Aminiya:
2025-11-20@10:31:14 GMT

Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia

Published: 20th, November 2025 GMT

Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Najeriya baki ɗaya.

Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da aka tilasta musu barin gidajensu.

Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki

Gwamna Alia, wanda tsohon Faston Katolika ne, ya ce: “A Binuwai, babu wani kisan kare addini, ƙabilanci, launin fata, ƙasa ko jiha.

“Muna da wasu matsalolin tsaro, amma ba kisan addini ba ne. Ya kamata mutane su duba ma’anar kisan ƙare addini ta Majalisar Ɗinkin Duniya.”

Ya kuma ce babu wani jihadi da ake yi a kowane ɓangare na Najeriya, ko da yake ƙungiyoyin ’yan ta’adda kamar Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas, suna iƙirarin  jihadi.

“Babu wani jihadi a Najeriya,” in ji Alia.

“A matsayina na Fasto kuma gwamna, ni ne zan fara yin magana idan hakan na faruwa a jihata ko a wani ɓangare na ƙasar nan.”

Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke zargin ana yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya.

Amurka ta taɓa sanya Najeriya a cikin jerin  “Ƙasashen Masu Matsala ta Musamman” saboda cin zarafin addini, amma gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargi.

Kiristoci da Musulmai duka sun sha wahala sakamakon rashin tsaro, fashi da makami, da kuma garkuwa da mutane.

Gwamna Alia, ya ce ya gana da ofishin jakadancin Amurka don bayyana yadda halin tsaro yake a Binuwai.

“Na bayyana cewa babu kisan ƙare addini a Najeriya, musamman a Binuwai. Ma’anar Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta dace da yanayin nan ba,” in ji shi.

Jihar Binuwai ta jima tana fuskantar matsalolin da suka shafi kisan jama’a da sace mutane.

Bayanai sun nuna cewa sama da mutum 800 sun mutu, yayin da aka sace kusan mutum 400 cikin shekaru biyu da suka gabata.

A watan Yuni, aƙalla mutum 100 ne suka mutu a hare-haren da ’yan ta’adda suka kai a Ƙaramar Hukumar Guma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Binuwai gwamna matsalar tsaro Najeriya zargi kisan ƙare

এছাড়াও পড়ুন:

Kasashen Iran Da Malesiya Sun Rattaba Hannu Kan Jarjejeniyar Fadada Dangantakar Addini

Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Iran da malesiya sun cimma yaejejeniyar kara fadada dangantar yin aiki tare a bangaren Addinin da Ala’adu musamman a bangaren kimiyar alkur’ani bayan tarurruka da manyan jami’an gwamnati suka yi a birnin kuala Lumpur babban birnin kasar,

Wannan yarjejeniyar za ta kara karfafa hadin guiwa tsakanin manyan kasashen musulmi  adaidai lokacin da kasashen musulmi suke fuskantar matsalolin aladu da tasirin kasashen yamma a tsarin zaman takewarsu da tashe tashen hankula na siyasa musamman ma kan yankin falasdinu.

Kasashen biyu suna da matsaya daya na dogon lokaci a bangaren abincin Halal, aladun musulunci da kuma ilimin Addinin, don haka wannan tattaunawar da aka yi an sake sabunta alakar ne bisa ababen girmama wa na musulunci da kare iyali da kuma bunkasa karatun alkur’ani tare da yin aiki tare.

Zulkaranen bin Hassan mataimakin ministan harkokin Addini na kasar malesiya ya jinjinawa matsayin iran akan gwamnatin sahyuniya da kuma goyon bayan da take bawa alummar falasdinu da ake zalunta ya bayyanata a matsayin cibiyar hadin kan musulmi .

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 27 a wani sabon harin bam November 20, 2025 Iran : daftarin kudurin da Canada ta gabatar, siyasa ce da kin jininmu November 20, 2025 AU ta yi Allah-wadai da tsoma bakin kasashen waje a harkokin tsaron Afirka November 20, 2025 Amurka ta Shawarci Ukraine ta amince da yankunan da Rasha ta mamaye mata November 20, 2025 Sudan ta yaba da kokarin Amurka da Saudiyya na kawo karshen rikicin kasar November 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: A Yanzu Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka November 19, 2025 Sojojin Yemen Suna Da Makami Mai Linzami Da Babu Mai Makamancinsa Sai Iran November 19, 2025 Daraktar Hukumar IAEA Ya Ce: Suna Tuntubar Juna Da Iran Kuma Masu Bincikensu Sun Kamo Kasar November 19, 2025 Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta A Gaza Kusan Sau 400 November 19, 2025 Kotu A Gabon Ta Yanke Hukuncin Dauri A Kurkuku Kan Jami’an Tsohuwar Gwamnatin Kasar November 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasashen Iran Da Malesiya Sun Rattaba Hannu Kan Jarjejeniyar Fadada Dangantakar Addini
  • Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: A Yanzu Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka
  • Sojojin Yemen Suna Da Makami Mai Linzami Da Babu Mai Makamancinsa Sai Iran
  • United za ta yi wasanni 6 a jere babu Benjamin Sesko
  • Sojojin Najeriya Sun Karyata Cewa “ISWAP” Ta Kashe Wani Babban Jami’i Mai Mukamin  Birgediya
  • Najeriya ta Fara tattaunawa da Amurka kan zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi
  • Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty