Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin ’yan gudun a Borno
Published: 22nd, November 2025 GMT
Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida.
Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba.
An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki.
Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba.
Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin gobarar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara Sansanin yan gudun hijira
এছাড়াও পড়ুন:
Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 160
160-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku, kissoshi wadanda suka zo cikin Alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Mrtada Muttahari, ko kuma cikin littafan Mathnawa na maulana Jalaluddeen Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////… Ma dalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Haddan dan Aliyu (a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun bayyana yadda Imam (a) yayi musayar wasiku da Mu’awiya dan Abu-Sufyan, wanda ya kai ga, Imam ya tada rundunar yaki don yakarshi a lokacinda ya fahinci cewa Mu’awiya yana kan hanyarsa ta zuwa Iraki da mayakansa.
A cikin Shirin mun bayyana cewa kafin shahadar Imam Ali(a) ya rika ya tanaji runduna mai akalla mayaka dubu 40, kamar yadda ibn Abil Hadid ya kawo, don haka wannan rundunar itace dansa Imam Hassan (a) ya gada da kuma ita ce ya tunkari Mu’awiya dan Abu sunfyan bayan an masa Bai’a.
Malaman tarihi sun yi sabani a kan yawan sojojin Imam Al-Hassan (a) wasu sunce, dubu, 100, wasu sun ce dubu 90 wasu sun ce 70 da sauransu. Sabanin da malaman tarihi suka samu dangane da adadin sojojin Imam Al-Hassan (a) bai da muhimmanci, abu mai muhimmanci shi ne, yadda wannan rundunar ta kasance, cikin sabani da rashin hadin kai da son zuciya da son duniya wanda daga karkashe ya kai ga wargajewarta da kuma rashin samun nasara a kan makiyanta.
Sheikh Al-Mufita ya sifanta rundunar Imam (a) a lokacin, da cewa, wasu daga cikinsu, basa son fita zuwa yakin bayan ya kirasu zuwa yakar Mu’awiya. Wasu kuma sun fi son kasancewa tare da mu’awiya duk da cewa suna cikin rundunar Imam Hassan (a), wasunsu suna bin shuwagabannin kabilunsu ne kawai, ba ruwansu da addini, duk inda shuwagabanninsu suka je zasu basu ba tare da sun yi tunana mai zurfi ba. Wasu kuma suna neman duniya ido a rufe, Sunan son jin dadin duniya don haka duk wanda zai basu suna tare da shi.
Sheikh ya ci gaba da cewa: Rundunar Imam Al-Hassan (a), sun rarrabu a akidarsu da kuma shugabancinsu, Wasu daga cikinsu, shi’an Imam Al-Hassan ne, da mahaifinsa(a), suna suna masa biyayya a kan duk abinda ya umurcesu. Sannan yawansu kadan ne sosai a cikin wannan rundunar.
Da wadan nan suna da yawa, da ba’a tilastawa Imam Ali (a) amincewa da Sulhu a Siffin ba, da kuma basu bar Imam Al-Hassan (a) shi kadai da yan tsirari a yakinsa da Mu’awiya wanda ya tilasta masa sulhu da Mu’awiya ba.
Wadan nan sun yi Imani kan cewa shugabanci bayan manzon Allah (s) na iyalan gidan manzon Allah (s) ne, kuma biyayya a garesu wajibi ne. don sune wasiyyan manzon Allah (s). kamar yadda na fadi so kadan ne, kuma an kashe mafi yawansu a yake-yaken Jamal da Siffin.
Sai kuma Khawarijawa a cikin rundunar, wadanda suke ganin da Mu’awiya da Imam Al-Hassan (a) daya ne a wajensu. Sun jinkirta yakar Mu’awiya ko kashe shi ne, zuwa lokacin da zasu sami damar hakan, idan sun sami nasara a kansa, kashe Imam Al-Hassan a wajensu mai sauki ne, Tunda sun kashe mahaifinsa kafin sa. Don haka wannan itace ikidarsu da kuma matsayinsu, duk da cewa a Zahiri suna cikin rundunar Imam Al-Hassan (a).
Sai kuma wasu daga cikin rundunar Imam Al-Hassan (a) suna jiran duk wata dama da cimma manufofinsu na duniya, babu ruwansu da wanda yake da iko, duk wanda ya sami nasara suna tare da shi. Suna neman duk anda masalaharsu ta duniya take. Babu ruwansu da addini. Ba addini ne a gabansu ba.
Sannan akwai wasu kuma suna tsaka-tsaki, suna shakka, a cikin al-amura, kuma a cikin wannan halin ne Mu’awiya ya jawo hankalin mafi yansu tare da yawan kyaututtuka, da bada cin hanci da rashawa. Hakama Khawarijawa sun janye da dama daga cikinsu zuwa bangarensu, wanda ya kara jefasu cikin shakku kan Iyalan gidan manzon Allah (s) suna manta da shirinsu na gwara. Da kuma kyautata mummunan halin da musulmi suke. Iran wadan nan suna da yawa a cikin rundunar Imam Al-Hassan. Saboda rashin fahintar addini, da kuma kokarinda shuwagabannin da suka gabata suka yi na nesanta Iyalan gidan manzon Allah (s) daga mutane, da boye ]matsayinsu a cikin al-ummar musulmi. Don haka da dama suka jahilce su.
Wadan nan gaba daya hatsari ne ga nasarar Imam Al-Hassan (a) a yakin da yake fuskanta da Mu’awiya dan Abu Sufyan. Amma mafi hatsari daga cikinsu su ne, kabilun larabawa wadanda ba sa Kallon kowa da girma sai shuwagabannin kabilunsu, sannan su suka fi yawa a cikin rundunar Imam Al-Hassan (a).
Wadan nan basa da wani tunani nasu, basa ganin wajibcin biyayya ga shuwagabannin addini, a wajensu shugaban kabilarsu shi ne kome. Duk inda ya je suna tare da shi. Wannan al-adace ta kabilun larabawa tun Jahiliya, abin mamaki har zuwa lokacin basu fahinci cewa addinin musulunci ya zo ya hana irin wannan fahintar ba.
Malaman tarihi sun bayyana cewa, mafi yawan mutanen kasar Iraki a lokacin har zuwa yau suna bin shuwagabannin kabilarsu ne, ba addini ba. Wannan ne yasa a lokacinda shugabannin kabilun kinda da sauransu, wadanda suka hada da Kais ibn Ash’ash Al-kindi, da Amru dan Hajjaj da Hajjar bin Abjar da wasu shuwagabannin kabilu cikin Khawarijawa suka rubutawa Mu’awiya wasku kan cewa zasu yi masa biyayya sannan sun yi Alkawalin zasu kashe shugaban matasan Aljanna Imam Alhassan (a) ko su kama shi su mika ga makiyansa.
Mafi yawan mutanen Iraki a lokacin suna karkata zuwa ga kabilarsu, bisa mafi yawan al-amura hatta a kan al-amarin addini.
Sannan wani abu mai muhimmanci da ya faru a lokacinda malaman tarihi suka zo rubuta tarihi shi ne sun ya kura-kurai, ko kuma mu ce wasu daga cikinsu da gangan suka sauya hakikanin abinda ya faru a sulhun da Imam Al-Hassan yayi da Mu’awiya, inda suka sauya gaskiya, suka kuma rubuta tarihin yadda Mu’awiya dan Abusufyan da Banu’umayya suke son ya kasance.
Da farko, Hakim Nishaburi a cikin littafinsa Al-Mustadrak, ya kawo cewa: Imam Al-Hassan (a) yad ora dan Amminsa Abdullahi dan Jaafaru kan shugabancin rundunarsa, ya kuma sanya shi kwamandan sojojin dubu 10. Wanda ya sabawa dukkan malaman tarihi wadanda suka ruwaiti wannan bangare na tarihin musulunci. Inda suka nuna cewa Imam Al-Hassan (a) ya dora Ubaidullahi dan Abbas kan Rundunarsa, tare da sanya Kai dan Sa’ad tare da shi, da kuma Sa’id dan Kai. Kuma runduna ta gaba ta kunshi mayaka dubu 12 ne, ba dubu 10.
Sannan Ya’kubi ya kawo a cikin tarihinsa kan cewa, Imam Al-Hassan (a) ya shirya yaki da Mu’awiya a cikin kwanaki 18 kacal da shahadar Mahaifinsa Amirulmuminina (a).
Wanda wanna ma ba haka banez, saboda abinda mafi yawan malaman tarihi suka tafi a kai shi ne, cewa Imam Al-Hassan (a) y afara da rubuta wa Mu’awiya wasiku, sai da suka dauki kimani watanni biyu suna musayar wasiku, kamar yadda muka kawosu a shirye-shiryemmu da suka gabata. Ya bi duk hanyoyin da za’a kaucewa yaki, da kuma gyara al-amuran musulmi ba tare da zubar da jininsu ba, amma Mu’awiya ya ki amincewa, sannan bayan da ya sami labarin cewa Mu’awiya ya fito daga Sham da rundunarsa don yakarsa ne, sai shi kuma ya tara mayaka ya fito daga kufa da fatan zasu hadu a siffin.
