta rawaito yadda majijoyi masu tushe suka tabbatar da cewa tuni Kwankwaso ya fara tattaunawa da shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, a kan batun komawar.
Amma a cikin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC, ranar Juma’a Ganduje ya ce jam’iyyar tana da dokoki da sharudda, kuma dole Kwankwason ya bi su kafin ya shige ta.
Ganduje ya ce, “Babu shakka mun ji wannan [maganar dawowar su Kwankwaso]. Kuma ka san a Dimokuradiyya, da kuri’ar barawo da ta malami duk daya suke. Saboda haka ba za mu ce mun rufe kofa a jam’iyyarmu babu mai shigowa ba.
“Duk mai son shigowa muna maraba da shi, amma dole sai an bi ka’ida, saboda muna da ka’ida da tsarin mulki.
“Idan suka shigo, muna maraba da su, amma dole za mu sa musu suna, shi ne sun yi amai sun lashe,” in ji shi.
Game da taron da masu fada a ji na APC na jihar Kano suka yi a Abuja ranar Alhamis, Ganduje ya ce sun yi shi ne domin yin nazarin dalilin faduwarsu zabe a 2023 da kuma gode wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kan ayyukan da yake yi a jiharsu da kuma tarin mukaman da ya bayar a jihar.
‘Babu wata matsala tsakanina da Tinubu’Sai dai Ganduje ya ce sabanin yadda wasu suke tunani, babu wata baraka tsakaninsa da Tinubu da ta sa ya ajiye shugabancin jam’iyyar, sabanin yadda wasu suke tunani.
A maimakon haka ma, ya ce alakarsa da shugaban kasar tana nan kamar yadda take a baya, sai ma abin da ya karu.
Ya ce, “Ita siyasa ka san kashi-kashi ce, kuma ita jam’iyyar APC tana ba da mukamai a kan bangare-bangare, kuma ta dauro wani bangare yana ganin kamar cewa wannan mukamin nasa ne.
“To tun da yake ba don mukami muke siyasa ba, idan an ce wannan mukamin na bangare kaza ne, a ajiye a ba su, ba batawa aka yi ba. Shi kansa taron da muka yi, mun yi shi ne saboda mu gode wa Shugaba Tinubu, to ka ga maganar batawa tsakaninmu ba ta ma taso ba.
“Babu wani abu a tsakaninmu sai soyayya. Zai taimaka mana, mu ma za mu taimaka masa mu kwace jihar Kano a 2027,” in ji Ganduje.
Sai dai ya tabbatar da cewa yanzu jam’iyyar ta dinke barakar da ke cikinta a jihar Kano, yana mai cewa tun a baya dama ba ta kai yadda aka rika zuzuta ta ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kwankwaso Ganduje ya ce
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi.
’Yan ta’addan sun kai hari makarantar ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar.
Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja.
An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu.
Shugaba Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin an kubutar da dukkan mutanen da ’yan ta’adda suka sace.
Ya umarci jami’an tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa don ceto sauran ɗaliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.
“Ina farin cikin cewa an samu dukkan ’yan mata 24. Ya zama wajibi mu ƙara tura jami’an tsaro yankunan da ke da rauni don hana sake faruwar irin wannan lamari. Gwamnatina za ta bayar da dukkan tallafin da ake buƙata don cimma haka,” in ji Shugaba Tinubu.