Kotu Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Zaman Kurkuku Na Har Abada Akan Laifin Ta’addanci
Published: 20th, November 2025 GMT
A zana da kotun ta yi a birnin Abuja a yau Alhamis, mai shari’a James Omotosho ya yanke hukuncin cewa mai shigar da kara ya gabatar da kwararan dalilai akan yadda jawaban da Kanu ya rika watsawa su ka ingiza mambobin haramtacciyar kungiyar ” IPOB” su ka kai wa jami’an tsaro hari a yankin kudu maso gabashin kasar.
Mai shari’ar ya bayyana Kanu a matsayin wanda ya shirya ayyukan da su ka kai ga yin ta’addanci.
A 2009 ne dai Kanu ya fara watsa shirye-shiryen Rediyo Bi’afara daga London, da yake Magana da ‘yan kungiyarsa ta IPOB.
Tun da fari dai Alkalin ya bayar da umarnin a fitar da Nnamdi Kanu daga cikin kotun sabdoa abinda ya kira rashin da’a daga gare shi.
Alkalin kotun koli ta tarayyar Najeriya dake Abuja, ya bayar da umarnin a fitar da shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafra ( IPOB) daga cikin kotu saboda rashin da’ar da ya nuna gababin yanke hukunci a yau Alhamis.
Mai shari’a James Omotosho ya yi watsi da wasu kararraki sabbi da Kanu ya shigar saboda rashin dacewarsu.
Shi dai Kanu yana fuskantar shari’a ne akan tuhumar ayyukan ta’addanci da kungiyarsa ta “IPOB” mai son kafa kasar Biafara ta ‘yan kabilar Igbo.
Mai shari’ar ya kuma ce; saboda rashin da’ar Kanu da kuma halayyarsa ta son rikici, za a yanke hukunci ne ba tare da halarci zaman kotun ba.
A lokacin da mai shari’a yake kokarin yanke hukuni ne dai Kanu ya furta cewa ba shi da hakkin yin hakan saboda bai rubuta jawabinsa na karshe ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Nigeria: An Rufe Makarantun Kwana A Jahar Kwara Saboda Matsalar Tsaro November 20, 2025 Hizbullah: Ba Za Mu Taba Ajiye Makamanmu Ba November 20, 2025 Ribadu Ya Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Amurka Kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla November 20, 2025 Hukumar Kula Da Jiragen Sama Ta Najeriya Ta ci Tarar Kamfanin Jiragen Sama Na Qatar November 20, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Kara Dagulewar Al’amura Bayan Harin Isra’ila A Gaza November 20, 2025 Labanon Ta Bukaci Gudanar Da Taron Kwamitin Tsaro Na MDD Cikin Gaggawa November 20, 2025 Achraf Hakimi Ya Zama Gwarzon Wasan Kwallon Kafar Afirka Na Shekara Ta 2025 November 20, 2025 Kasashen Iran Da Malesiya Sun Rattaba Hannu Kan Jarjejeniyar Fadada Dangantakar Addini November 20, 2025 Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 27 a wani sabon harin bam November 20, 2025 Iran : daftarin kudurin da Canada ta gabatar, siyasa ce da kin jininmu November 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mai shari a
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta A Gaza Kusan Sau 400
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza kusan sau 400
Babban Daraktan Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza, Ismail al-Thawabta, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta aikata laifuka 393 da aka rubuta tun lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Zirin Gaza. Ya jaddada cewa wadannan laifukan sun shafi rayukan fararen hula kai tsaye, da nufin tsoratar da su da kuma fadada barna, ta haka ne ke kara ta’azzara yanayin jin kai da kuma barazana ga makomar kwanciyar hankali.
Al-Thawabta ya kara da cewa, a cikin sanarwar da ya bayar ga Al Jazeera Net, cewa: Yanayin jin kai a Gaza yana kara muni tare da rugujewar tsarin lafiya da kuma rufe sama da kashi 80% na asibitoci, baya ga toshewar abinci mai tsari. Wannan ya faru ne duk da cewa jami’an tsaro suna ci gaba da tabbatar da kwanciyar hankali a cikin gida, suna kula da yanayin da ake ciki a kasa, da kuma kare wuraren da ‘yan gudun hijira ke zaune da kuma cibiyoyin hidima a tsakanin hare-haren da ake ci gaba da kai musu da kuma keta dokokin yau da kullum.
Waɗannan take hakki sun zo ne bayan wani hari da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a yankin Gaza wanda ya ɗauki tsawon shekaru biyu, wanda ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa kimanin 70,000, da kuma raunata wasu sama da 17,000, da kuma dubban mutanen da suka ɓace a ƙarƙashin tarkacen gidajensu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kotu A Gabon Ta Yanke Hukuncin Dauri A Kurkuku Kan Jami’an Tsohuwar Gwamnatin Kasar November 19, 2025 Kasar Maziko Tayi Watsi Da Shirin Trump Na Kai Harin Soji Kan Iyakar Kasar. November 19, 2025 Iran Ta yi Gargadi Kan Kada Kudurin Amurka Da MDD Ta Amince Da Shi Ya Tauye Hakkin Falasdinawa November 19, 2025 kungiyar Hadin Guiwa Ta SCO Ta yi Watsi Da Adawar Da Kasashen Turai Ke Nuna wa Kasar Iran November 19, 2025 Majalisa wakilai A Najeriya Ta Bukaci Gwamnati Ta Sake Dabarun Yaki Da Ta’addanci November 19, 2025 Kimanin Falasdinawa 22 Ne Suka yi Shahada Sakamakon Harin Isra’ila A Ainul Hilwa November 19, 2025 Iran : Dole ne kudirin Amurka ya kare hakkin Falasdinawa da samuwar kasar Falasdinu November 19, 2025 Saudiyya za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya November 19, 2025 Iraki : Jam’iyyar al-Soudani ta samu rinjaye a Majalisar dokoki November 19, 2025 Shugaban gwamnatin Togo zai gana da Shugaba Putin na Rasha November 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci