Aminiya:
2025-11-21@05:38:54 GMT

NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu

Published: 21st, November 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya.

 

Yayin da gwamnati ke cewa hukuncin ya biyo bayan dogon shari’a da hujjoji da suka tabbatar da aikata laifukan da ake tuhumarsa da su, wasu na ganin batun na da matuƙar sarkakiya musamman ma yadda iyalansa da magoya bayansa ke kallon wannan hukunci.

NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace

Shin ko yaya ‘yan uwan Nnamdi Kanu suka kalli wannan hukunci?

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da tafiyarsa zuwa Birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Luanda na Angola, sakamakon sace ɗalibai a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a wata coci da ke yankin Eruku a Jihar Kwara.

Tinubu, shirya barin Abuja a ranar Laraba domin halartar taron G20 karo na 20 da kuma Taron AU-EU karo na bakwai.

Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.

“Shugaban ƙasa ya umarci sojoji da ’yan sanda da su aike ƙarin jami’ai zuwa waɗannan yankuna domin a tabbatar an bi diddigin ’yan bindigar da suka kai wa masu ibada hari.”

Shugaban ya ɗage tafiyar domin samun ƙarin bayanan tsaro da ɗaukar matakan gaggawa.

Bayan neman agaji da Gwamnan Jihar Kwara ya yi, Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su tura ƙarin dakaru da ’yan sanda zuwa Eruku da dukkanin yankin Ƙaramar Hukumar Ekiti domin inganta tsaro.

Idan ba a manta ba ’yan bindiga sun kai wa masu ibada hari a Cocin Christ Apostolic Church a ranar Litinin.

Shugaba Tinubu na jiran cikakken rahoto daga Mataimakinsa Kashim Shettima, wanda ya kai wa al’ummar Jihar Kebbi ziyarar jaje kan sace ɗalibai mata da wasu mahara suka yi.

Hakazalika, yana jiran rahotan ’yan sanda da Hukumar DSS game da harin da aka kai a Jihar Kwara.

Onanuga, ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa ya damu matuƙa kan sace ɗaliban da aka yi a Jihar Kebbi.

“Shugaba Tinubu ya bayyana a fili cewa dole ne a yi duk mai yiwuwa domin ceto ɗalibai 24 da aka sace tare da dawo da su gida lafiya,” in ji shi.

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce kiyaye rayukan ’yan Najeriya shi ne babban abin da shugaban ƙasa ya fi mayar da hankali a kai.

A cewar fadar wannan ne dalilin da ya sa ya ɗage tafiyarsa don mayar da hankali kan inganta tsaro a yankunan da abin ya shafa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kotu Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Zaman Kurkuku Na Har Abada  Akan Laifin Ta’addanci
  • An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai
  • Kotu ta sami Nnamdi Kanu da laifukan ta’addanci
  • Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka
  • Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia
  • NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki
  • Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Osimhen ba zai halarci bikin karrama gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana ba
  • Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya