2025-11-22@11:04:19 GMT
إجمالي نتائج البحث: 52

«Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya»:

    Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin rufe makarantu arba’in da daya  saboda matsalolin tsaro. A wata takardar sanarwa da aka aikewa dukkan Shugabannin makarantu, wadda Daraktan Makarantu Manyan Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ya sanya wa hannu, gwamnati ta bayyana cewa sakamakon ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar nan da kuma buƙatar kare duk wani yunkurin hari, Ministan Ilimi ya amince a rufe makarantun nan dltaje. Ga jerin makarantu da abin ya shafa: Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Minjibir, Jihar Kano Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Ganduje, Jihar Kano Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Zariya, Jihar Kaduna Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Kafanchan, Jihar Kaduna Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya, Bakori, da wacce ke Bwari, Abuja. Kwalejin Fasaha...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai Gidan Gwamnati da ke Dutse. Ya taya shugaban kwalejin da tawagarsa murna, inda ya bayyana nadin nasu a matsayin tarihi kuma mai matuƙar muhimmanci. Malam Umar Namadi ya ƙara da cewa kafa sabuwar cibiyar ilimi aiki ne babba, yana mai bayyana tabbacin cewa  mutanen da aka zaba don fara gudanar da kwalejin za su taka rawar gani. “Kafa sabuwar cibiyar ilimi ba abu ba ne...
    Daga Abdullahi Shettima Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya karɓi Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan manyan muhimman abubuwan ci gaban jihar musamman a fannoni na noma, ababen more rayuwa da tsaro. A yayin ganawar, Gwamna Uba Sani ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa bisa goyon bayan da gwamnatin tarayya ke bai wa Jihar Kaduna, musamman wajen ci gaban harkokin noma da sarrafa amfanin gona. Ya ce kafa Special Agro-Industrial Processing Zone (SAPZ) da African Quality Assurance Centre (AQAC) ya ɗaga martabar jihar a matsayin jagora wajen ci gaban sarkar samar da kayayyakin noma da kuma faɗaɗa damar fitar da su ƙasashen waje. Shugaban Ƙasa ya yaba da wannan...
    Daga Aliyu Muraki Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa  ta Kasa reshen Jihar Nasarawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya Lafia ta bi umarnin ƙungiyar ta ƙasa wajen shiga yajin aiki na ɗindindin. Wakilinmu wanda ya ziyarci asibitin koyarwar, ya bayar da rahoton cewa likitocin sun bar wuraren aikinsu domin matsin lamba ga gwamnatin tarayya ta biya dukkan hakkokinsu da ke karuwa zuwa biliyoyin naira. A yayin ziyarar, ya ruwaito cewa nas nas da ungozoma ne kawai ke kula da marasa lafiya, musamman a sashen bada kulawar gaggawa,  inda suke ƙoƙarin taimaka wa waɗanda ke cikin mawuyacin hali, yayin da ake tura waɗanda lamuransu ke neman kulawar likitoci zuwa wasu asibitoci domin samun kulawar gaggawa. Haka zalika su ma likitocin ...
      “Wannan yajin aikin yana nan yana gudana, har sai an biya duk buƙatunmu mafi ƙaranci,” in ji shi.   NARD ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani a duk faɗin ƙasar a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, bayan abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati na cika jerin “mafi ƙanƙancin buƙatunta.” Wannan matakin dai tuni ya riga ya kawo cikas ga ayyuka a asibitoci mallakar gwamnatin tarayya da na jiha a faɗin ƙasar.   A halin yanzu, Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, a cikin wata sanarwa da Shugaban Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Alaba Balogun ya fitar, ya nace cewa, gwamnati ta saki kuɗaɗe kuma tana ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin...
    Jami’ar Tarayya ta Dutsinma ta zabi Farfesa Muhammed Khalid Othman a matsayin sabon Shugaban Jami’ar na dindindin, tare da amincewar Majalisar Gudanarwar Jami’ar. Da yake zantawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, Magatakardar Jami’ar, Dokta Musa Ajiya, ya bayyana cewa mai kula da jami’ar (Pro-Chancellor), Ali Abubakar-Jatau, ne ya sanar da nadin. A cewar Dokta Ajiya, Abubakar Jatau wanda shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa, ya bayyana hakan ne bayan taron na musamman karo na 36 da aka gudanar a daren Juma’a. Ya ce Farfesa Othman ya fito ne a matsayin wanda ya fi kowa cancanta bayan wani tsari na tantancewa mai tsauri kuma bisa gaskiya, a cikin mutane 17  da suka nemi mukamin 17. Ya ƙara da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Siyasa Babu Rikici A Jam’iyyar APC A Nasarawa — Shugaban Jam’iyya October 21, 2025 Siyasa Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu October 20, 2025 Siyasa Tsohon Ɗan Majalisar Bayelsa Ya Shawarci Jonathan Ya Guji Neman Takara A 2027 October 17, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima  October 17, 2025 Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025
    Amma ya nuna damuwa cewa jinkiri wajen aiwatar da yarjejeniyar da gwamnati ta yi da ASUU na ƙara haifar da rashin jituwa. Ya roƙi Shugaba Tinubu, da ya sa baki kai-tsaye don kawo ƙarshen rikicin, yana mai gargaɗin cewa jinkiri wajen ɗaukar mataki na iya gurgunta ci gaban da aka samu a fannin ilimi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa October 15, 2025 Labarai Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu October 15, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Bindiga Sun Hana Manoma Girbi A Zamfara, Al’umma Na Neman Taimako October 15, 2025
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don  Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025
    Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu. A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana. Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja “Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar. Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin...
    Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta.   A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare.   Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da...
    Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da sabon Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da aka gina a garin Kumo, Ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne tare da halartar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da kuma Ministan Kula da Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate. NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe A jawabinta, uwargidan shugaban Ƙasar ta ce wannan asibiti na nuna sakamakon jagoranci irin na hangen nesa ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ta ce, asibitin zai ƙara inganta damar samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Jihar Gombe da ma maƙwabtan jihohi, tare da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Wannan muhimmin al’amari ya sake tabbatar da himmar Gwamnatin Tarayya a fili don kiyaye walwala da haƙƙin ’yan fansho dake ƙarƙashin shirin (DBS) bisa ga manufar sabunta fata,” in ji Daraktan PTAD.   Mahukunta PTAD sun nuna jin daɗinsu ga shugaba Tinubu kan amincewa da tallafin gaggawar, wanda a cewarsu hakan zai inganta jin daɗi da walwalar masu karɓar fanshon. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin da aka shirya gudanarwa domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba. Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Litinin daga Ofishin sakataren gwamnatin tarayya. “Soke faretin bikin ƴancin kai da gwamnati ta shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga Oktoba ba zai rage darajar wannan muhimmiyar rana ta tarihi ba,” in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati na ba da haƙuri kan wannan sauyi, amma sauran ayyukan da aka tsara domin zagayowar ranar za su ci gaba kamar yadda aka tsara. Wannan ya haɗa da jawabin shugaban ƙasa, bukukuwan al’adu, da wasu abubuwa da aka shirya.
    Gwamnatin Tarayya ta sanar da gobe Laraba a matsayin ranar hutu a ƙasar somin bikin cikar ƙasar shekara 65 da samun ƴancin kai. Cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na ƙasar, Olibunmi Tunji-Oja ya fitar, ya taya ƴan Najeriya murnar cimma wannan ”babban matsayi”. Ministan ya kuma buƙaci ƴanƙasar su ci gaba da nuna kishin ƙasa da hadin kai da juriya, waɗanda ya ce su ne ke taimaka wa ƙasar wajen dunƙulewa tun lokacin samun ƴancin kai a 1960. A ranar 1 ga watan Otoban 1960 ne dai Najeriya ta samun ƴancin kai daga Turawan mulkin Birtaniya da suka yi mata mulkin mallaka.
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewar ma’aikatar, dakatarwar ta na nufin samar da damar ci gaba da tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki da kuma yin cikakkiyar bitar tsarin harajin da tasirinsa na dogon lokaci ga tattalin arziki. A watan Afrilu 2025, Kwaturola Janar na Kwastom, Adeniyi, ya bayyana shirin sake gabatar da harajin kashi 4 bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, cewa wannan cajin, wanda ake lissafawa bisa Free on Board (FOB) na kayan da ake shigowa da su, an riga an sokƙ shi a baya daga al’umma masu kasuwanci saboda nauyinsa ga masu shigo da kaya. Nan da nan sanarwar ta jawo cece-kuce daga ƴ an kasuwa, kamfanonin jigilar kaya, da ƙungiyoyin masana’antu, waɗanda suka bayyana cewa matakin zai rage...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan asarar rayuka da aka yi a gobarar da ta tashi a ranar Talata a Afriland Towers da ke Broad Street, a  Legas.   A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma hukumomi da ma’aikatan hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS), United Capital, United Bank for Africa (UBA) Plc, da kuma Afriland Properties Limited.   Ya kuma jajanta wa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan bala’in, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.   Shugaba Tinubu ya yaba da matakin da hukumomin gaggawa...
    Mataimakinsa kan harkokin majalisa Honarabul Attahiru Danmadi ne ya wakilci dan majalisar ya kuma tabbatarwa wadanda lamarin ya shafa kokarinsa kan daukar matakan da suka kamata domin tabbatar da tsaron rayukan su da dawowa da zaman lafiya a yankunan.   Garuruwan da ‘yan bindigar suka tarwatsa a gundumar Kuchi sun hada da Fakku, sha’alwashi, tulluwa da Rafin- gora a inda mutane bakwai suka rasa rai. A gundumar Jabo kuwa kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Gesolodi, Hilya, Guraye, Guma, Chakai, Modo, Badariya, Tafki, Balera, Gudumawa da Rafin shinka.   “Mun girgiza kwarai da wannan halin da kuke ciki. A matsayina na wakilin ku, zan ci-gaba da kokarin da ya kamata a majalisa domin ganin jami’an tsaro sun kawo karshen...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, tsohon shugaban kungiyar masu tsara gidaje a Nijeriya, Aliyu Wammako, ya ce, rashin biyan ‘yan kwangila kudadensu na shafan tattalin arziki sosai. Ya bukaci gwamnatin tarayya da ka da ta tsaya bata wani lokaci ta kama biyan ‘yan kwangila kudadensu da hakan zGwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da wani kwamiti da zai tattauna batun basussukan da suka dabaibaye harkokin jakadancin Nijeriya a kasashen ketare. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen waje, Kimiebi I. Ebienfa, shi ne ya shaida hakan ya cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Abuja. Ebienfa ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar da cewa an yi amfani da kudaden da aka tura domin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Idris ya ce a tsawon shekaru ‘yan Nijeriya suna tafiya Amurka saboda dalilai daban-daban, ciki har da yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu, da kuma neman magani.   Ya ce: “An san Nijeriya a duniya a matsayin ƙasar da ‘yan ƙasar ta suke yawan yin tafiya zuwa ƙasashe daban-daban, suna hulɗa da ƙasashen duniya ta fuskar harkar kasuwanci, ilimi, yawon buɗe ido, da sauran muhimman fannoni. Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suka fi ziyarta, abin da ke nuna zurfin dangantaka mai tsawo tsakanin ƙasashen biyu.   “Yawancin ‘yan Nijeriya suna zuwa Amurka ne domin karatu, aiki, neman magani, ziyartar ‘yan’uwa, yawon buɗe ido, da damar zuba jari.   “Wannan mu’amala mai ƙarfi tana...
    Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere.   A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mai wakiltar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kowane dan wasa zai karbi dala 100,000, yayin da koci da kungiyar kwararru za su samu dala 50,000 kowanne, tare da karramawar kasa ga daukacin kungiyar. Ya kuma yi alkawarin karin tukuicin da zai zo.   Shettima ya ce ba wai don murnar nasarar da kungiyar ta samu a cikin shekaru 78-64...
    A cewar NANNM, sun dakatar da yajin aikin ne domin ci gaba da tattaunawa bisa alƙawarin da gwamnati ta ɗauka na aiwatar da buƙatun cikin ƙanƙanin lokaci. Takardar ta ce, “Kwamitin zartarwa na ƙasa ya yaba da matakan da gwamnatin tarayya ta fara ɗauka, musamman yadda ta bayyana lokacin da za ta aiwatar da buƙatunmu guda tara da muka gabatar.” Takardar da shugaban ƙungiyar NANNM, Kwamared Haruna Mamman, da sakataren janar, Dr. A. Shettima suka sanya wa hannu, ta umarci mambobinsu da su koma bakin aiki nan take. Haka kuma shugabannin na ƙasa za su ci gaba da lura da yadda gwamnati za ta cika alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyar ta kuma gargaɗi duk wata cibiyar lafiya ko hukuma da...
    Kwamitin ya nemi a mayar da sama da Naira miliyan 124, kusan dala 795,000 zuwa asusun gwamnatin tarayya, an kuma bayar da karin wasu kudade da suka hada da Naira miliyan 31.7 da dala 155,923.00, a matsayin wadanda aka kashe ba bisa ka’ida ba. An umarci ma’aikatar da ta kwato Naira miliyan 49.4 da aka biya, domin yin gyaran ba tare da bin ka’idojin sayen kayayyakin ba. Kazalika, an raba Naira miliyan 9.2 ga jami’an ofishin jakadancin, ba tare da cikakkiyar shaida ba. Haka nan kuma, an binciki bankin noma; kan basussuka kimanin Naira biliyan 75.6. Kwamitin ya umarci hukumar da ta buga jerin sunayen wadanda ake bi bashi a akalla a jaridu guda uku na wannan kasa tare da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya ce; Amincewa da aikata zalunci, ya yi daidai da hada baki da mai aikata shi.” Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto Dr. Baka’i wanda ya wallafa sako a shafinsa na X cewa; Shugaban gwamnatin kasar Jamus yana ci gaba da nuna goyon baya ga munanan ayyukan da HKI take aikatawa wanda yake cin karo da yarjeniyoyin MDD da kuma dokokin kasa da kasa.” Haka nan kuma Dr. Baka’i ya ce; Abinda Jamus din ta aikata zai mayar da ita wacce za ta amsa tambayoyi a matsayin wacce take yin zuga a aikata laifi. A lokacin da HKI ta fara kawo wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran hare-hare dai shugaban...
      Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan.   Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin da ya kai ziyara ta jaje ga iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu a Zaria, inda ya nuna alhini da ta’aziyya ga dangin waɗanda wannan al’amari ya shafa.   Tsohon Akanta Janar na Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Kajuru, ya yi Allah-wadai da kisan, yana mai jaddada cewa babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na kashe...
    Wannan matakin ya biyo bayan shawarar Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na ASUU wanda ya amince da tsarin “Ba Albashi, Ba Aiki” saboda yawan jinkirin biyan albashi da suke fuskanta. ASUU ta ɗora laifin hakan kan Ofishin Akanta-Janar na Tarayya. Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana a ranar Litinin cewa gwamnatin na nuna halin ko-in-kula kan batun. Ya ce duk da yawan ganawa da jami’an gwamnati, malamai na fuskantar jinkirin albashi ba tare da wani dalili ba. “Muna so mu yi aiki, amma ba za mu iya ba saboda ba su ba mu damar yin haka ba. Wannan aiki ne da aka yi da gangan. Matsalar ba daga wajen tsarin biyan albashi ba ne, matsalar tana wajen...
    Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya. “Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi. Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya...
    Haka kuma, an ce ta ƙara da cewa: “Mu tambayi Shugaban Majalisar Dattawa, me ya sa ya janye jami’an tsarona tun farko, idan ba don ya sa a kai min hari ba? Ya ce a kashe ni, amma a kashe ni a Kogi.” Gwamnati ta bayyana cewa waɗannan kalaman suna da nufin ɓata suna, kuma hakan ya saɓa da Sashe na 391 na Dokar Laifuka 89, Dokokin Tarayya na shekarar 1990. Hukuncin laifin yana ƙarƙashin Sashe na 392 na wannan doka. A wani tuhumar daban, an zargi Sanata Natasha da yin irin waɗannan kalaman game da Akpabio a cikin wata tattaunawa ta waya da wata Sandra C. Duru a Abuja, a ranar 27 ga watan Maris, 2025. An ƙara tsaurara...
