Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya  saboda matsalolin tsaro.

A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk wani yunkurin hari, Ministan Ilimi ya amince a rufe makarantun nan dltaje.

Ga jerin makarantu da abin ya shafa:

Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Minjibir, Jihar Kano Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ganduje, Jihar Kano Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Zariya, Jihar Kaduna Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kafanchan, Jihar Kaduna Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bakori, da wacce ke Bwari, Abuja. Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Dayi, Jihar Katsina Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Daura, Jihar Katsina Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Tambuwal, Jihar Sakkwato Kwalejin Kimiyya ta Tarayya, Jihar Sakkwato Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Wurno, Jihar Sakkwato Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Gusau, Jihar Zamfara Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Anka, Jihar Zamfara Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Gwandu, Jihar Kebbi Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Birnin Yari, Jihar Kebbi Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Zuru, Jihar Kebbi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Kazaure, Jihar Jigawa Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Kiyawa, Jihar Jigawa Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Hadejia, Jihar Jigawa Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bida, Jihar Neja Kwalejin Gwamnatin Tarayya, New Bussa, Jihar Neja Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kuta-Shiroro, Jihar Neja Akademiyar Gwamnatin Tarayya, Suleja, Jihar Neja Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Ilorin, Jihar Kwara Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Omu-Aran, Jihar Kwara Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Gwanara, Jihar Kwara Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Ugwolawo, Jihar Kogi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Kabba, Jihar Kogi Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ogugu, Jihar Kogi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bwari, Abuja Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Rubochi, Abuja Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Abaji, Abuja Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Potiskum, Jihar Yobe Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Buni-Yadi, Jihar Yobe Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Gashua, Jihar Yobe Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Michika, Jihar Adamawa Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Ganye, Jihar Adamawa Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Azare, Jihar Bauchi Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Misau, Jihar Bauchi Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bajoga, Jihar Gombe Kwalejin Gwamnatin Tarayya, Billiri, Jihar Gombe Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Zambuk Jihar Gombe.

Takardar ta umarci Shugabannin makarantu da abin ya shafa su tabbatar da cikakken bin wannan umarni.

 

RN

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Rufe Makarantu Tsaro Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya Kwalejin Fasaha ta Tarayya Kwalejin Gwamnatin Tarayya

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗalibai 215 da malamai 12 aka sace a Makaranta a Neja — CAN

Yawan ɗaliban da aka sace a makarantar Sakandaren St. Mary’s da ke Jihar Neja ya kai 215 da kuma ma’aikata 12 a cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).

Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Neja, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya ce mutum 227 aka sace a makarantar, ɗalibai 215 da kuma malamai 15.

A safiyar Juma’a ne ’yan bindiga suka kutsa makarantar da ke yankin Papiri da ke Karamar Hukumar Agwara ta jihar Neja suka yi awon gaba da su.

Da yake jawabi bayan ziyartar makarantar, ya bayyana cewa, “Na gana da iyayen ɗaliban kuma mun tabbatar musu cewa muna aiki tare da gwamnati da jami’an tsaro domin ganin an ceto yaran.

Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya

“Alƙaluman da aka tattara sun nuna yara 215 da malamai 12 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin.

“Akwai yaran da suka tsere a lokacin da aka kai harin, kuma iyayen sun zo suka kwashe ’ya’yansu tunda an rufe makarantu,” in ji shi.

Aminiya ba ta iya tabbatar da alƙaluman ba, kuma hukumomi ba su fitar da nasu alƙaluman ba, zuwa lokacin da muka kammala wannan labari.

Wakilinmu ya gano cewa da misalin ƙarfe 2 na dare ne ’yan bindigar suka kai harin, inda daga bisani suka loda ɗaliban da malaman a cikin wata babbar mota da suka ƙwace a yankin.

Daga baya sun jefar da motar a hanya bayan da ya samu matsala, suka kora mutanen zuwa cikin daji.

An kai harin ne kwana huɗu bayan a ranar Litinin ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai 26 makarantar ’yan mata ta GGCSS da ke yankin Maga a Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu da ke Jihar Neja — ’yan bindigar na neman kuɗin fansa Naira miliyan 100 a kan ɗaliban.

Aminiya ta ruwaito cewar Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe duk makarantunta na kwana guda 41 da ke faɗin ƙasar nan a sakamakon hare-haren.

Kafin nan gwamnatin jihar Katsina ya rufe ɗauƙacin makarantu, gwamnatin Filato ta rufe ɗauƙacin makarantun ƙananan sakandare, a yayin da gwamnatin Kwara ta rufe wasu makarantu 50 a wasu yankuna saboda tsaro, bayan sace Ɗaliban Makarantar Maga.

Gwamnatin Jihar Neja zargi Hukumomin Makarantar St. da rashin bin umarnin kada a bisa ga makarantar saboda rashin tsaro a yankin, amma hukumomin makarantar suka yi biris da umarnin gwamnatin suka yi gaban kansu wajen buɗe makarantar, lamarin da ya jefa rayuwar dalibai da malaman cikin haɗari.

Idan ba a manta ba, bayan harin Makarantar Maga, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Ministan Tsaro Bello Matawalle da ya koma Jihar Kebbi, jami’an tsaro kuma su tabbata sun ceto yaran cikin aminci.

SP Wasiu Abiodun, kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, ya tabbatar da harin tare da cewa an tura jami’an tsaron haɗin gwiwa na musamman domin ceto ɗaliban da malamansu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba
  • Ɗalibai 215 da malamai 12 aka sace a Makaranta a Neja — CAN
  • Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja
  • Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta
  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
  • Tinubu Ya Jaddada Goyon Bayan Gwamnatin Tarayya Ga Muhimman Tsare-Tsaren Kaduna.
  • Nigeria: An Rufe Makarantun Kwana A Jahar Kwara Saboda Matsalar Tsaro
  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro