Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya.

Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Gaza.

Wardley ya zama zakaran damben boksin na duniya Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana

A farkon wannan watan ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana Najeriya cikin jerin ƙasashen matsala ta musamman.

Sannan Trump ya umarci wasu ’yan majalisar Amurka, ciki har da Ɗan Majalisa Riley Moore da su binciki lamarin.

Duk da ƙoƙarin da Najeriya ta yi na bayyana haƙiƙanin abin da ke faruwa bai sa wasu jami’an Amurka sun sauya ra’ayi ba.

Daga cikin tawagar akwai: Bianca Ojukwu, Ƙaramar Ministar Harkokin Waje; Kayode Egbetokun, Sufeto Janar na ’Yan Sanda; Lateef Olasunkami Fagbemi, Antoni-Janar na Ƙasa; Janar Olufemi Olatunbosun Oluyede, Shugaban Ma’aikatan Tsaro; da Laftanar Janar E.A.P. Undiendeye, Shugaban Leƙen Asirin Tsaro na Ƙasa.

Sauran sun haɗa da Idayat Hassan, Jakada Ibrahim Babani, Daraktan Hulɗar Ƙasashen Waje a ONSA; Jakada Nuru Biu, Mai Riƙe da Muƙamin CDA na Ƙasashen Waje a Ma’aikatun Jakadancin Najeriya; da Paul Alabi, daga Sashen Siyasa da Tattalin Arziƙi a Ofishin Jakadancin Najeriya.

A ranar Talata, an gayyaci fitacciyar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj zuwa zauren Majalisar Ɗinkin Duniya domin gabatatar da jawabi, inda ita ma ta nemi a kai wa Kiristocin Najeriya ɗauki.

Sai dai ba a bai wa Najeriya damar halartar taron ba wanda ya gudana a Birnin New York, lamarin da ya ƙara tayar da ƙura.

Wakilin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Syndoph Endoni, ya ce hakan tamkar “aske mana kai ba tare da mu ba.”

A ranar Laraba, tawagar Najeriya ta gana da Ɗan Majalisar Amurka Moore domin tattaunawa kan matsalolin tsaro a ƙasar da ƙoƙarin gwamnati ke yi na shawo kan tashe-tashen hankula.

Bayan ganawa da wakilan gwamnatin Najeriya, Moore ya ce ya fahimci yadda abubuwan suke.

Moore ya ce: “Yau na yi magana ta gaskiya, a buɗe kuma mai amfani da manyan jami’an gwamnatin Najeriya game da mummunan tashin hankali da bazaranar da Kiristoci ke fuskanta a faɗin Najeriya.

“Na bayyana a fili cewa dole Amurka ta ga an ɗauki ƙwararan matakai da za su tabbatar da cewa Kiristoci ba su fuskanci tashin hankali, zalunci, ko kisa saboda ba saboda sun gaskata Yesu Almasihu.”

Ya kara da cewa: “Mun shirya mu yi aiki tare da ’yan Najeriya domin taimaka musu su yaƙi ta’addancin da Boko Haram, ISWAP, da makiyaya Fulani ke aikatawa musamman a kan Kiristoci a yankin Arewa maso Gabas da Kudancin Kaduna da sauran yankunan Najeriya.”

Haka kuma Moore ya ce: “Gwamnatin Najeriya na da damar ƙarfafa dangantakarta da Amurka.

“Shugaba Trump da Majalisa sun haɗa kai kuma suna da niyyar kawo ƙarshen tashin hankalin da Kiristoci ke fuskanta da kuma karya ƙungiyoyin ta’addanci a Najeriya.

“Ina kira ga ’yan Najeriya su yi aiki tare da mu cikin haɗin kai domin magance wannan babban lamari.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, tawagar Najeriya ba ta fitar da sanarwarta kan wannan ziyara ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Arewa maso Gabas Boko Haram Makiyaya Tawaga zargi wa Kiristoci

এছাড়াও পড়ুন:

Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa

Kafofin yada labaran kasar Rasha sun rawaito a jiya Litinin cewa an dakile wani yunkurin kisan gilla kan sakataren majalisar tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu a makabartar Troyekurov da ke birnin Moscow.

Kafofin yada labaran kasar Rasha sun rawaito majiyoyi suna bayyana cewa wadanda suka aikata laifin sun yi yunkurin tayar da bam ne a lokacin ziyarar Shoigu a kaburburan ‘yan uwansa.

Kazalika majiyoyin sun tabbatar da kame dukkan wadanda ake zargin tare da dakile shirin nasu, kamar yadda kafafen yada labaran Rasha suka rawaito.

Shoigu ya taba rike mukamin ministan tsaron kasar Rasha daga shekara ta 2012 zuwa 2014 kafin shugaba Vladimir Putin ya nada shi sakataren kwamitin tsaron kasar ta Rasha, wanda ya zama babban mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasar baki daya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama miji da mata kan zargin mallakar buhuna 360 na Tabar Wiwi
  • Cibiyar fasaha ta kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin ’yan kasuwa mata a Jihohi 3
  • Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya
  • Saudiyya za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya
  • Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis
  • Najeriya ta Fara tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi
  • Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa
  • Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
  • Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya