Cibiyar fasaha ta kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin ’yan kasuwa mata a Jihohi 3
Published: 19th, November 2025 GMT
Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya.
Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano, tare da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU).
Da take jawabi a wajen kaddamarwar a Kano ranar Talata, shugabar cibiyar, Maryam Lawan Gwadabe, ta ce an kirkiro shirin ne domin samar wa mata amintaccen muhallin da za su yi amfani da shi wajen bunƙasa kasuwancinsu.
Ta ce shirin zai gudana a jihohin Kano, Katsina da Sakkwato domin ƙarfafa tattalin arzikin mata da kuma tabbatar da sun samu dogaro da kai.
“Mun sanya wa shirin suna Women Venture Studio domin tabbatar da cewa mata za su ji daɗin kasancewa a cikin muhalli mai tsaro. Masu ba da shawara a nan su ne ’yan kasuwa da matan da suka yi nasara, waɗanda za su saurara, su jagoranta, kuma su tallafa wa mahalarta shirin,” in ji ta.
Maryam ta ƙara da cewa cibiyar tana bayar da wuraren yin aiki na zahiri da na intanet, domin tabbatar da cewa ana damawa da mat aba tare da an ware su ba.
Shugabar cibiyar ta kuma ce matakin farko na shirin zai haɗa da horar da mata 150, wato mata 50 daga kowacce jiha.
Ita ma da take jawabi, Shugabar ANWE, Hafsat Sahabi Dange, ta ce shirin ya fi mayar da hankali kan mata a fannin kirkira, musamman a harkar dinka kaya, sana’o’in hannu da fasaha.
“Manufarmu ita ce mu sauya waɗannan kasuwancin zuwa tsarin zamani domin mata su iya yin gogayya, ba kawai a Najeriya ba, har ma a duniya. Wannan shiri zai shafi ’ya’ya mata da kuma mata ta hanyar amfani da kirkirarsu da kuma ƙarfafa musu tsarin kasuwanci a Arewacin Najeriya,” in ji ta.
A nata bangaren, wakiliyar Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS, Inga Stefanovic, ta ce EU ta ware sama da Yuro miliyan 700 a matsayin tallafi domin tallafa wa ayyuka daban-daban a fadin Najeriya.
Ta jaddada cewa haɗin gwiwar EU da Najeriya ya shafi fannoni da dama ciki har da fasahar zamani, bunkasa tattalin arziki, dimokuraɗiyya, zaman lafiya da tsaro, lafiya, ilimi, samar da makamashi da kuma noma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Maryam Lawan Gwadabe
এছাড়াও পড়ুন:
Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas.
Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki.
Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a GombeA cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa.
Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar ce bayan sun hangi yadda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya, lamarin da ya sa suka gaggauta kiran ma’aikatar kashe gobara kuma suka kawo dauki domin tarar hanzarin lamarin na hana gobarar bazuwa zuwa sauran gidaje.
Haka kuma, wani mazaunin yankin ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa gobarar ta tashi ne a harabar wata kwaleji ta Captain Elechi Amadi da ke Rumuola, yana mai bayyyan cewa lamarin ya faru ne a bayan makarantar, inda ake da dogayen gine-gine da ke ɗauke da iyalai sama da 27.
Ya bayyana takaicin cewa dubban mutane sun rasa matsugunni a sanadiyar gobarar wadda ta ƙone dukiyoyin da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa yaran biyu da suka mutu shekarunsu na haihuwa ba su gaza biyar da tara ba.
Ta ce an fara bincike domin gano musabbabin gobarar, kana an gayyaci mahaifiyar yaran domin amsa tambayoyi.