Aminiya:
2025-11-21@14:56:38 GMT

Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa

Published: 21st, November 2025 GMT

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa.

Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano.

An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su

An dakatar da Yauyayin da ake bincike a kansa.

Bayan sanar da dawo da shi kan kujerunsa, dubban magoya bayansa ne suka tarbe shi da murna a kan iyakar Rano da Bunkure.

Daga nan ya wuce zuwa fadar Sarkin Rano, Muhammad Isa Umaru, wanda ya yi masa addu’a kafin ya sake komawa ofis ɗinsa da ke sakateriyar Ƙaramar Hukumar Rano.

Da yake yi wa ma’aikata da magoya bayansa jawabi, Yau, ya gode wa Allah da Ya tsare masa mutuncinsa.

Sannan ya gode wa Majalisar Dokokin jihar da ta wanke shi.

Ya yi godiya ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Gwamna Abba Kabir Yusuf, shugabannin NNPP da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen dawo da shi kan kujerarsa.

Tun farko an dakatar da shi ne bayan kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafe na majalisar ya miƙa rahoton wucin-gadi.

Rahoton ya zarge shi da aikata ba daidai ba, cin zarafin ofishinsa, karkatar da dukiyar jama’a da kuma aikata rashin gaskiya wajen sarrafa kuɗaɗen gwamnati.

Sauran zarge-zargen sun haɗa da haifar da rikici tsakanin shugabannin siyasa, sayar da taki sama da farashin da gwamnati ta ƙayyade, da kuma rashin bayyana gaskiya wajen karɓar kuɗaɗen haraji na kasuwanni.

Haka kuma an zarge shi da sayar da rumfunan kasuwa ba bisa ƙa’ida ba.

Yanzu da an wanke shi daga dukkanin zarge-zargen, ya koma bakin aikinsa a matsayin Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Majalisar Dokoki Rano Yau Zarge zarge Ƙaramar Hukumar Rano

এছাড়াও পড়ুন:

Araqchi: Yarjejeniyar  Da Aka Cimma Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA A Kasar Masar Ta Rushe

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yarjejeniyar Alkahira tsakanin Iran da IAEA ba ta da inganci

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: Iran ta sanar da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) cewa: Yarjejeniyar Alkahira ba ta da inganci a martanin kudurin da ta bayar, yana mai nuni da cewa yarjejeniyar ta rasa rawar da take takawa a matsayin tsarin hadin gwiwa tsakanin Iran da IAEA.

Da yake mayar da martani ga kudurin da kwamitin Gwamnonin IAEA ta dauka kan Iran, Araqchi ya ce: “Sun sanar da IAEA cewa Yarjejeniyar Alkahira ba ta da inganci a martanin kudurin da ta bayar.”

Ministan harkokin wajen Iran ya kara da cewa: “Yarjejeniyar Alkahira ta rasa rawar da take takawa a matsayin tsarin hadin gwiwa tsakanin Iran da IAEA.”

Araghchi ya yi nuni da cewa: ‘Tawagar Turai da Amurka sun yi watsi da fatan alherin Iran ta hanyar gabatar da daftarin kuduri ga Kwamitin Gwamnonin IAEA.

Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: ‘Tawagar Turai da Amurka sun lalata sahihancin Hukumar IAEA da ‘yancin kanta kuma sun kawo cikas ga hadin gwiwar Iran da ita.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kakakin Rundunar ‘IRGC’: Yakin Kwanaki 12 Ya Nuna Karfin Kariyar Makaman Masu Linzamin Iran November 21, 2025 Iran Da Wasu Kasashe Bakwai Sun Mayar Da Martani Kan Hudurin IAEA Kan Kasar Iran November 21, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Kiran Da A Sanya Isra’ila Cikin Jerin Masu Aikata Abin Kunya Saboda Kashe Yara November 21, 2025 Tarayyar Turai Ta Kakaba Takunkumi Kan Dan Uwan Kwamandan Rapid Support Forces Ta Sudan November 21, 2025  Iran Tana Cikin kasashe 10 Na Farko Da Su Ka Fi Yawan Wuraren Tarihi November 20, 2025 Nigeria:Kotu Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Zaman Kurkuku Na Har Abada   November 20, 2025 Nigeria: An Rufe Makarantun Kwana A Jahar Kwara Saboda Matsalar Tsaro November 20, 2025 Hizbullah: Ba Za Mu Taba Ajiye Makamanmu Ba November 20, 2025 Ribadu Ya Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Amurka Kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla November 20, 2025 Hukumar Kula Da Jiragen Sama Ta Najeriya Ta ci Tarar Kamfanin Jiragen Sama Na Qatar November 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araqchi: Yarjejeniyar  Da Aka Cimma Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA A Kasar Masar Ta Rushe
  • Za a aurar da marayu 200 a Zamfara
  • IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka
  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro
  • Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano
  • Kotu ta sanya ranar fara shari’ar shugabannin ƙungiyar Ansaru
  • Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa
  • An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari
  • Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe