Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa
Published: 24th, September 2025 GMT
Darajar Naira ta ɗan ƙaru a kasuwanni, bayan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da rage kuɗin ruwa daga kashi 27.5 zuwa kashi 27.
Wannan mataki, a cewar masana tattalin arziƙi, na nufin gwamnati na ƙoƙarin rage matsin tattalin arziƙi da farashin kayayyaki ga ’yan ƙasa.
’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu, sun sace mutum 8 a Kwara Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240A ranar Talata, an sayar da dala ɗaya kan Naira 1,487.
Hakazalika, farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya tashi zuwa dala 67.82 a kan kowace ganga ɗaya, abin da ya ƙaru da kashi 0.3 idan aka kwatanta da farashin baya.
Wannan na iya taimaka wa Najeriya, wadda mafi yawan kuɗaɗenta na samuwa ne daga sayar da mai.
Masana sun ce wannan sauyi ba shi da yawa, amma yana nuna cewa ana iya ganin sauƙin matsin tattalin arziƙi idan aka ci gaba da ɗaukar irin waɗannan matakan.
Sai dai har yanzu farashin kayayyaki a kasuwannin cikin gida na ci gaba da hauhawa, lamarin da ke haifar da ƙalubale ga rayuwar talakawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Daraja Hauhawar Farashi kuɗin ruwa Naira
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sakkwato Ta Dakatar da Karɓar Kuɗin Makaranta
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp