Gwamnatin Kano Ta Rarraba Takardun Guraben Karatu Ga Dalibai
Published: 25th, September 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kano, ta raba wa daliban da suka kamala karatun Furamare takardun gurbin karatu zuwa manyan makarantun sakandare a fadin jihar.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar a makarantar sakandiren ’yan mata ta Maryam Aloma da ke Kano, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ya ce shirin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen samar da ilimi kyauta da kuma wayar da kan al’umma don bunkasa ilimi.
Dokta Makoda ya bayyana sauye-sauyen da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bullo da su, da suka hada da daukar malamai aiki, gyaran makarantu, da samar da kayayyakin koyarwa, inda ya bayyana su a matsayin matakan farfado da harkar ilimi.
Ya danganta fitowar jihar Kano a matsayin jihar da ta zo kan gaba a jarabawar NECO ta shekarar 2025 ga yadda Gwamna Yusuf ya ba da fifiko a fannin ilimi, inda ya yaba wa gwamnan kan yadda ya rika tallafa wa bukatun ma’aikatar.
“Mai girma Alhaji Abba Kabir Yusuf yana aiki tukuru, shi ya sa harkar ilimi ta Kano ke tafiya cikin hanzari, misali, don magance matsalar karancin malaman lissafi, gwamna ya amince da daukar sabbin ma’aikata, kuma nan ba da dadewa ba za a tura su makarantu a fadin jihar.” Inji Dr. Makoda.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga iyaye da su kara kaimi ga kokarin gwamnati ta hanyar tabbatar da ‘ya’yansu na zuwa makaranta akai-akai domin samun ilimi mai inganci.
A nasa jawabin, babban sakataren hukumar kula da manyan makarantun sakandire ta jihar Kano, Alhaji Rabi’u Saleh Gwarzo, ya bayyana cewa, Kano ba ta taba shiga matsayi na gaba na NECO ba sai a yanzu, inda ya ce wannan nasarar ta samu ne sakamakon yadda Gwamna Yusuf ya himmatu wajen inganta ilimi.
Ya jaddada bukatar yin aiki tare tsakanin Hukumar Kula da Ilimi ta (SUBEB), Hukumar Kula da Manyan Makarantu ta Sakandare, da Sashen Albarkatun Ilimi don ba da tabbacin samun sauyi ga dalibai.
Hakazalika, shugaban kungiyar iyaye da malamai ta jiha (PTA), Alhaji Dahiru Salisu Mai Jimiri da shugaban kwamitin kula da makarantu (SBMC), Tijjani Haladu Baraya, sun yaba da kokarin gwamnati na farfado da ilimi tare da yin kira ga iyaye da kungiyoyin farar hula da su ci gaba da tallafawa gwamnati.
Shirin wanda ake ganin wani muhimmin mataki ne na dorewar ci gaban ilimi a Kano, ya samu halartar daraktocin shiyya, jami’an ma’aikatar, da manyan wakilan SUBEB da kuma hukumar kula da manyan makarantun sakandire.
COV/KHADIJAH ALIYU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
Jami’an tsaro a Jihar Kaduna, sun fara gudanar da babban samame domin kawar da ’yan ta’adda da ’yan bindiga a wasu ƙananan hukumomin jihar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce an gudanar da aikin tare haɗin gwiwar sojoji, DSS, NSCDC, KADVS, da kuma ƙungiyoyin sa-kai da mafarauta.
Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000Aikin ya shafi ƙananan hukumomin Makarfi, Hunkuyi da Ikara.
Rundunar ta ce manufar wannan samame shi ne “share dukkanin maɓoyar miyagu, rushe sansanonin da suka kafa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.”
Wannan mataki ya biyo bayan umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, wanda ya umarci dukkanin rundunonin ’yan sanda a faɗin ƙasar nan su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da aikata laifuka.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Rabiu Muhammad, ya tabbatar wa jama’a cewa jami’an tsaro za su ci gaba da matsa wa miyagu lamba.
Ya ce za su ci gaba da yin gwiwa da rundunonin tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar.