China ta ce Ya Kamata A Aiwatar Da Sakamakon Taron Kolin Tianjin Don Inganta Kungiyar SCO
Published: 21st, November 2025 GMT
Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha.
Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da kasar Sin ta gabatar, da karfafa kungiyar SCO a bangaren hadin kai da harkoki da kuma tasirinta.
Shekaru 24 da suka wuce bayan kafuwar kungiyar SCO, a karkashin jagorancin ruhin Shanghai, an samu habakar abotan kungiyar, da kara ingancinta, shi ya sa ma ta zama kungiyar yanki mafi girma a duniya, wadda ta kare muradun kasashe mambobin kungiyar, ta kuma inganta zaman lafiya da ci gaban duniya. A daidai sanda take ci gaba da samun bunkasa, kungiyar SCO tana kara taka rawar gani a harkokin duniya, inda ta fito da wata sabuwar hanya dake hada kowa a cikinta, wanda hakan ya ba da misali ga samun ingantaccen tsarin shugabancin duniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta yi Gargadi Game Da Sakamakon Da Zai Iya Faruwa A Yankin Bayan Shigar Isra’ila Kasar Siriya November 21, 2025 Araqchi: Yarjejeniyar Da Aka Cimma Tsakanin Iran Da Hukumar IAEA A Kasar Masar Ta Rushe November 21, 2025 Kakakin Rundunar ‘IRGC’: Yakin Kwanaki 12 Ya Nuna Karfin Kariyar Makaman Masu Linzamin Iran November 21, 2025 Iran Da Wasu Kasashe Bakwai Sun Mayar Da Martani Kan Hudurin IAEA Kan Kasar Iran November 21, 2025 Kungiyar Hamas Ta Yi Kiran Da A Sanya Isra’ila Cikin Jerin Masu Aikata Abin Kunya Saboda Kashe Yara November 21, 2025 Tarayyar Turai Ta Kakaba Takunkumi Kan Dan Uwan Kwamandan Rapid Support Forces Ta Sudan November 21, 2025 Iran Tana Cikin kasashe 10 Na Farko Da Su Ka Fi Yawan Wuraren Tarihi November 20, 2025 Nigeria:Kotu Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Zaman Kurkuku Na Har Abada November 20, 2025 Nigeria: An Rufe Makarantun Kwana A Jahar Kwara Saboda Matsalar Tsaro November 20, 2025 Hizbullah: Ba Za Mu Taba Ajiye Makamanmu Ba November 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kungiyar SCO
এছাড়াও পড়ুন:
Wardley ya zama zakaran damben boksin na duniya
Ana sa ran za a karrama shahararren ɗan damben boksin na Birtaniya, Fabio Wardley, da kambun zakarun ajin masu nauyi na WBO, bayan Oleksandr Usyk ya janye daga kare kambunsa a fafatawar da zai yi da Wardley.
Janyewar ta faru ne bayan Usyk, ɗan kasar Ukraine, ya shaida wa Hukumar Damben Boksin ta Duniya (WBO) cewa ba zai kare kambunsa a kan Wardley ba.
Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana Na sha alwashin kafa tarihi a Camp Nou — Lamine YamalWBO ta tabbatar da cewa Usyk “ya zaɓi ya ajiye kambun ne saboda wasu dalilai da suka gamsar da hukumar.”
A halin yanzu, Usyk na ci gaba da riƙe kambuna uku: WBA, WBC da IBF, bayan nasarar da ya samu kan Daniel Dubois a filin wasa na Wembley a watan Yuli, wanda ya tabbatar da shi a matsayin zakaran ajin masu nauyi sau biyu a jere.
Usyk ya fara riƙe bel huɗu a watan Mayu 2024 bayan da ya doke Tyson Fury. Sai dai daga baya ya ajiye kambun IBF makonni biyar bayan nasarar, tare da yanke shawarar ƙin sake dambatawa domin kare shi.
Wannan mataki na janyewa ya biyo bayan wata sanarwa da shugaban hukumar WBO, Gustavo Olivieri, ya fitar, inda ya kira Usyk “zakaran zakarun damben duniya.”
A sakamakon haka, Wardley na dab da karɓar kambun WBO a hukumance, lamarin da zai ƙara ɗaga matsayinsa a sahun manyan ‘yan damben duniya.