Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi
Published: 24th, September 2025 GMT
Wata kotu ta musamman a Coimbatore da ke kasar Indiya, ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Samson Chukwunonso hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari kan laifin safarar miyagun kwayoyi.
Jaridar Times of India ta ruwaito cewa lamarin ya faro tun a watan Yuli na shekarar 2012, lokacin da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta India (NCB), reshen Chennai, suka kama wasu fakiti guda uku a ofishin aika sakonni.
A cikin fakitin, an gano tabar wiwi mai nauyin kilo 1.195 da methaqualone giram 200, wanda darajarsa ta haura kimanin Dalar Amurka 240,000 a kasuwar duniya.
Bincike ya gano cewa fakitin na da alaka da Samson mai shekaru 40, wanda ake zargin yana zaune ba bisa ka’ida ba a kasar.
Jami’an na NCB sun kai samame gidansa inda suka gano ganja kilo 4, lamarin da ya kai ga cafke shi a watan Satumba 2012.
Bayan tambayarsa, an gano cewa Samson yana shirya aika miyagun kwayoyi zuwa kasashen waje ta hanyar kamfanonin aika sakonni, kuma yana da hannu a kungiyoyin safarar kwayoyi na duniya.
A ranar Asabar, 20 ga Satumba, an gurfanar da shi a gaban mai shari’a Rajalingam a kotun musamman da ke karkashin dokar hana safarar miyagun kwayoyi.
An same shi da laifin shirya aika kwayoyi zuwa kasashen waje a matsayin wani bangare na wata babbar kungiyar safarar kwayoyi ta duniya, kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari tare da tara ₹1 lakh.
Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kama ’yan Najeriya da dama a kasashen Asiya kan laifukan da suka shafi safarar kwayoyi da aikata laifuka na kasa da kasa.
Ko a watan Agusta, sai da ’yan sanda a birnin Kozhikode na kasar ta Indiya suka kama ’yan Najeriya takwas kan zargin safarar kwayoyi.
Jaridar The Hindu ta ce ana zargin su da taka rawa a wata babbar kungiyar safarar kwayoyi da ke da rassa a fadin India.
A wani rahoto makamancin haka, wata kotu ta musamman a gundumar Bengaluru ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Kingsley Samuel hukuncin daurin shekaru 14 kan safarar kwayoyi, lamarin da ke kara nuna yadda ’yan Najeriya ke kara shiga harkar safarar kwayoyi a India.
Yawan kamawa da yanke hukunci ga ’yan Najeriya a kasashen waje na ci gaba da haifar da tambayoyi kan yadda ake kallon Najeriya a idon duniya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Indiya Safarar kwayoyi safarar kwayoyi miyagun kwayoyi yan Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu
“Lamarin daya kai miliyan daya na wadanda suka nemi a basu bashin karatu, lalle abin ya nuna a gaskiya matasa sun son su kyautata yadda rayuwarsu data wasu zata kasance a gaba, musamman ma yadda suka maida hankali wajen neman ilimi.
Ya ci gaba da bayanin “Wannan yana nunawa a fili yadda jagorancin na Shugaban kasa Bola Tinubu ya damu da lamarin ilimi domin shi ne ginshikin ci gaban al’umma kamar yadda ya ce,”.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA