A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas tun farko.

Tinubu ya bayyana matakin ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan shafe watanni ana rikicin siyasa da ke barazana ga harkokin mulki da tsaro a jihar mai arzikin man fetur. Cikakken bayanai na nan tafe…

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Tabbatar Da Adalci Ga Falasdinawa Wajen Maido Da Hakkinsu Na Kasa

Dangane da halin da ake ciki game da rikicin Falasdinu da Isra’ila, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin 22 ga wata cewa, karfin soja ba zai iya samar da zaman lafiya ba, kuma tashin hankali ba zai iya samar da tsaro ba. Kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen ci gaba da jajircewa a kan tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin da ake yi a zirin Gaza, da kuma matukar nuna goyon baya ga tabbatar da adalci ga al’ummar Falasdinawa wajen maido da hakkinsu na kasa, da kuma kara azamar warware matsalar Falasdinu tun da wuri ta hanyar samar da cikakkiyar mafita, mai adalci da kuma dorewa.

Guo Jiakun ya ce, kawo karshen rikicin cikin hanzari da samar da dawwamammen zaman lafiya, shi ne babban burin al’ummar Falasdinu da Isra’ila da kuma yankin Gabas ta Tsakiya, kuma wannan aiki ne na gaggawa da ke gaban kasashen duniya. Kasar Sin ta yi imanin cewa, a halin da ake ciki yanzu, ya zama tilas a karfafa tsagaita bude wuta a zirin Gaza, tare da daukar matakin gaggawa domin rage radadin bala’in jin kai a yankin.

Ya ci gaba da cewa, ya kamata kasashen da ke da tasiri na musamman a kan Isra’ila su sauke nauyin da ke wuyansu. Dole ne a aiwatar da ka’idar barin “Falasdinawa su mulki Falasdinu” bisa turbar gaskiya, kuma dole ne a kiyaye hakkin kasar Falasdinu kan batutuwan da suka shafi shugabanci bayan yaki da kuma shirye-shiryen sake gina kasar. Kazalika, a cewarsa, dole ne a ci gaba da bibiyar shawarar “kafa kasashe biyu” ba tare da kakkautawa ba, da samar da karin fahimtar juna da cimma matsaya tsakanin kasa da kasa da kuma yin watsi da duk wani mataki na bangare guda da zai iya yin kafar ungulu a kan “kafuwar kasashe biyu”. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gavi Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Yi Masa Tiyata
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Tabbatar Da Adalci Ga Falasdinawa Wajen Maido Da Hakkinsu Na Kasa
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tattalin Arzikin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 4.32 A 2025
  • Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau
  • Babu Gwamnatin Sojin Da Ta Kai Ta  Tinubu Muni A Tarihin Nijeriya
  • Bayan Mutuwar Wani Matashi, An Kafa Dokar Ta Baci A Yauri
  • Bayan Nesanta Kanta, Jami’ar European American Ta Yi Wa Rarara Tayin Digiri
  • Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro