An ƙone al’aurar ’yar shekara 5 saboda fitsarin kwance a Bauchi
Published: 23rd, September 2025 GMT
Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance.
Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa.
Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana.
“Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata katifa ta daban domin ta riƙa kwanciya a kai, amma duk da haka matar tasa ba ta daina azabtar da yarinyar ba,” in ji Kabiru.
Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya bayyana ne lokacin da yarinyar ta roƙi kawunta ya saya mata katifa, inda ta shaida masa cewa mamanta ta ƙona al’aurarta saboda yawan fitsarin kwance, dalili ke nan da ya yi wa ’yan sanda ƙorafi.
Kazalika, ana zargin cewa duk lokacin da matar ta samu sabani da mijinta, sai ta huce fushi a kan yarinyar.
Da yake jawabi, mahaifin yarinyar, Mohammed Umar, wanda ke aiki da wani gidan talabijin, ya tabbatar da cewa matarsa ta kan yi ƙorafi kan yawan fitsarin kwancen yarinyar, abin da ya sa ya saya mata katifa ta daban.
Umar ya ce: “A farko, da na ga ƙuna a jikinta, matata ta shaida min wai shayi mai zafi ne ya zubo a jikinta. A lokacin na gaskata hakan, har sai da na lura da ciwon yana ƙaruwa.”
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa rahoto ya iso ofishin su da misalin ƙarfe 3:00 na ranar 13 ga Satumba, 2025.
Wakil ya ce yarinyar ta sami ƙonuwa a ƙasan cikinta, cinyoyinta, da kuma al’aurarta.
Ya ƙara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Sani Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a gaggauta kama matar tare da miƙa ta zuwa sashen manyan laifuka domin gudanar da cikakken bincike.
Ya bayyana cewa da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da ita a gaban kotu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Fitsarin Kwance Jihar Bauchi yarinya
এছাড়াও পড়ুন:
An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai
Al’ummar Ƙauyen Sarai da ke Ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano sun shiga ruɗani a ranar Alhamis bayan da aka gano gawar wata mata mai shekara 96 a cikin masai.
Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya bayyanawa manema labarai a ranar Juma’a.
Ma’aikacin jinya ya kashe marasa lafiya 10 saboda aiki ya masa yawa Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800Abdullahi ya ce, sashin bayar da agajin gaggawa na hukumar ya samu kiran gaggawa daga wani mai suna Usman Adamu ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa wata tsohuwa ta faɗa cikin masai a ƙauyen Sarai.
“Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Daraktan, Sani Anas ta samu kiran gaggawa daga Usman Adamu da misalin ƙarfe 9:27 na safiyar ranar Alhamis, 6 ga watan Nuwamba, 2025, inda ya bayar da rahoton ibtila’in da wata mata ta faɗa cikin ramin masai a ƙauyen Sarai da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu,” a cikin sanarwar.
“Jami’anmu na sashen agajin gaggawa daga hedikwatar hukumar ta isa wurin, inda ta gano wata mata mai suna Habiba Ado mai shekara 96, wanda ’yan uwanta suka ce tana fama da taɓin hankali,” in ji shi.
Abdullahi ya bayyana cewa, ‘yan uwanta sun shafe kwanaki huɗu suna nemanta kafin a gano gawarta a cikin masai ranar Alhamis.
“Sun kuma yi kira ga mai gidan da ya rufe ramin masan don hana afkuwar irin haka nan gaba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa jami’an ceto sun gano matar daga cikin ramin, amma an tabbatar da mutuwar ta.
Tuni dai aka miƙa gawarta ga Hakimin Unguwa, Alhaji Musa Muhammad domin yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.