Aminiya:
2025-11-20@19:54:00 GMT

IAEA ta buƙaci Iran ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka

Published: 20th, November 2025 GMT

Kwamitin hukumar hana yaɗuwar makamin nukiliya IAEA a Majalisar Dinkin Duniya, ya buƙaci ƙasar Iran da ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka.

Wannan dai na zuwa ne bayan kwamitin ya amince da wani ƙuduri da zai tilasta wa Iran bayyana musu yawan makamashin nukiliyarta.

An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai Kotu ta sami Nnamdi Kanu da laifukan ta’addanci

A cewar sabon ƙudurin da ƙasashe 19 suka yi na’am da shi, dole Tehran ta bayar da kai bori ya hau ta hanyar sallama duk wasu bayanai gamsassu, da kuma ba wa ƙwararrun jami’an IAEA damar shiga wuraren da take gudanar da shirinta na bunƙasa makamashi.

Ƙudurin ya kuma ce dole ne Iran ta bayar da damar ziyartar tashoshinta na nukilya, ciki har da waɗanda aka kai wa hari lokacin yaƙi tsakaninta da Isra’ila a watan Yuni.

Ƙasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da Amurka ne suka bijoro da ƙudurin wanda Rasha da China da kuma Jamhuriyyar Nijar suka hau kujerar naƙi wajen kaɗa ƙuri’a.

China da Rasha dai sun nuna fargaba kan abubuwan da ka iya biyowa baya, idan aka samar da sabon ƙudurin, wanda suka ce ka iya sa Iran ta bijire wa batun, duba da takun saƙar da aka fuskanta a baya-bayan nan a tsakanin jami’an hukumar IAEA da fadar mulki ta Tehran.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Faransa Iran Rasha Tehran

এছাড়াও পড়ুন:

Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya

Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa.

Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya.

‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas

Ezea, wanda aka zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar LP, shi ne kaɗai Sanatan da ya ci zabe daga Enugu karkashin jam’iyyar a Majalisar Dattawa ta 10.

Rasuwarsa ta sa ya zama sanata na biyu daga yankin Kudu maso Gabas da ya rasu cikin shekaru biyu, bayan mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra, wanda shi ma ya rasu a Landan a watan Yuli 2024 yana da shekara 52.

Da labarin rasuwarsa ya isa Majalisar, abokan aikinsa sun yi ta’aziyya, suna bayyana shi a matsayin ɗan majalisa mai tawali’u, mai jajircewa, da kuma sadaukarwa, wanda rashin sa ya bar gibi a zauren majalisar.

Sanata Orji Uzor Kalu, wanda ke wakiltar Abia ta Arewa, ya ce ya yi matukar kaduwa da samun labarin, inda ya bayyana marigayin a matsayin ɗan’uwana kuma abokinsa.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Kogi ta Tsakiya, ita ma ta yi jimami, tana bayyana Ezea a matsayin aboki mai hikima da natsuwa, wanda shawarwarinsa da addu’oinsa suka taimaka mata a lokutan da ta shiga ƙalubale.

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta yi magana a hukumance kan rasuwarsa a zaman majalisa, tare da yin shiru na minti ɗaya don girmamawa, kamar yadda al’ada ta tanada.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sai da Kwankwaso APC za ta iya samun nasara a 2027 — NNPP
  •  Iran Tana Cikin kasashe 10 Na Farko Da Su Ka Fi Yawan Wuraren Tarihi
  • Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano
  • Daraktar Hukumar IAEA Ya Ce: Suna Tuntubar Juna Da Iran Kuma Masu Bincikensu Sun Kamo Kasar
  • Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa
  • An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari
  • Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya
  • Iran: An Bayyana Taron Gundumomin Dake Gabar Ruwan ” Caspian” Da Cewa Yana Bunaksa Alakar Kasashen Yankin
  • CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana