Aminiya:
2025-11-19@12:27:36 GMT

‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’

Published: 19th, November 2025 GMT

Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, mai gadin makarantar ’yan mata ta GCGSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, wadda aka kai wa hari da safiyar Litinin, ta bayyana yadda aka kashe mijinta.

Da take magana da ’yan jarida a wurin da lamarin ya faru, ta ce bayan da maharan suka kutsa cikin makarantar, sai suka shigo cikin gidansu.

Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas HOTUNA: Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe

Matar ta ce ba ta san cewa mutane ne a bakin ƙofar ba sai da suka shigo cikin ɗakinsu.

“Da misalin ƙarfe 4:00 na Asuba a ranar Litinin muna kwance ni da mijina sai muka ji ana ƙoƙarin karya ƙofar dakinm. Na tashe shi amma ya yi tunanin akuya ce ke motsi a waje.

“Kafin mu ankara, sai gungun ’yan bindiga suka shigo ɗakinmu suka ce ya kai su ɗakin kwanan dalibai. Da ya ƙi, sai suka harbe shi. Na yi gaggawar rungumarsa, amma suka ture ni gefe suka ci gaba tafiya ɗakin daliban.

“Ban san yadda suka yi suka sace ’yan mata ba, amma na ji ihunsu da kukansu. Har yanzu abin yana min kamar mafarki mai ban tsoro,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa wani mutum mai suna Ali Shehu, wanda shi ne mai gadin makarantar, shi ma ’yan bindigar sun harbe shi har lahira.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi

Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi.

Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa.

Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi

Aminiya ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, inda bayanai ke nuni da cewa sun yi awon gaba da ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin shugaban makarantar da wani maigadi kana suka jikkatar da dama.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta bayyana tsananin damuwa kan harin, inda ta ce ta bai wa jami’an tsaro umarnin gano da ceto ɗaliban cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai, Muhammad Idris ya fitar, ya ce gwamnati za ta tabbata an kamo waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci.

Ya ƙara da cewa gwamnati na tare da iyaye da ’yan uwan waɗanda abin ya shafa, tare da jaddada cewa za a yi duk wani abu mai yiyuwa domin ganin yaran sun koma gida cikin aminci.

Ita ma ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International, ta yi kakkausar suka kan sabon harin, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici wanda ta ce ya tabbatar da gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
  • Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi
  • Dole ku ceto daliban da aka sace a Kebbi Shugaban Sojoji
  • GGCSS Maga: Halin da iyaye ke ciki bayan sace ’ya’yansu
  • Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi
  • ’Yan ta’adda sun yi garkuwa da dalibai 25 a Kebbi