Ribadu Ya Gana da Sakataren Yakin Amurka Kan Batun Kashe Kiristoci A Nijeriya
Published: 22nd, November 2025 GMT
Mai ba wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya gana da Sakataren Yakin Amurka, Pete Hegseth, a Washington, inda gwamnatin Trump ta nuna damuwarta kan karin hare-haren da ake kai wa mabiya addinin Kirista a Nijeriya.
Hegseth ya tabbatar da ganawar a shafinsa na X, yana mai cewa bangarorin biyu sun tattauna kan “mummunan tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta,” tare da bayyana cewa Amurka na aiki da gaggawa da Nijeriya wajen rage hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi.
Ganawar ta gudana ne a daidai lokacin da Amurka ke kara nuna damuwa game da tsaro a Arewaci da tsakiyar Nijeriya, inda Boko Haram da ISWAP da kungiyoyin ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare a kauyuka, da coci-coci da gonaki. Ƙungiyoyin kare hakkin bil’adama sun ruwaito karuwar kashe-kashe, inda alkalumman baya-bayan nan ke nuna cewa sama da Kiristoci 7,000 aka kashe cikin watanni bakwai na 2025. Taron ya biyo bayan sace dalibai 215 da malamai 12 daga wata makarantar Katolika a jihar Neja, wanda ya kara tayar da hankalin jama’a kan tabarbarewar tsaro. Wannan lamari ya kuma kara sa Amurka cikin damuwa kan karuwar ayyukan sace mutane da kashe-kashe a kauyuka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Daliban Jami’ar st Gorges Ta Birnin London Sun yi Zanga-zangar Nuna Adawa Da Daukar Tsohon Sojan Isra’ila Aiki November 22, 2025 Isra’ila Ta Kashe Yara Falasdinawa Guda 22 A Yankin Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta November 22, 2025 Iran Ta Sanar Da Nada Janar Jahanshashi A Matsayin Kwamandan Dakarun Rudunar Sojin Kasa November 22, 2025 Majalisar Dattawa A Najeriya Ta Bukaci shugaba Tinubu Ya Dauki Sojoji 100,000 November 22, 2025 Nijar: Dubban Mutane Sun Tarbi Janar Thiani Bayan Komarwa Birnin Yamai November 22, 2025 Afirka Ta Kudu: Rashin Halartar Amurka Taron G-20 Ba Zai Yi Wani Tasiri Ba November 22, 2025 Rundunar Sojan Iran Tana Cikin Shirin Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana November 22, 2025 Madagascar: An Bayyana Jadawalin Farko Na Gwamnatin Rikon-Kwarya Da Kuma Manyan Zabuka November 22, 2025 Unifil: Girmama Hurumin Kasar Lebanon Ne Ginshikin Kuduri Mai Lamba 1701 November 22, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 160 November 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dattawa A Najeriya Ta Bukaci shugaba Tinubu Ya Dauki Sojoji 100,000
Majalisar Dattijai ta nuna damuwa kan tabarbarewar yanayin tsaro a kasar sannan ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta amincewa da daukar akalla matasa 100,000 cikin rundunar sojoji domin karfafa tsarin tsaro na Nijeriya da yake fuskantar kalu bale.
‘Yan majalisar sun kuma yanke shawarar kafa kwamitin musamman domin bincikar yadda aka yi amfani da kudaden da aka ware shekaru da dama don Shirin Makarantu Masu Tsaro (Safe School Programme), a yayin da ake sake nuna damuwa cewa makarantun Nijeriya na ci gaba da kasancewa cikin hadari, inda a baya-bayan nan aka sace ‘yan mata a Jihar Kebbi.
Wadannan kudurori sun biyo bayan tayin da Sanata Abdullahi Yahaya (APC, Kebbi North) ya gabatar, wanda ya yi gargadi cewa tsaro ya kai matakin tashin hankali wanda ke bukatar daukar matakin gaggawa mai karfi.
A yayin tattaunawa, Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi Central) ya bayyana yanayin a matsayin “barazana mai tsanani ga rayuwar kasa”, yana rokon abokan aikinsa da su tabbatar da abin domin magance matsalar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nijar: Dubban Mutane Sun Tarbi Janar Thiani Bayan Komarwa Birnin Yamai November 22, 2025 Afirka Ta Kudu: Rashin Halartar Amurka Taron G-20 Ba Zai Yi Wani Tasiri Ba November 22, 2025 Rundunar Sojan Iran Tana Cikin Shirin Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana November 22, 2025 Madagascar: An Bayyana Jadawalin Farko Na Gwamnatin Rikon-Kwarya Da Kuma Manyan Zabuka November 22, 2025 Unifil: Girmama Hurumin Kasar Lebanon Ne Ginshikin Kuduri Mai Lamba 1701 November 22, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 160 November 22, 2025 Duniyarmu A Yau: Sabon Kuduri Mai Yin Allawadai Da Iran A Hukumat IAEA November 22, 2025 Ghalibaf: Makiya Sun Sawya Dabarbarun Yaki Da Iran November 22, 2025 Tsohon Ma’aikacin CIA Ya Ce HKI Ta Yi Barazanar Amfani Da Makaman Nukliya Kan Iran November 22, 2025 Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Sami Rarrabuwar Kai Dangane Da ‘Keshe Kiristoci A Najeriya’ November 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci