’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu, sun sace mutum 8 a Kwara
Published: 24th, September 2025 GMT
’Yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka na Patigi a Jihar Kwara, inda suka kashe wata mata mai juna biyu tare da wasu mutane.
Haka kuma sun yi garkuwa da mutane takwas tare da jikkata da dama.
Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 Tarihi da rayuwar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh (1943-2025)Shaidu sun ce maharan sun shiga ƙauyukan ne a babura, inda suka dinga harbi ba ƙaƙƙautawa wanda ya sa mazauna ƙauyukan suka gudu.
Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Motokun, Egboro da Fanagun.
Wani mai suna James Ibrahim, ya ce: “Mun farka da safe muka ga mutane suna gudu daga Motokun bayan harin. An harbi wata mace wadda daga bisani ta rasu a asibitin Patigi.
“Sun kuma sace mutum takwas tare da yin awon gaba da babura da dama. Muna roƙon gwamnati ta taimake mu.”
Wani shugaban al’umma, Malam Mohammed, ya ƙara da cewa: “’Yan bindigar sun fara kai hari Motokun, daga nan suka nufi Egboro. Yawancin mazauna ƙauyukan sun tsere.
“Sun kashe wani malami da ya saba zuwa yin wa’azi, sannan suka sace mutanen da suke ganin za su iya karbar fansa a hannunsu.”
Harin ya tilasta wa magidanta da dama barin gidajensu, inda suka nemi mafaka a garuruwan da ke kusa da su.
Mazauna ƙauyukan sun ce suna rayuwa cikin tsoro saboda hare-haren da ke ƙara yawaita kullum.
Gwamnatin Jihar Kwara, ta yi alƙawarin ƙara tsaurara tsaro tare da buƙatar al’umma su fallasa masu bai wa ’yan bindiga bayanai.
Rundunar sa-kai da sojoji kuma sun ƙara tsaurara tsaro, duk da cewa jama’a sun koka cewa sau da yawa maharan na kai farmaki kafin a kai musu agaji.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hare hare hari Kwara
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wasu mutum huɗu a yankin Kamba da ke jihar, bisa zargin su da shigar da babura uku da suka saya daga Jamhuriyar Benin domin kai wa kungiyar ta’addanci ta Lakurawa.
Haka kuma an kama wani Mubarak Ladan bayan ya yi tayin cin hancin naira dubu dari shida (₦600,000) ga DPO na Kamba, SP Bello Mohammad Lawal, domin a saki waɗanda aka kama.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce baburan da ake kira “Boko Haram” guda uku an saye su ne kan kudi naira miliyan 5 da dubu 400, kuma an tanadar da su ne domin kai wa kungiyar Lakurawa ta hannun wani Alhaji da ke a Kangiwa.
Sanarwar ta ƙara da cewa an cafke mutanen ne bayan samun sahihan bayanai, inda jami’an ’yan sanda tare da ’yan sa-kai ƙarƙashin jagorancin DPO na Kamba suka kai samame
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kebbi, Bello M. Sani, ya umurci Mataimakin Kwamishina na Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID), Birnin Kebbi, da ya bi sahun sauran waɗanda suka tsere a lamarin