Aminiya:
2025-11-19@17:04:35 GMT

An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari

Published: 19th, November 2025 GMT

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa.

Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya

DSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012.

Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan sanda na Unguwa Uku, da wasu wurare.

Mutane da dama sun jikkata a yayin kai waɗannan hare-hare.

An kama Ismaila ne a ranar 31 ga watan Agustan 2017, a ƙauyen Tsamiyya Babba da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa, a Jihar Kano.

Daga nan aka gurfanar da shi a gaban kotu bisa dokar hana aikata ta’addanci ta 2013.

Shari’ar ta ɗauki lokaci saboda ɗaukaka ƙara da kuma tabbatar da bayanan da ya bayar da farko ba tursasa shi aka yi ba.

A ƙarshe, lauyoyin gwamnati sun kira shaidu biyar, ciki har da jami’an DSS da mutanen da harin ya shafa.

Da farko Ismaila, ya ƙi amincewa da laifin da ake tuhumarsa amma bayan gabatar da shaida na biyar, ya sauya maganarsa ya amsa laifin.

Lauyansa daga Hukumar LAC, P. B. Onijah, ya roƙi kotu ta yi masa sassauci, inda bayyana cewa Ismaila ya nuna nadama kuma bai son ɓata wa kotu lokaci.

A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Nwite ya yanke masa shekar 15 kan tuhumar farko da kuma shekaru 20 kan sauran kowace tuhuma uku.

Dukkanin hukuncin za su tafi a lokaci guda, kuma za su fara aiki tun daga ranar da aka kama shi a shekarar 2017.

Alƙalin ya umarci Hukumar Gyaran Hali ta tsare shi a gidan yari da Babban Kwamandan Hukumar ya zaɓa.

Bayan ya kammala zaman gidan yari, dole a yi masa horon gyaran hali da kawar da ra’ayin ƙiyayya kafin a sake mayar da shi cikin al’umma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hari Harin Kano ISWAP

এছাড়াও পড়ুন:

Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa

An shiga jimami a garin Zugai da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare yin sanadin rasuwar mutum da jikkata wasu.

Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu.

An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku ne kwana uku bayan shugaban Ƙaramar Hukumar, ya raba ruwa ga masu sana’r sayar da ruwa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu mutane.

Tankin ruwa, wanda ke amfani da hasken rana wajen samar da ruwa, ya fashe yayin da mutane da yawa suka taru a ƙasa domin ɗibar ruwa.

Shaidu sun ce tankin ya rushe ba zato ba tsammani, inda mutum uku suka mutu nan take, waɗanda suka jikkata aka garzaya da su asibiti.

Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Roni, Dokta Abba Ya’u Roni, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya tabbatar da mutuwar mutum huɗu.

Dokta Abba, ya ce fashewar tankin ta faru ne sakamakon iska mai ƙarfi wadda ta turo tankin ya faɗo kan mutane.

Ya ƙara da cewa: “Na umarci mataimakina da jami’an majalisa su kai ziyara ƙauyen don tabbatar da cewa duk waɗanda suka ji rauni an kula da su.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Daraktar Hukumar IAEA Ya Ce: Suna Tuntubar Juna Da Iran Kuma Masu Bincikensu Sun Kamo Kasar
  • Kotu A Gabon Ta Yanke Hukuncin Dauri A Kurkuku Kan Jami’an Tsohuwar Gwamnatin Kasar
  • Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa
  • Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe
  • Sojojin Najeriya Sun Karyata Cewa “ISWAP” Ta Kashe Wani Babban Jami’i Mai Mukamin  Birgediya
  • Masu shigar da kara na ICC sun bukaci hukuncin daurin rai da rai a kan kwamandan RSF
  • Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno
  • An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa
  • Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku