Aminiya:
2025-11-20@12:40:57 GMT

Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas

Published: 20th, November 2025 GMT

Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas,

bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda ba a tantance sunansa ba tukuna, ya mutu nan take a wurin.

Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia

Rahotanni sun ce wani mazaunin unguwar da aka karrama da sarauta ne ya shirya taron cashiyar a titin Anjorin domin murnar nadin.

Sai dai yayin da ake tsaka da bikin, wata babbar mota mai ɗaukar yashi ta yi ƙoƙarin shiga layin amma ta samu cikas saboda ɗaya daga cikin tantunan da aka kafa a kan hanya.

Wani ganau mai suna Femi Ajiboye, ya shaida wa wakilinmu a ranar Laraba cewa yayin da suke ƙoƙarin matsar da tantin gefe, ƙarfen tantin ya taɓa wayar lantarki, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar su nan take.

Femi ya ce, “Bikin nadin sarauta ya ɗauki mako guda ana yin sa, kuma a cikin wannan lokaci wani mazaunin unguwar ya sami sarauta. Yayin da yake gudanar da wani taro na musamman don murnar nadin, wata mota mai ɗaukar yashi ta yi ƙoƙarin shiga sabon rukunin gidajen da ke ƙarshen titin, amma tantin da aka kafa ya tare hanya.
“A lokacin ne wasu daga cikin mahalarta bikin tare da ɗaya daga cikin yaran motar suka ɗage tantin daga hanya.

“Ba tare da sun ankara ba, ashe akwai budaddiyar wayar lantarki a ƙasa. Da ƙarfen tantin ya taɓa wayar, sai wutar ta ja su. Mutane ba su fahimci abin da ke faruwa ba sai da suka ga sun faɗi a ƙasa. A lokacin ne aka gane cewa wutar lantarki ce ta kashe su,” in ji Femi.

Rahotanni sun ce lamarin ya jefa taron cikin alhini, inda aka dakatar da bukin nan take.

Wani mazaunin unguwar da ya bayyana sunansa da Olajide, ya ce an garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwar yaron motar nan take.

“Dukkan yankin ya rikice lokacin da lamarin ya faru saboda mutane sun yi tunanin sun mutu gaba ɗaya. An kai su huɗun asibiti, amma yaron motar bai tsira ba. Sauran baƙi uku an karɓe su kuma suna samun kulawa a yanzu,” in ji shi.

Olajide ya ƙara da cewa iyalan mamacin sun ɗauki gawarsa daga baya suka yi masa jana’iza.

Wani mazaunin unguwar da ya nemi a ɓoye sunansa saboda dalilai na sirri ya ce ya ga mamacin kafin lamarin, lokacin da ya sayi dizal a gidan mai.

“Na ga mutumin lokacin da ya sayi dizal a tashar mai ba da jimawa ba. Na yi matuƙar mamaki da aka ce ya mutu. Wannan mutumin da na gani kimanin mintuna talatin kafin haka,” in ji shi.

Lokacin da aka tuntubi jami’an ‘yan sanda a ranar Lahadi don jin ta bakinsu, jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar ta ce ba ta da masaniya.

Ta ce: “Na kira DPO na yankin, ta ce babu irin wannan rahoto da aka kawo ofishin ’yan sanda.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Wutar Lantarki wani mazaunin unguwar

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Najeriya Sun Karyata Cewa “ISWAP” Ta Kashe Wani Babban Jami’i Mai Mukamin  Birgediya

A wani labari da kungiyar “ISWAP” mai alaka da “Isis” ta watsa, ta sanar da kashe wani babban jami’in sojan Najeriya a wani kwanton bauna da ta yi wa sojoji a kusa da kauyen Wajiroko dake Jahar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sanarwar kungiyar ta “Isis” ya kuma kunshi cewa, baya ga Birgediya  janar Uba da su ka kashe, sun kuma kashe wasu sojojin 4.

Kamfanin dillancin labarun “Reuters” da ya tuntubi rundunar sojan kasar ta Najeriya domin samun Karin bayani akan abinda ya faru bai sami jawabi ba.

Sai dai rundunar sojan ta Najeriya ta ce labarin da ake watsawa na kama babban jami’i mai mukamin janar, ba gaskiya ba ne, kuma bai kamata ‘yan kasa su gaskata shi ba.

Mayakan kungiyar ta “Iswap” sun buga a shafinsu mai suna “A’amaq” cewa, sun kashe jami’in sojan, a wani kwanton bauna da su ka yi .

Jahar Borno tana fada da matsalar masu dauke da makamai da suke ikirarin jihadi, tun daga 2009, wanda ya zuwa yanzu ya ci rayukan dubban mutane da kuma mayar da wasu zama ‘yan hijira nesa da gidajensu.

Ita dai kungiyar “Iswap” ta balle daga Bokoharam, bayan da su ka sami sabani, da a karshe ya kai ga kashe magudun kungiyar Abubakar Shekau.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya ta Fara tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi November 18, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Amincewa Da Kudurin Amurka Da Kwamitin Tsaro Ya yi Kan Gaza November 18, 2025 Afrika ta Kudu Ta yi Gargadi Game Da Duk Wani Yunkuri Na Fitar Da Falasdinawa Daga Yankin Gaza November 18, 2025 Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza November 18, 2025 Mataimakin Shugaban Iran Na Daya Ya Gana Da Prime Ministan Rasha A Birnin Mosko November 18, 2025 Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin November 18, 2025 Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF November 18, 2025 MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro
  • Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 27 a wani sabon harin bam
  • Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa
  • ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’
  • Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas
  • Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe
  • Harin Isra’ila ya kashe mutum 15 a sansanin ‘yan gugun hijira na Falasdinawa a Lebanon
  • DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
  • Sojojin Najeriya Sun Karyata Cewa “ISWAP” Ta Kashe Wani Babban Jami’i Mai Mukamin  Birgediya