Jami’ar Bayero Ta Bayyana Alhininta Bisa Kisan Gillar Wani Dalibinta
Published: 7th, August 2025 GMT
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta bayyana alhinita kan kisan gilla da aka yi wa Umar Abdullahi Hafizi, dalibi da ke matakin karatu na 3 a Sashen Ilimin Zamantakewa (Sociology), wanda wasu masu kwacen waya suka daba wa wuka har lahira a gidansa da ke unguwar Dorayi a ƙaramar hukumar Gwale.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Malam Lamara Garba, ya fitar, wacce aka rabawa manema labarai.
A cewarsa, kodayake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’ar, shugabannin BUK sun jaddada cewa suna kokari wajen tabbatar da tsaron ɗalibansu.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana wannan lamari a matsayin babban rashi da ya girgiza al’ummar jami’ar, tare da mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, abokansa da ɗaliban jami’ar baki ɗaya.
Farfesa Abbas ya ce jami’ar na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan danyen aiki sun fuskanci hukunci.
Daga cikin matakan gaggawa da jami’ar ta ɗauka, sun haɗa da jigilar gawar mamacin zuwa garinsu na Zariya a Jihar Kaduna domin yi masa jana’iza bisa tsarin Musulunci.
BUK ta kuma shawarci ɗalibai da su zauna lafiya da yin taka-tsantsan, tare da kira ga jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su iya taimaka wa binciken da ake ci gaba da yi.
Jami’ar Bayero ta yi addu’ar Allah ya jikan Umar Abdullahi Hafizi, ya kuma bai wa iyalansa juriyar wannan babban rashi.
Daga Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Buba ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi kyauta
Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi da kuma takin zamani kyauta ga al’ummar mazaɓarsa.
Da yake ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobin garin Goɗɗiya da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, Sanata Buba ya ce, “A bana, za mu yi allurar rigakafin dabbobi 85,000 a wannan yankin na Majalisar Dattawa.”
Ya ce a baya an yi wa dabbobi kimanin 40,000 allurar rigakafin a fadin yankin.
“Na yi imanin cewa wannan abu ɗaya ne daga ayyukan wakilci wa mutanenmu manoma da makiyaya. ’Yan Najeriya ne kamar mu duka, suna zaɓe mu, kuma suna ba da gudummawa sosai ga tattalin arzikin ƙasar nan.
“Wannan ba wani abu ba ne na musamman amma na yi imanin cewa wani abu ne da muke yi wa makiyaya da manoma.”
Ya ce alluran rigakafin na kyauta na da nufin kare rayuwar dabbobi, da ƙara haɓaka kiwonsu, da kuma tabbatar da lafiyarsu da wadatar abinci a ƙananan hukumomi bakwai da ke Shiyyar Bauchi ta Kudu.
“Wannan aikin wata babbar alama ce da ke nuna aniyarmu ta kare lafiyar dabbobinmu, da kare lafiyar al’ummarmu, da kuma martaba tattalin arzikinmu.
“Za a gudanar da wannan aiki a dukkanin ƙananan hukumomin bakwai na shiyyar Sanata na Bauchi ta kudu, inda za a yi wa shanu, tumaki da awaki a kowace ƙaramar hukuma alluran rigakafin.
“Ƙwararrun likitocin dabbobi da masana kimiyyar kiwon lafiyar dabbobi za su yi aiki tare da shugabannin al’umma, masu dabbobi, da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da cewa wannan aikin ya samu nasara a a kowace ƙaramar hukuma.”
Wani mai ruwa da tsaki a mazaɓar Dass, Tafawa Valewa da Vogoro Alhaji Aminu Tukur ya buƙaci manoman yankin da su fito da dabbobinsu domin yin rigakafin.
Tukur ya yi kira ga Sanatan da ya gina cibiyar koyar da sana’o’i a yankin domin rage yawan matasa marasa aikin yi, ya kuma shawarce shi da ya riƙa bibiyar aikin hanyar Gwamnatin Tarayya da tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya fara da ba a ƙarasa su ba.
Makiyaya da dama da suka ci gajiyar allurar sun yaba da yadda Sanata Buba ya jajirce wajen inganta harkokin kiwon dabbobi da lafiyarsu, da tallafa wa manoma ta hanyar ingantattun tsare-tsare da kuma daukar matakai cikin lokaci. Sun nuna jin daɗinsu bisa bayar da tallafin a kan lokaci.
Sankaran ya kuma fara rabon takin zamani buhu 4,200 samfurin NPK kyauta ga manoma.
Ya ce an dauki matakin ne don tallafa wa ayyukan noma da inganta amfanin gona ga manoman yankin.
Sanatan ya ce shirin na da nufin ƙarfafa wa manoma gwiwa domin su sami damar rage ƙalubalen da ake fuskanta wajen samar da abinci tare da inganta adadi da ingancin amfanin gona ga al’ummar gundumar.
Ya gode wa kwamitin rabon kayayyakin tare da shawartar su da su tabbatar da adalci tare da raba kayan ga manoma na gaskiya.