Mun Kawo Ƙarshen Dogon Layin Mai Na Shekara 50 A Nijeriya – Matatar Dangote
Published: 20th, September 2025 GMT
A baya, ƙasashe biyu kawai na Afirka ba sa shigo da man fetur, amma abin takaici, yanzu sun koma shigo da kaya. Wannan yana da illa ga Afirka,” in ji shi.
Dangote ya bayyana cewa aikin masana’antar ya kasance mai haɗari sosai. Ya ce ya samu gargaɗi sau da dama daga masana harkokin mai, masu zuba jari, da jami’an gwamnati na cikin gida da waje, waɗanda suka yi jayayya cewa irin wannan aikin masana’antar mai girma manyan ƙasashe ne kaɗai ke iya yi, ya amince cewa da aikin ya gaza, zai rasa dukiyoyinsa ga masu ba da rance.
“Yanke shawarar gina masana’antar ba abu ne mai sauƙi ba. Idan ya gaza, masu ba da rance za su daka wawa a dukiyoyinmu. Amma mun yi imani da Nijeriya da Afirka,” in ji shi.
Duk da adawar da ƙalubalen tattalin arziki, masana’antar ta rage farashin man fetur daga kusan Naira 1,100 kafin fara samarwa zuwa Naira 841 a yankunan Kudu maso Yamma, Abuja, Delta, Riɓers, Edo, da Kwara. Tare da ci gaba da amfani da motoci masu amfani da CNG, Dangote na sa ran wannan rage farashin da zai shafi ƙasa baki ɗaya nan ba da jimawa ba.
Dangote ya jaddada cewa manufar masana’antar ba ta maye gurbin ma’aikata ba, sai dai tana ƙirƙirar dubban sabbin damar aiki. Ana sa ran amfani da motoci 4,000 masu amfani da CNG zai samar da aƙalla ayyuka 24,000 a faɗin Nijeriya.
“Ba mu maye gurbin ma’aikata ba; muna ƙirƙirar ayyuka da yawa. Motocin CNG ba za su yi aiki da robot ba. Ma’aikatanmu na karɓar albashi sau uku fiye da mafi ƙarancin albashi. Direbobinmu na samun albashi mai rai, inshorar rayuwa, inshorar lafiya da ke rufe su, matan su, da har zuwa yara huɗu, har da fansho na rayuwa. Ba wai kawai muna ɗaukar direbobi ba, har ma da masu gyaran mota, manajoji na jirgin motoci, da sauran ƙwararru don tallafawa jirgin motoci na CNG.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: masana antar
এছাড়াও পড়ুন:
An Rufe Makarantu 6 Masu Zaman Kansu A Kano Saboda Karin Kudin Makaranta Da Tilasta Iyaye Sayen Littafai
A ci gaba da kokarin da take yi na tsaftace harkar ilimi, wata kotu a Kano ta bayar da umarnin rufe wasu makarantu masu zaman kansu nan da nan, 6 saboda saba ka’idojin jihar da suka hada da kara kudin makaranta da kuma tilasta iyayen yara sayan litattafai na dole da sauran tsarabe-tsarabe da suka dorawa iyayen yara.
Sakataren zartarwa na hukumar kula da cibiyoyi masu zaman kansu da sa kai na jihar Kano (KSPVIB), Kwamared Baba Abubakar Umar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai.
A cewarsa, makarantun da abin ya shafa sun hada da Prime College, Darul Ulum, Gwani Dan Zarga College, Unity Academy, Dano Memorial Academy, da Auwa Academy.
Ya yi nuni da cewa hukumar tana kuma jiran umarnin kotu na rufe makarantar Nurul Islam da kwalejin As-Saif.
“Makarantun sun kara kudade ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba, kuma sun kasa mika jerin sunayen litattafai yadda ya kamata ga iyaye, da sauran laifuka,” in ji Baba Umar.
Sakataren zartarwa wanda ya zama mai ba gwamna shawara na musamman kan cibiyoyi masu zaman kansu da na sa kai ya bayyana cewa an umurci makarantun da abin ya shafa da su dakatar da duk wasu harkokin ilimi har sai an kammala zaman kotun da aka shirya yi a ranar 30 ga Satumba da 7 ga Oktoba, 2025.
Baba Umar ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar ta kafa ofisoshin shiyya ta KSPVIB a fadin kananan hukumomi 44 domin sa ido da kuma dakile haramtattun makarantu da kuma cibiyoyin da ke bijirewa dokokin jihar.
Ya jaddada cewa gwamnati a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta baiwa ilimi fifiko, inda ya nuna cewa a cikin sama da makarantu masu zaman kansu da na sa kai sama da 7,000 da ke Kano, kusan 2,700 ne kawai ke da rijista.
“Tarin bayanai yana da mahimmanci don ingantaccen tsarin ilimi, tsara tsarin karatu, tura malamai masu inganci, da samar da ingantaccen yanayin koyo,” in ji shi.
Yayin da yake bayyana mahimmancin makarantu a cikin tsarin ilimi, ya jaddada cewa masu mallakar su dole ne su bi ka’idoji.
“Ba ma son rufe ko dakatar da makarantu, amma da yawa daga cikin masu hannun jari suna ganin sun fi karfin bin doka, ina so in tabbatar muku da cewa a jihar Kano, babu wata makaranta da ta fi karfin doka,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su tabbatar da biyan kudaden makaranta a kan lokaci, domin hakan yana baiwa makarantu damar biyan albashin ma’aikata da inganta tsarin ilimi.
Kwamared Umar ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta bunkasa ilimi a duniya.
COV/Khadija Aliyu