Sannan ibn Kakhir a cikin tarihinsa, yana cewa: Imam Al-Hassan bai da niyyar yakar Mu’awiya kwanta-kwata sai da mutane suka yi gangami a Kufa, gangamin da basu taba yin irinsa ba. suka bukaci ya fito yakar Mu’awiya tare da su, a nan ne sai (a) ya sanya Kai dan Sa’ad dan Ubada kan runduna mai mayaka dubu 12. …).
Wannan maganar ba gaskiya bace, saboda , da Imam Al-Hassan (a) bai bukatar yakar Mu’awiya da bai yi musayar wasikun da yayi da shi ba. Da bai kuma yi masa barazanar yaki a cikin wasikun ba.
In ba bai yi niyyar yakarsa ba, da bai haw kan mimbari ya kodaitar da mutane yakarsa da kuma yin jihadi a kan tafarkin Allah kamar yadda muka bayyana a shirye-shiryemmu da suka gabata ba.
Sai kuma Taha Hussain a cikin littafinsa ‘Aliyu wa Banuhu” : yana cewa Imam Al-Hassan (a) ya yi watanni biyu bayan yi masa bai’a bai yi maganar yakar Mu’awiya ba, sai da Kais dan Sa’adu dan Ubada, da Abaidullahi dan Abbas, suka matsa masa. Sannan Abdullahi dan Abbas daga Makka ya rubuta masa wasika yana kodaitar da shi yakar Mu’awiya, a sannan ne ya tashi ya fara Shirin yaki.) (195 Aliyu wa banuhu.).
Wannan shi ne ra’ayin Ibn Kathir, mai yuwa daga wajensa ne Taha Hussain ya dauka, amma ga wanda ya karanta wasikun da Imam Al-Hassan (a) ya yi musayarsu da Mu’awiya, wadanda kuma muka gabatar a baya, zai fahinci cewa Imam (a) yana Shirin yakar Mu’awiya tun bayan da aka yi masa bai’a. A cikin daya daga cikin wasikun yana cewa
{..idan ka ki amincewa sai ci gaba da tawaye, to kuwa zan kama hanya zuwa wajenka tare da musulmi, har sai Allah yayi hukunci Tsakanimmu shi ne mafi alkhairin masu hukunci..}
Banda haka, mu’awiya ne ya raba kan musulmi, tunda musulmi gaba daya sun yiwa Amirulmuminina (a) bai’a a Madina, wadanda basa madina sun aiko da wakilansu, sun kuma bayyana biyayyarsu gareshi. Ba wanda ya ki hakan inda banda Mu’awiya dan Abu Sufyan a Sham. Da sunan neman jinin Khalifa Uthman, wanda daga baya ya tabbata Khalifanci yake so ba neman Jinin khalifa Uthman ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Duniyarmu A Yau: Sabon Kuduri Mai Yin Allawadai Da Iran A Hukumat IAEA November 22, 2025 Ghalibaf: Makiya Sun Sawya Dabarbarun Yaki Da Iran November 22, 2025 Tsohon Ma’aikacin CIA Ya Ce HKI Ta Yi Barazanar Amfani Da Makaman Nukliya Kan Iran November 22, 2025 Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Sami Rarrabuwar Kai Dangane Da ‘Keshe Kiristoci A Najeriya’ November 22, 2025 Kasar Ukraine Ta Ki Amincewa Da Sabon Shirin Amurka Na Kawo Karshen Yaki A Kasar November 22, 2025 Yan Wasan Kasar Iran Sun tashi Da Lambobin Yabo 81 A Wasannin Zumunci Tsakanin Kasashen Musulmi November 22, 2025 Shugaban Rasha yace Ba zai Janye Ayyukan Soji Da Yake Yi A Kasar Ukrain Ba November 21, 2025 Kwamitin Sulhu Na MDD Ya yi Tsokaci Kan Rashin Tsaro A Najeriya November 21, 2025 Araqchi: Iran Ta Shirya Tsaf Fiye Da Kowanne Lokacin Musamman Bayan Yakin Kwanaki 12 November 21, 2025 China ta ce Ya Kamata A Aiwatar Da Sakamakon Taron Kolin Tianjin Don Inganta Kungiyar SCO November 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci