Na sha alwashin kafa tarihi a Camp Nou — Lamine Yamal
Published: 19th, November 2025 GMT
Tauraron ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ya shirya jagorantar ƙungiyar wajen kafa sabon tarihi a filin wasa na Camp Nou, wanda za su koma buga wasa a ƙarshen makon nan yayin karɓar baƙuncin Atletico Bilbao.
Tun kusan kwanaki 900 da suka gabata ne aka rufe filin wasa na Camp Nou sakamakon wasu manyan gyare-gyare da ake yi wa filin, lamarin da ya tilasta wa Barcelona komawa wasu filayen waje domin buga wasanninta.
Sai dai duk da cewa ba a kammala gyaran filin gaba ɗaya ba, an ba da damar komawa amfani da shi domin buga wasanni.
Yamal, mai shekara 18, ya buga wasa ɗaya ne kacal a Camp Nou kafin a rufe shi a watan Agusta 2023, inda a yanzu ya ce yana fatan farantawa dubban magoya baya kulob ɗin a sabon filin da aka sauyawa fasali.
A wani saƙo da ya wallafa a Instagram, Yamal ya saka hotonsa riƙe da bajon Barcelona tare da rubutun cewa Camp Nou shi ne wajen da za a rubuta tarihi.
A farkon watan Nuwamba an gudanar da gwajin farkon shigar tara a filin, inda aka bai wa magoya baya 23,000 damar shiga. Sai a yanzu da aka ƙara yawan kujeru domin ɗaukar ‘yan kallo har 45,401.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barcelona Lamine Yamal
এছাড়াও পড়ুন:
Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Amnesty ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga.
CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a RibasƘungiyar ta ce bincikenta ya gano cewar ’yan bindigar sun kai hari ne da misalin ƙarfe 5 na safiya, inda suka tilasta wani ma’aikacin makarantar ya nuna musu ɗakin kwanan daliban mata, sannan suka yi awon gaba da su.
Amnesty ta ce wannan harin ya sake nuna cewa, “gwamnatin Tinubu ba ta da wani ingantaccen tsari na kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga, duk da matakan da ake ce an ɗauka, domin babu wani gagarumin sauyi da aka gani a ƙasa.”
Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin ceto ɗaliban cikin aminci, tare da gano musabbabin yawaitar sace-sacen mutane a sassan ƙasar, abin da ta ce yana barazana ga ilimi da zaman lafiyar al’umma.
Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da sace ɗalibanA nata ɓangaren, gwamnatin Najeriya ta bayyana tsananin damuwa kan harin, inda ta ce ta bai wa jami’an tsaro umarnin gano da ceto ɗaliban cikin gaggawa.
Cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai, Muhammad Idris ya fitar, ya ce gwamnati za ta tabbata an kamo waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci.
Ya ƙara da cewa gwamnati na tare da iyaye da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa, tare da jaddada cewa za a yi duk wani abu mai yiyuwa domin ganin yaran sun koma gida cikin aminci.
Za mu dawo da duk ɗaliban da aka sace —Jami’an TsaroWata rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da ’yan sanda, na ci gaba da laluben ɗaliban bayan ’yan bindiga sun awon gaba da su.
Da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar ’yan matan, inda bayanai ke nuni da cewa an sace ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin shugaban makarantar da wani maigadi kana suka jikkatar da dama.