Ta Yaya Za a Ba Matasa Damar Raya Kansu?
Published: 7th, August 2025 GMT
Mun san cewa, ci gaban harkokin matasa na bukatar bunkasar sana’o’i. Cikin shekarun nan, aikin zuba jari ga kasashen Afirka da kasar Sin ke yi na samun ci gaba yadda ake bukata. Inda yawan kudin da Sin take zubawa kai tsaye a fannin samar da kayayyaki a kasashen Afirka, ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 400 a duk shekara.
Ban da haka, ci gaban harkokin matasa ba zai rasa alaka da karuwar ilimi da ingantuwar fasahohi ba, inda a wannan fanni ma kasar Sin ta tsara ayyukan hadin kai da yawa, don samar da damammakin samun horon fasahohin sana’o’i ga dimbin matasan Afirka, da horar da kwararrun masana matasa masu ilimin aikin gona da masu jagorantar aikin wadatar da manoma ta wasu sabbin fasahohi a kasashen Afirka, da kafa cibiyoyin bude sabbin kamfanoni da kirkiro sabbin fasahohi na matasa, da kulla huldar hadin kai tsakanin jami’o’i dari 1 na kasashen Afirka da kasar Sin, da dai sauransu. Inda gasar da muka ambata ita ma take cikin ayyukan da aka tsara tare da aiwatar da su.
Sande Ngalande, darakta ne na cibiyar nazarin batutuwa masu alaka da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ta jami’ar Zambia. Ya taba bayyana cewa, dabarar kasar Sin ta zamanantar da kasa ta amfani kasashen Afirka, inda dimbin matasan Afirka masu sana’o’i daban daban ke son mu’ammala da Sin, da fahimtar Sin, da koyon fasahohin kasar Sin. Kana ta hanyar hadin gwiwar Sin da Afirka, matasan Afirka suna iya kulla zumunci mai zurfi da Sinawa, gami da samun damar raya kansu, da kasashensu, da tabbatar da ci gaba mai dorewa a nahiyar Afirka.
Cikin shirin ajandar shekarar 2063 na kungiyar kasashen Afirka ta AU, an ce ya kamata a sanya matasa su zama karfin farfado da nahiyar Afirka, kuma hadin gwiwar Sin da Afirka na taimakawa wajen ganin tabbatuwar wannan buri a zahiri. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
UNGA: Shettima Ya Tallata Damar Zuba Jari Na Dala Biliyan 200 A Fannin Makamashi A Nijeriya
Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa tuni gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki manyan matakai na gyara tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa farashin musayar kuɗi, da kuma sabunta tsarin haraji da kwastam.
Ya ƙara da cewa waɗannan sauye-sauye sun fara samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, inda ya nuna cewa manyan kamfanonin tantance darajar kuɗi irin su Fitch da Moody’s sun ɗaga matsayin Najeriya saboda ingantattun manufofi da ƙaruwar ajiyar kuɗi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp