Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 27 a wani sabon harin bam
Published: 20th, November 2025 GMT
Rahotanni daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 28 tare da raunata wasu 77 a zirin Gaza, wanda ke nuni da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a shiga tsakanin Amurka.
Rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida sun nuna cewa mata da yara 17 suna cikin wadanda Isra’ila ta yi wa kisan gilla.
Sojojin Isra’ila sun kuma tabbatar da kai hari kan al-Mawasi a Khan Younis, kudancin Gaza.
Isra’ila ta kai hare-hare uku daban-daban a birnin Gaza da ke arewacin yankin Falasdinawa da kuma kudancin Khan Younis, a cewar hukumar Falasdinawa.
Hukumomin lafiya na Falasdinawa sun ce sojojin Isra’ila sun kai hare-hare 393, inda suka kashe akalla Falasdinawa 290 tare da raunata wasu kusan 700 a hare-haren da suka kai a fadin Gaza tun bayan tsagaita wuta a ranar 10 ga Oktoban da ya gabata.
Kisan kare dangi da Isra’ila ta yi a Gaza ya kashe Falasdinawa sama da 69,000, galibi mata da yara, tare da raunata wasu sama da 170,000 tare da mayar da yankin kufai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : daftarin kudurin da Canada ta gabatar, siyasa kawai da kin jinin Iran November 20, 2025 AU ta yi Allah-wadai da tsoma bakin kasashen waje a harkokin tsaron Afirka November 20, 2025 Amurka ta Shawarci Ukraine ta amince da yankunan da Rasha ta mamaye mata November 20, 2025 Sudan ta yaba da kokarin Amurka da Saudiyya na kawo karshen rikicin kasar November 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: A Yanzu Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka November 19, 2025 Sojojin Yemen Suna Da Makami Mai Linzami Da Babu Mai Makamancinsa Sai Iran November 19, 2025 Daraktar Hukumar IAEA Ya Ce: Suna Tuntubar Juna Da Iran Kuma Masu Bincikensu Sun Kamo Kasar November 19, 2025 Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta A Gaza Kusan Sau 400 November 19, 2025 Kotu A Gabon Ta Yanke Hukuncin Dauri A Kurkuku Kan Jami’an Tsohuwar Gwamnatin Kasar November 19, 2025 Kasar Maziko Tayi Watsi Da Shirin Trump Na Kai Harin Soji Kan Iyakar Kasar. November 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila ta
এছাড়াও পড়ুন:
Tsohon jami’an MDD Yayi Tir Da Amincewa Da Kudurin Amurka A Kwamitin Sulhu Kan Gaza
Rahotanni sun bayyana cewa Craig mokhiber tsohon babban jami’in hukumar kare hakkin dan adam na majalisar dinkin duniya ya sanar a hukumance yin Allah wadai da kuri’ar amincewa da kudurin Amurka da aka yi a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na aikewa da dakarun kasashen waje zuwa yankin Gaza yace wannan baban abin kunya ne.
Kalaman nasa ya nuna irin suka da kungiyoyin kasa da kasa suke yi ne kan mummunan tasirin da yakin yayi wa yankin gaza, da kuma kasa tsagaita wuta da yadda za’a shigar da kayayyakin agaji zuwa yankin
Isra’ila ta toshe kafar shigar da magunguna da kayayyakin lafiya da kuma hana fitar da marasa lafiya sama da 16500 zuwa wajen don yi musu maganin, bayan da cibiyoyin kula da lafiya suka rushe baki daya ya bar marasa lafiya da dama a yashe ba tare da kulawa ba.
Daga ranar 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 da isra’ila ta kaddamar da hari kan gaza zuwa yanzu Kimanin mutane 68872 ne suka yi shahada akalla 170,000 kuma suka jikkata dubbai kuma sun bace bata sama ko kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mataimakin Shugaban Iran Na Daya Ya Gana Da Prime Ministan Rasha A Birnin Mosko November 18, 2025 Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin November 18, 2025 Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF November 18, 2025 MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci