Aminiya:
2025-09-24@13:56:34 GMT

Yada labaran karya a intanet babban laifi ne a Musulunci – Sheikh Ibrahim Khalil

Published: 24th, September 2025 GMT

Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya gargadi masu yada labaran karya musamman a kafafen sada zumunta da su daina, domin Musulunci ya haramta hakan.

Ya bayyana cewa a Musulunci, yada labaran karya daidai yake da yin karya, kuma addinin Musulunci yana tsananin kin masu karya.

UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi

Sheikh Khalil ya fadi hakan ne a Kano a ranar Talata yayin wani taron horaswa na kwanaki biyu da aka shirya wa malamai da limamai kan yadda za a yaki labaran karya da kuma inganta fahimtar kafofin yada labarai, wanda kungiyar Alkalanci ta shirya, wata kungiya da ke tantance gaskiyar labarai da ilmantar da jama’a.

A cewar malamin, “Musulunci ya riga ya haramta yin karya, kamar yadda Allah ya gargade mu a cikin Alkur’ani: ‘Kada ku bi abin da ba ku da ilimi a kansa. Hakika kunne, ido da zuciya, duk abubuwan tambaya ne a gare ku’.

“Saboda haka, kirkira da yada labaran karya ba su da bambanci da yin karya, wanda laifi ne,” in ji shi.

Ya kara da cewa malamai na da muhimmiyar rawa da za su taka wajen ilmantar da jama’a game da hadarin yada labaran karya, musamman a intanet da kafafen sada zumunta.

Tun da farko da yake jawabin maraba, Editan Alkalanci kuma wanda ya shirya taron, Alhassan Bala, ya jaddada muhimmancin shirya bitar ga malaman.

“Muna rayuwa a wani zamani da bayanai ke yaduwa cikin sauri fiye da da. Abin takaici, yawancin abin da ake yadawa yana da rudani, raba kan jama’a, kuma yana da illa,” in ji shi.

Bala ya bayyana cewa an tsara taron musamman don malamai saboda tasirinsu a cikin al’umma.

“Wa’azinku da koyarwarku suna da tasiri wajen gina ra’ayin jama’a. Tare da wannan amana, akwai nauyin tabbatar da cewa abin da kuke yadawa gaskiya ne, an tabbatar da shi, kuma yana da amfani,” kamar yadda ya fada wa mahalarta bitar.

Ya ce tun bayan kafuwarta a watan Oktoban bara, kungiyar Alkalanci ta mayar da hankali kan yaki da labaran karya da ake yadawa da Hausa, tare da niyyar fadada ayyukanta a fadin Najeriya.

Ya jaddada cewa har manyan shugabanni da ake girmamawa na iya yada karya ba tare da sun sani ba, lamarin da ke nuna muhimmancin tunani mai zurfi da tabbatar da gaskiya.

A yayin bitar an koya wa mahalarta amfani da fasahohin zamani wajen tantance gaskiyar rubuce-rubuce, hotuna da bidiyo, da nufin yaki da yada labaran karya.

Taron ya kuma yi kira ga ci gaba da hadin gwiwa tsakanin shugabannin addini da masu wayar da kan jama’a don kare gaskiya da hadin kai a cikin al’umma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sheik Ibrahim Khalil Yada labaran karya yada labaran karya da labaran karya

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Kama Masu Laifi

Rundunar sojojin ta ce waɗannan hare-hare sun nuna ƙudirin gwamnati wajen yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar nan.

Ta kuma tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa za ta ci gaba da ƙoƙari domin kare al’umma daga ‘yan ta’adda da sauran masu laifi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tarihi da rayuwar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh (1943-2025)
  • Imam Khamenei: Hadin kan al’ummar Iran a yakin kwanaki 12 ya sanya makiya kunya
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda, Sun Kama Masu Laifi
  • An kama ɗan sandan bogi a Kano
  • Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya
  • Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Sarkin Ruman Katsina ya rasu