kungiyar Hadin Guiwa Ta SCO Ta yi Watsi Da Adawar Da Kasashen Turai Ke Nuna wa Kasar Iran
Published: 19th, November 2025 GMT
pirme ministocin kungiyar hadin guiwa ta kasashen shangai SCO sun kawo karshen taron kungiyar karo na 24 a birnin mosko inda suka fitar da bayanin hadin guiwa na yi watsi da duk wani mataki na kasashen turai dake nuna adawa da kasar iran, musamman kan abin da ya shafi shirin ta na nukiliya na zaman lafiya.
Bayanin karshe na taron da mamabobin kungiyar suka fitar ya yi tir da adawa da kasashen yamma ke nunawa kasar iran da ya shafi takunkumin karya tattalin arziki da ya sabama dokokin kasa da kasa , shuwagabannin sun yi gargadin cewa daukar irin wannan matakai zai cutar da majalisar dinkin duniya wajen cimma kudurin ci gaban alumma.
Kasashen Amurka da sauran kawayenta sun maka takunkumai kan kasar iran kan shirinta na naukiliya na zaman lafiya da zargin cewa wai kasar tana neman kera makamin nukiliya, lamarin da iran ta karyata tun tuni.
Iran da Amurka sun gana ba kai tsaye ba har sau 5 a farkon wannan shekara domin sabunta yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta 2015 wanda ya hada da kudurin majalisar dinkin duniya dake gab da karewa amma haka ba ta cimma ruwa ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisa wakilai A Najeriya Ta Bukaci Gwamnati Ta Sake Dabarun Yaki Da Ta’addanci November 19, 2025 Kimanin Falasdinawa 2 Ne Suka yi Shahada Sakamakon Harin Isra’ila A Ainul Hilwa November 19, 2025 Iran : Dole ne kudirin Amurka ya kare hakkin Falasdinawa da samuwar kasar Falasdinu November 19, 2025 Saudiyya za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya November 19, 2025 Iraki : Jam’iyyar al-Soudani ta samu rinjaye a Majalisar dokoki November 19, 2025 Shugaban gwamnatin Togo zai gana da Shugaba Putin na Rasha November 19, 2025 Harin Isra’ila ya kashe mutum 15 a sansanin ‘yan gugun hijira na Falasdinawa a Lebanon November 19, 2025 Iran: An Bayyana Taron Gundumomin Dake Gabar Ruwan ” Caspian” Da Cewa Yana Bunaksa Alakar Kasashen Yankin November 18, 2025 Nijar: An Dakatar Da Ayyukan Kungiyoyin Agaji Da Dama November 18, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin “Sahayoniya A Garin Bint-Jubail November 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing
A yau ne aka bude taron tattaunawa game da wayewar kai takanin Sin da kasashen Larabawa karo na 11, wanda sashen cudanya da kasashen waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin da sakatariyar kawancen kasashen Larabawa suka dauki nauyin shiryawa a Beijing.
A gun taron, shugabanni na jam’iyyu da kungiyoyin siyasa, ‘yan majalisa, jami’an gwamnati, da wakilan masana da kafofin watsa labarai daga Sin da kasashen Larabawa guda 22 sun hallara don inganta ilmantarwa da fahimtar juna kan wayewar kai da kuma zurfafa hadin gwiwar abokantaka.
A wannan taron kuma, Sin da kasashen Larabawa za su mayar da hankali kan batutuwa kamar “Musayar darussan mulkin kasa da binciken hanyoyin zamanantarwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa”, da “Shawarwarin wayewar kan duniya da hadin gwiwar al’adu na Sin da kasashen Larabawa”, da kuma “Shawarar ziri daya da hanya daya da hadin kan jama’a tsakanin Sin da kasashen Larabawa”, kana za su shiga tattaunawa da musayar ra’ayoyi masu zurfi.(Safiyah Ma)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA