Aminiya:
2025-11-19@15:21:28 GMT

Gwamna Abba ya gabatar da kasafin 2026 na N1.36trn

Published: 19th, November 2025 GMT

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 tiriliyan a Majalisar Dokokin jihar.

Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.”

Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya

Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya.

Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka.

Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su tafi ne a ayyukan yau da kullum.

Gwamna Abba ya ce ya aiwatar da kashi 80 na alƙawuran da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Ya ce kasafin 2026 zai mayar da hankali ne wajen kammala ayyuka a birane, faɗaɗa gidaje da kuma tallafa wa ƙananan masana’antu.

Ya fara jawabinsa da jajanta wa iyalan hamshaƙin attajiri Alhaji Aminu Alhassan Dantata, Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi, da tsohon ɗan siyasa Alhaji Ahmadu Haruna Zago, waɗanda suka rasu a wannan shekara.

Hakazalika, ya yi jimamin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da ’yan wasan Kano 22 da suka rasu a hatsarin mota a watan Mayu.

Abba, ya ce an aiwatar da kashi 75 na kasafin 2025 daga Janairu zuwa Oktoban wannan shekara, wanda a cewarsa an samu ci gaba mai kyau.

Ɓangaren ilimi ya samu Naira biliyan 280.6 (kashi 31) a 2025.

Ayyukan da aka yi sun haɗa da gyaran azuzuwa, shirye-shiryen ilimi kyauta, biyan kuɗin NECO, bayar da tallafin karatu, kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gaya, ɗaukar malaman darasin lissafi guda 400, masu gadi 1,600 da gyaran manyan makarantun sakandare.

Ya ce wannan ya taimaka wa Kano wajen zama ta farko a sakamakon NECO na 2025 a Najeriya.

A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan 149.7 biliyan wajen gyara asibitoci a ƙananan hukumomi, inganta inshorar lafiya.

Sauran sun haɗa da ƙaddamar da shirin Abba-Care, gyaran cibiyoyi, da samar da kayan aikin lafiya da hanyoyin samar da wuta a manyan asibitoci.

Gwamnatinsa ta sayi buhun taki 199,000, ta raba wa al’umma shinkafa, ta amince da gina ƙananan madatsun ruwa 11, sannan ta ɗauki sababbin ma’aikatan aikin gona.

Ayyukan da aka yi sun haɗa da faɗaɗa tituna, siyan na’urar lantarki, saka fitilu a kan tituna, gyara masallatai, da samar da gidaje a sassa daban-daban na jihar.

Gwamnatin ta farfaɗo da cibiyoyin ɗinka kaya a ƙananan hukumomi 44, ta gyara manyan kasuwanni, ta tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa, sannan ta shirya bukukuwan al’adu kamar KANFEST.

Haka kuma ta aiwatar da dokar canjin yanayi, ta share magudanan ruwa, ta sayi kayan sarrafa shara, ta kuma shuka bishiyoyi sama da miliyan 5.5.

Gwamna Abba, ya ce Hukumar Kula da Tsaro ta Jihar Kano, ta horar da jami’ai 2,000, ta kuma samar da kayan sintiri 6,000.

Matasa sama da 5,384 sun amfana da shirin tallafin Naira miliyan 800; dubban mata sun samu dabbobi; ƙananan ’yan kasuwa sun samu tallafin Naira 50,000 kowannensu.

A kasafin 2026, an raba jadawalin yadda kowane ɓangare zai samu:

Ilimi: Naira biliyan 405.3 (kashi 30) Lafiya: Naira biliyan 212.2 (kashi 16) Gine-gine: Naira biliyan 346.2 biliyan (kashi 25)

Sauran sassa kamar noma, tsaro, kasuwanci, ruwa, muhalli da ci gaban matasa suma sun samu kuɗi mai yawa.

Gwamnan ya roƙi majalisar da ta hanzarta amincewa da kasafin, inda ya ce kasafin zai taimaka wajen samar wa al’ummar Kano ci gaba mai tarin yawa.

Ya gode wa ma’aikata, hukumomi, da al’ummar Kano kan goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa.

Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Ismail Jibril Falgore, ya tabbatar da cewa majalisar za ta hanzarta amincewa da kasafin da zarar ta kammala nazarinsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ayyuka Gwamna Abba Tsaro Naira biliyan

এছাড়াও পড়ুন:

An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano

An ɗaura auren Sanatan Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila, da Aisha Isah, wata jami’ar soji a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, a wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar sali-alin a Rano.

Ɗaurin auren wanda jama’a kaɗan ne suka halarta ya gudana ne da safiyar Litinin ɗin nan a fadar Sarkin Rano da ke Jihar Kano, lamarin da ya nuna cewa ba a yi wata sanarwa ta musamman ba kafin bikin.

Masu ibadar Umarah 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC

Mai taimaka wa sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Muttaqa Babire, ya tabbatar da auren a shafinsa na Facebook, inda ya wallafa hoton sanatan tare da amaryar cikin kayanta na jami’an soji.

Shi ma wani na hadiminsa, Ahmad Tijjani Kiru, ya wallafa a shafin Facebook cewa: “Alhamdulillah, yau 17-11-2025, an ɗaura auren Sanata S.A. Kawu Sumaila OFR, PhD a Rano. Allah Ya albarkaci rayuwar auren Ya kawo zuri’a ɗayyiba.”

Kawu Sumaila, wanda shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Albarkatun Mai, a bayan nan ne ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi
  • Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana
  • Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065%
  • Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS
  • An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano
  • NELFUND ya raba wa ɗalibai tallafin karatu na Naira Biliyan 116 
  • Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95
  • Tsaro: Na kan yi kuka duk lokacin da na ji an kashe wani — Akpabio