Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya
Published: 19th, November 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da tafiyarsa zuwa Birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Luanda na Angola, sakamakon sace ɗalibai a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a wata coci da ke yankin Eruku a Jihar Kwara.
Tinubu, shirya barin Abuja a ranar Laraba domin halartar taron G20 karo na 20 da kuma Taron AU-EU karo na bakwai.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.
“Shugaban ƙasa ya umarci sojoji da ’yan sanda da su aike ƙarin jami’ai zuwa waɗannan yankuna domin a tabbatar an bi diddigin ’yan bindigar da suka kai wa masu ibada hari.”
Shugaban ya ɗage tafiyar domin samun ƙarin bayanan tsaro da ɗaukar matakan gaggawa.
Bayan neman agaji da Gwamnan Jihar Kwara ya yi, Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su tura ƙarin dakaru da ’yan sanda zuwa Eruku da dukkanin yankin Ƙaramar Hukumar Ekiti domin inganta tsaro.
Idan ba a manta ba ’yan bindiga sun kai wa masu ibada hari a Cocin Christ Apostolic Church a ranar Litinin.
Shugaba Tinubu na jiran cikakken rahoto daga Mataimakinsa Kashim Shettima, wanda ya kai wa al’ummar Jihar Kebbi ziyarar jaje kan sace ɗalibai mata da wasu mahara suka yi.
Hakazalika, yana jiran rahotan ’yan sanda da Hukumar DSS game da harin da aka kai a Jihar Kwara.
Onanuga, ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa ya damu matuƙa kan sace ɗaliban da aka yi a Jihar Kebbi.
“Shugaba Tinubu ya bayyana a fili cewa dole ne a yi duk mai yiwuwa domin ceto ɗalibai 24 da aka sace tare da dawo da su gida lafiya,” in ji shi.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce kiyaye rayukan ’yan Najeriya shi ne babban abin da shugaban ƙasa ya fi mayar da hankali a kai.
A cewar fadar wannan ne dalilin da ya sa ya ɗage tafiyarsa don mayar da hankali kan inganta tsaro a yankunan da abin ya shafa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hari Kwara Najeriya Sace Ɗalibai Taron G20
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi
Ƴan bindiga sun kai hari a makarantar Government Girls Comprehensive Senior Secondary School (GGCSS), Maga, da ke ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi, inda suka kashe Mataimakin Shugaban makarantar, Hassan Yakubu Makuku, tare da sace wasu ɗalibai mata da ba a san adadinsu ba. Al’ummar yankin sun ce harin ya sake tayar da hankula a garin, wanda ke fama da yawan hare-hare a kwanakin nan.
Wani mazaunin Maga, Aliyu Yakubu, ya ce maharan sun shigo makarantar ne kimanin ƙarfe 5 na safiyar Litinin, ba tare da wata ƙwaƙƙwarar musayar wuta daga jami’an tsaro ba. Ya bayyana cewa harin ya jefa mazauna yankin cikin firgici da tashin hankali, abin da ya sa jama’a ke cikin tsananin damuwa da alhini.
’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A KebbiYakubu ya ce sun harbe Shugaban Makarantar ne a lokacin da yake ƙoƙarin kare ɗalibansa daga faɗawa hannun ƴan bindigar. Ya bayyana rasuwar tasa a matsayin babban rashi ga makarantar da kuma al’ummar yankin gaba ɗaya.
ADVERTISEMENTDaily Trust ta rawaito cewa, a halin da ake ciki, babu wata sanarwa daga Rundunar ƴansanda Jihar Kebbi game da harin. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, bai amsa kiran waya da dama da aka yi masa ba yayin rubuta wannan rahoto.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA