Aminiya:
2025-11-21@21:21:35 GMT

Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya

Published: 22nd, November 2025 GMT

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya.

Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya.

Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja

A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro.

Takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da kuma kauce wa duk wata barazana.

Makarantun da abin ya shafa sun haɗa da waɗanda ke Zariya, Daura, Sakkwato, Potiskum, Ikare-Akoko, Abaji, da sauransu.

Wannan umarni na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren da ake kai wa makarantu ke ƙara tsananta.

A Jihar Kebbi, ’yan bindiga sun kai hari makarantar Government Girls Comprehensive Secondary School da ke Maga, inda suka sace ɗalibai 25, tare da kashe mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Makaku, yayin da yake ƙoƙarin kare su.

Rahotanni sun nuna cewa daga 2014 zuwa 2022, an sace yara sama 1,680 a makarantun Najeriya.

Gwamnati ta ce rufe makarantun na wucin gadi ne, domin kare ɗalibai.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gwamnatin tarayya hare hare makarantu Rufe Makarantu rufe makarantun

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi 

Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25.

Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare.

Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta

“An tura sojoji, amma sun bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare, sannan ƙarfe 3:45 harin ya faru. Wa ya bayar da izinin su bar makarantar a wannan lokaci mai muhimmanci?” in ji Idris.

Ya ce bayan barin makarantar da sojoji suka yi ƙasa da awa guda ’yan bindiga suka kai hari.

Ya ce barin makarantar da sojojin suka yi, ya saɓa wa alƙawuran da aka yi na ƙarfafa tsaro a makarantu da ke kan iyakar jihar.

Idris, ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya da ta jihar na aiki tuƙuru don ceto ɗaliban da aka sace.

Gwamnan, ya bayyana cewa an umarci malaman addini da su yi addu’a domin samun zaman lafiya da kuɓutar da waɗanda aka sace.

Idris, ya ce abin da ya faru na nuna cewa akwai maƙiya da ke ƙoƙarin kawo cikas ga ci gaban jihar.

A yayin ziyarar nuna goyon baya, Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce abin da ya faru abin damuwa ne, musamman ma a lokacin da Kebbi ke samun ci gaba mai kyau.

Ya ƙara da cewa duk wani yunƙuri na daƙile ci gaban jihar ba zai yi nasara ba, kuma ya shawarci gwamnan da ya dage.

Ajaero ya ce, “Wannan kawo cikas ne, amma duk wani yunƙuri na daƙile ci gaban jihar ba zai yi nasara ba. Muna tare da ku.”

A halin yanzu, rundunar sojin ƙasa ta fara bincike kan dalilin da ya sa sojojin da aka tura makarantar suka bar wajen aiki kafin aukuwar harin.

Majiyoyin tsaro sun ce a yanzu haka an fara binciken wasu manyan jami’ai kan lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja
  • Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi 
  • ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja
  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
  • ’Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 100 Kudin Fansa Kan Kowane Mutum Ɗaya da Suka Sace a Kwara
  • Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai
  • Nigeria: An Rufe Makarantun Kwana A Jahar Kwara Saboda Matsalar Tsaro
  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro