DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato
Published: 21st, November 2025 GMT
Hukumar DSS ta mayar d Shugaban ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), zuwa gidan gyaran hali a Jihar Sakkwato.
Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke masa na ɗaurin rai da rai kan laifukan ta’addanci.
Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsaA ranar Alhamis ne, Alƙalin Kotun Tarayya da ke Abuja, James Omotosho, ya ce DSS za su kai Kanu kowace cibiyar gyaran hali da ke Najeriya.
Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya tabbatar da mayar da shi Sakkwato aranar Juma’a.
Ya ce: “DSS ta ɗauke Mazi Nnamdi Kanu daga gidan yari na Abuja zuwa Sakkwato, sun nesanta shi da lauyoyinsa, iyalinsa, da masoyansa.”
An yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai kan laifuka bakwai da suka shafi ta’addanci.
Kotun ta tabbatar da cewa Kanu ya yi amfani da ta’addanci wajen raba yankunan Kudu-Maso Gabas da Kudu Maso Kudu, da wasu sassan Binuwai da Kogi daga ma Najeriya baki ɗaya.
Hukumomin shari’a sun kuma buƙaci a rufe dukkanin shafukan Kanu, tare da tabbatar da cewa yana cikin tsaro domin ba shi kariya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gidan Yari Sakkwato Shari a
এছাড়াও পড়ুন:
Cibiyar fasaha ta kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin ’yan kasuwa mata a Jihohi 3
Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya.
Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano, tare da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU).
Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’Da take jawabi a wajen kaddamarwar a Kano ranar Talata, shugabar cibiyar, Maryam Lawan Gwadabe, ta ce an kirkiro shirin ne domin samar wa mata amintaccen muhallin da za su yi amfani da shi wajen bunƙasa kasuwancinsu.
Ta ce shirin zai gudana a jihohin Kano, Katsina da Sakkwato domin ƙarfafa tattalin arzikin mata da kuma tabbatar da sun samu dogaro da kai.
“Mun sanya wa shirin suna Women Venture Studio domin tabbatar da cewa mata za su ji daɗin kasancewa a cikin muhalli mai tsaro. Masu ba da shawara a nan su ne ’yan kasuwa da matan da suka yi nasara, waɗanda za su saurara, su jagoranta, kuma su tallafa wa mahalarta shirin,” in ji ta.
Maryam ta ƙara da cewa cibiyar tana bayar da wuraren yin aiki na zahiri da na intanet, domin tabbatar da cewa ana damawa da mat aba tare da an ware su ba.
Shugabar cibiyar ta kuma ce matakin farko na shirin zai haɗa da horar da mata 150, wato mata 50 daga kowacce jiha.
Ita ma da take jawabi, Shugabar ANWE, Hafsat Sahabi Dange, ta ce shirin ya fi mayar da hankali kan mata a fannin kirkira, musamman a harkar dinka kaya, sana’o’in hannu da fasaha.
“Manufarmu ita ce mu sauya waɗannan kasuwancin zuwa tsarin zamani domin mata su iya yin gogayya, ba kawai a Najeriya ba, har ma a duniya. Wannan shiri zai shafi ’ya’ya mata da kuma mata ta hanyar amfani da kirkirarsu da kuma ƙarfafa musu tsarin kasuwanci a Arewacin Najeriya,” in ji ta.
A nata bangaren, wakiliyar Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS, Inga Stefanovic, ta ce EU ta ware sama da Yuro miliyan 700 a matsayin tallafi domin tallafa wa ayyuka daban-daban a fadin Najeriya.
Ta jaddada cewa haɗin gwiwar EU da Najeriya ya shafi fannoni da dama ciki har da fasahar zamani, bunkasa tattalin arziki, dimokuraɗiyya, zaman lafiya da tsaro, lafiya, ilimi, samar da makamashi da kuma noma.