Aminiya:
2025-11-22@17:24:26 GMT

’Yan sanda sun daƙile harin ’yan bindiga, sun ceto mutum 25 a Zamfara

Published: 22nd, November 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara, ta daƙile wani hari da ’yan bindiga suka kai wa al’ummar Kuraje da ke gefen birnin Gusau.

Wasu gungun ’yan bindiga, ɗauke da makamai ne, suka kutsa cikin ƙauyen suna harbi, lamarin da ya jefa mazauna Kuraje da maƙotan ƙauyukan cikin tashin hankali.

Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja

A yayin harin, sun yi awon gaba da mata 10 da yara 15.

Kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya ce ’yan sanda sun ɗauki mataki bayan samun kiran gaggawa.

Ya ce tawagar haɗin gwiwa daga sashen Damba, Sashen Ayyuka da kuma Rundunar Tsaron Al’umma (CPG) sun isa ƙauyen cikin gaggawa.

Sun bi sahun ’yan bindigar, sannan suka yi artabu da su.

’Yan sanda sun ceto dukkanin mutum 25 ba tare da kowa ya ji rauni ba.

An kai matan da yaran zuwa Sabon Gari Damba domin kula da su, kafin su da iyalansu.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya yaba wa jarumtar jami’an da suka yi aikin, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda Garkuwa hari yara Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja

’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba.

Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an yi awon gaba da ɗalibai da dama yayin harin da aka kai makarantar.

’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi

Wata majiya daga ɗaya daga cikin coci-cocin Katolika a jihar ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa har yanzu makarantar na kan tattara bayananta a kan harin.

“Eh, gaskiya ne, amma ba ni da ikon bayar da cikakkun bayani. Coci za ta fitar da sanarwa a hukumance daga baya a yau,” in ji shi.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai bayar da cikakkun bayanai daga baya.

Sai dai shugaban sashen bayar da agaji na ƙaramar hukumar Agwara, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da harin ta wayar salula.

Ya ce ’yan ta’addan sun kai hari kan makarantar ne tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na dare, yana mai cewa ba a kai ga tabbatar da adadin ɗalibai da malaman da aka sace ba tukuna, domin har yanzu hukumomi na ci gaba da tantancewa.

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan irin wannan hari a Maga, Jihar Kebbi, inda aka yi garkuwa da ɗalibai mata 25, abin da ya ƙara tayar da hankula kan tabarbarewar tsaro a makarantu a yankin.

Ko a ranar Alhamis, sama da makarantu 50 aka rufe a Jihar Kwara sakamakon barazanar ta’addancin ’yan bindiga.

Shugaba Bola Tinubu ya soke tafiyarsa zuwa kasashen Afirka ta Kudu da Angola domin jagorantar dakile matsalolin tsaron.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan Sanda a Zamfara Sun Ceto Mutane 25 Bayan Dakile Harin ’Yan Bindiga a Damba
  • Rundunar Sojan Iran Tana Cikin Shirin Mayar Da Martani Akan Kowace Barazana
  • ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja
  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
  • Rundunar Hadin Gwiwa na Faɗaɗa Bincike Don Ceto Daliban da Aka Sace a Neja
  • ’Yan Bindiga Sun Nemi Miliyan 100 Kudin Fansa Kan Kowane Mutum Ɗaya da Suka Sace a Kwara
  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro
  • Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas
  • Labanon Ta Bukaci Gudanar Da Taron Kwamitin Tsaro Na MDD Cikin Gaggawa