Iran : daftarin kudurin da Canada ta gabatar, siyasa kawai da kin jinin Iran
Published: 20th, November 2025 GMT
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa daftarin kudirin da kasar Canada ta gabatar yana cike da siyasa ne kawai hasali ma nuna kin jinin Iran ne.
Mataimakin Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, game da daftarin kudurin da Canada ta gabatar, ya ce: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna adawarta ta musamman ga wannan daftarin, wanda aka yi shi bisa dalilai na siyasa, son rai, da kuma na neman haddasa barna.
Gholamhossein Darzi, Jakadan Iran kuma Mataimakin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana a ranar Laraba, a lokacin zaman Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na Uku kan kudurin kare hakkin dan adam na Canada kan Iran:
Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa: “Mun yi watsi da abin da ke cikin wannan daftarin da kuma manufar da ke bayansa.
Mataimakin Wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce: Irin wadannan ayyuka suna raunana tattaunawa ta gaskiya, suna lalata aminci, wanda ya kamata ya jagoranci aikin Majalisar Dinkin Duniya a fannin hakkin dan adam.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka AU ta yi Allah-wadai da tsoma bakin kasashen waje a harkokin tsaron Afirka November 20, 2025 Amurka ta Shawarci Ukraine ta amince da yankunan da Rasha ta mamaye mata November 20, 2025 Sudan ta yaba da kokarin Amurka da Saudiyya na kawo karshen rikicin kasar November 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: A Yanzu Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka November 19, 2025 Sojojin Yemen Suna Da Makami Mai Linzami Da Babu Mai Makamancinsa Sai Iran November 19, 2025 Daraktar Hukumar IAEA Ya Ce: Suna Tuntubar Juna Da Iran Kuma Masu Bincikensu Sun Kamo Kasar November 19, 2025 Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta A Gaza Kusan Sau 400 November 19, 2025 Kotu A Gabon Ta Yanke Hukuncin Dauri A Kurkuku Kan Jami’an Tsohuwar Gwamnatin Kasar November 19, 2025 Kasar Maziko Tayi Watsi Da Shirin Trump Na Kai Harin Soji Kan Iyakar Kasar. November 19, 2025 Iran Ta yi Gargadi Kan Kada Kudurin Amurka Da MDD Ta Amince Da Shi Ya Tauye Hakkin Falasdinawa November 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin
Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya kai ziyarar aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa don inganta dangantakar soja da kuma huldar tsaro a yankin.
Nasirzadeh ya jagoranci wata babbar tawaga, wadda ta isa Dubai a ranar Litinin bisa gayyatar takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ministan tsaron Iran yana shirin yin tattaunawa da jami’an Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma halartar taron Dubai Airshow na 2025, wanda aka shirya gudanarwa a tsakanin 17-21 ga Nuwamba.
Ziyarar ta zo ne a karkashin tsarin diflomasiyyar tsaron Iran kuma tana da nufin inganta huldar yanki da kuma gano damar yin hadin gwiwa a fannoni daban-daban.
A lokacin rangadin baje kolin, an shirya cewa ministan tsaron na Iran zai yi tarurruka da jami’an tsaro daga kasashe da dama.
Bikin Dubai Airshow na 2025 zai karbi bakuncin masu baje kolin sama da 1,500, wadanda suka hada da sabbin masu baje kolin sama 440, masu Ziyara da ‘yan kasuwa 148,000, da kuma wakilai 490 na sojoji da fararen hula daga kasashe 115.
Za a nuna sama da jiragen sama 200, ciki har da jiragen sama na kasuwanci, na soja, na liken asirri, jiragen sama marasa matuki, da kuma fasahar zamani, wanda shi ne baje koli irinsa mafi girma a tarihi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF November 18, 2025 MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza November 18, 2025 Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci