Tuƙin ganganci: KASTELEA Ƙaddamar Da gangamin wayar da kai a Zariya
Published: 22nd, November 2025 GMT
Hukumar Kula da Tsaftace Muhalli da Ababen Hawa ta Jihar Kaduna (KASTELEA) ta ƙaddamar da yaƙin wayar da kan jama’a na watannin ƙarshen shekara na shekarar 2025 a Tashar Motoci ta Malam Nasiru El-Rufa’i da ke ’Yan Ƙarfe, Sabon Gari, Zariya.
Taron yaƙin wayar da kan jama’a na ‘Watannin Ember’ na shekarar 2025 mai taken: “Tafiyar aminci ana cimma ta ta hanyar tuƙi cikin tsaro,” ya samu halartar hukumomin tsaro daban-daban da ke da ƙudirin rage haɗurra a kan manyan hanyoyin jihar
A wajen taron, Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya jaddada muhimmancin rawar da kowa a cikin al’umma zai taka wajen tabbatar da tsaron hanya da kuma tuƙi cikin natsuwa.
Wakilin Sarkin a taron, Injiniya Ibrahim Balarabe Musa, ya bayyana cewa harkar kula da zirga-zirgar ababen hawa aiki ne da ya haɗa hukumomi da dama.
Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba“Batun zirga-zirga ba na hukuma ɗaya ba ne. Rundunar ’yan sanda, ma’aikatan kashe gobara, Sibil Difens Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) duk suna da rawar da za su taka wajen cimma manufa ɗaya — tsaro,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wayar da kan jama’a kan tsaro a hanya aiki ne na kullum, tare da yaba wa jajircewar ma’aikatan tsaro.
‘Watannin Ember’ da cunkoson hanyaA nata jawabin, Shugabar KASTELEA, Karla AbdulMalik, ta bayyana cewa Watannin Ember — daga Satumba zuwa Disamba — sukan fi fuskantar cunkoso sakamakon tafiye-tafiyen al’umma domin bukukuwan ƙarshen shekara.
Ta ce yawan zirga-zirgar ababen hawa a wannan lokaci kan haifar da cunkoso, tuƙin ganganci fa kuma karuwar hadurra, lamarin da ke janyo asarar rayuka da dukiya.
“Mun zo ne domin wayar da kan jama’a su bi ƙa’idojin hanya, tare da ƙarfafa wa fasinjoji gwiwa su tsawatar idan suka ga direba na tuƙi cikin hatsari. Kauce wa haɗurra nauyi ne da ya rataya a kan kowa,” in ji ta.
Ta buƙaci direbobi da ke cikin jihar ko masu wucewa su kiyaye dokokin hanya, su kuma rinƙa tuƙi cikin natsuwa don tsira da rayuwar al’umma.
Kiran FRSC da ƙungiyoyin sufuriA nasa ɓangaren, Kwamandan Shiyyar Zariya na Hukumar FRSC, Nasiru Abdullahi Falgore, wanda SRC Kabiru Kabiru Mado ya wakilta, ya bayyana wannan lokaci a matsayin na tsananin taka-tsantsan.
Ya nuna damuwa kan yawaitar mutuwar mutane da asarar dukiya, tare da kira ga direbobi su bi doka su kuma ɗauki matakan rage haɗurra.
Daga ɓangaren kungiyoyin sufuri, Mataimakin Shugaban NARTO na Jihar Kaduna, Sa’idu Mustapha Basawa, ya bayyana kyakkyawar hulɗar da ke tsakaninsu da hukumomin tsaro.
Ya kuma buƙaci gwamnati ta ƙara sanya alamun hanya a wurare masu muhimmanci, tare da jaddada buƙatar direbobi su riƙa bin ƙa’idojin hanya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zariya wayar da kan jama a
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Tabbatar da Yunkurin Kafa Cibiyar Tarayya Ta Uku a Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma.
Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai Gidan Gwamnati da ke Dutse.
Ya taya shugaban kwalejin da tawagarsa murna, inda ya bayyana nadin nasu a matsayin tarihi kuma mai matuƙar muhimmanci.
Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa kafa sabuwar cibiyar ilimi aiki ne babba, yana mai bayyana tabbacin cewa mutanen da aka zaba don fara gudanar da kwalejin za su taka rawar gani.
“Kafa sabuwar cibiyar ilimi ba abu ba ne mai sauƙi. Kun shiga tarihin wannan kwaleji, wacce idan ta yi nasara, za a tuna da ku cikin alheri; idan ta gaza kuma, babu shakka hakan zai shafe ku. Amma ina da tabbaci, ganin irin mutanen da ke cikin wannan tawaga, cewa kwalejin ta fara da ƙafar dama,” in ji shi.
Namadi ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da dokokin da suka kafa Kwalejin Noma ta Tarayya a Kirikasamma da Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Birnin Kudu, inda ya bayyana cewa Jigawa na kan hanyar samun wata cibiyar tarayya ta uku bayan tattaunawar da ya yi da shugaban ƙasan.
Gwamna Namadi ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga tawagar gudanarwar.
“Za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da nasarar fara aiki a kwalejin, kuna da cikakken goyon bayanmu, mun yi sa’a sosai da samun Dr. Gwaram a matsayin jagoran wannan cibiyar, ƙwararren masani a fannin noma, gogaggen mai gudanarwa, kuma ɗan asalin Jigawa mai kishin ƙasa.”
Ya yaba wa Ministan Noma, Ministan Ilimi, da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Mazabar Birniwa/Guri/Kirikasamma, Alhaji Fulata, kan rawar da suka taka wajen ganin an kafa sabuwar kwalejin.
Haka kuma ya jinjinawa shugaban kwalejin da Kwamishinan Ilimi na manyan makarantu bisa jajircewarsu.
Tunda farko, shugaban kwalejin, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa goyon bayanta, tare da jaddada cewa kwalejin ta shirya fara aiki nan take.
A cewarsa, kwalejin za ta kasance cibiya ta musamman da za a koyar da ingantattun hanyoyin noma na zamani.
Ya bayyana cewa sun shirya horas da manoma da kuma jawo hukumomin da suka dace zuwa Jihar Jigawa.
Ya ce sun fara tattaunawa da hukumomin da ke da alhakin rajista da tsari kamar NBTE da sauran da ake buƙata don fara aiki.
Ya yaba da irin ƙoƙarin da aka yi wanda ya kai ga amincewa da kafa cibiyar, yana mai jaddada yawan tattaunawar da aka yi da hukumomin tarayya, masu tsara doka, da masu ruwa da tsaki, tare da tabbatar wa gwamna cewa tawagarsu za ta yi aiki tukuru wajen cimma nasara kwalejin.