    Ya ce duk da cewa akwai damuwa kan yadda za a aiwatar da hakan, Gwamnatin Tarayya na da damar tsara ƙa’idoji da dokoki na musamman ga kowace jiha don hana amfani da ‘yansandan wajen cin zarafi. A halin yanzu, gwamnonin jihohi daga faɗin Nijeriya na gudanar da wani taron gaggawa a Babban Birnin Tarayya, wanda ke gudana a sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF). Taron ya samu halartar gwamnonin jihohi da mataimakansu daga dukkanin jihohi 36 na ƙasar. Koda yake ba a bayyana cikakken ajandar taron ba, kasancewar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, na cikin mahalarta taron, ya nuna cewa batutuwan tsaro ne ke kan gaba a tattaunawar. Taron na...
    Sanarwar ta ƙara da cewa ana aiki tare da hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin ganin an gudanar da aikin kwasar cikin tsaro. Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙarshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a waɗannan ƙasashe. “Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntuɓar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun ƙarin umarni.” Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da faɗa tsakanin Isra’ila da Iran, tare da buƙatar ɓangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare...
    Gwamnatin Tarayya ta roƙi ƙasashen Isra’ila da Iran da su daina rikici, su zauna lafiya su sasanta tsakaninsu.  A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar, ta bayyana damuwa kan yadda rikicin ke ƙara ta’azzara, inda ta nemi ɓangarorin biyu da su kai zuciya nesa don samar da zaman lafiya a duniya baki ɗaya. Mahara sun kashe mutum 26 a sabon hari a Binuwai Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung Sanarwar ta ce faɗa da ramuwar gayya na jefa rayukan fararen hula cikin hatsari, kuma yana iya haddasa rikici mai muni a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda hakan zai iya barazana ga tsaron duniya da kuma ci gaban tattalin arziƙi dunuya....
    Biyo bayan sauya sheka da aka yi kwanan nan, a zauren majalisar dattawa, APC na da kujeru 68; PDP na da 30; LP na da 5; SDP na da 2; NNPP na da 1; APGA na da 1 da kuma kujeru guda biyu da babu kowa, guda daya daga Jihar Edo da daya daga Jihar Anambra. Masana harkokin siyasa na ganin cewa bisa yadda lamura suke a halin yanzu, adadin na iya haurawa lokacin da majalisar tarayya ta dawo daga hutu, bayan sauya shekar Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom daga PDP zuwa APC. Ana sa ran wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya na jihar za su iya bin sahunsa. A halin yanzu, Jihar Akwa Ibom tana da sanatan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ce a nemi bayani daga wurare daban-daban kamar Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) da Ma’aikatar Kudi, ya kara da cewa sakataren gwamnatin tarayya shi ne shugaban kwamitin aiwatar da hukuncin. Abubuwan da mutane yawa suke gnin ya janyo jinkirta aiwatar da hukuncin shi ne, shigar da sabon sharadi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda ke bukatar dukkanin hukumomin gwamnati 774 su bayar da akalla shekaru biyu na rahotannin kudinsu kafin su iya karbar kasafin kudadensu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya. Babban bankin ya bayyana cewa dole ne gwamnatocin kananan hukumomi su cika bukatun kafin su bude asusu don kura musu kudadensu kai tsaye. Ka’idojin da aka gindaya wa kananan hukumomin ya kara janyo tsaiko wajen jinkirta aiwatar...
    Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
    Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta ARD-FCTA, Dokta George Ebong, da babban sakataren kungiyar, Dr. Agbor Affiong, sun yi Allah wadai da matakin da gwamnati ta dauka na cire ma’aikatan da abin ya shafa daga cikin tsarin albashi ba tare da sanarwa ko tuntuba ba, inda kungiyar ta ya bayyana matakin a matsayin “rashin gaskiya da adalci”.   A cewar kungiyar, ma’aikatan da aka kora da suka hada da likitoci, ma’aikatan jinya, masu kula da bangaren magunguna, da masana kimiyyar dakin gwaje-gwaje, an yi kuskure ne aka bayyana su a matsayin ma’aikatan bogi ko kuma wadanda basu zuwa aiki, duk kuwa da gudummawar da suke bayarwa wajen gudanar da ayyukan asibiti. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Mambobin Jam’iyyar PDP shida a Majlisar Wakilai daga Jihar Delta sun sauya sheka zuwa Jam’iyya APC. Kazalika wasu biyu daga Jihar Enugu sun sauya sheka daga Jam’iyyar adawa ta LP zuwa PDP. Shugaban Majalisar Wakiliai, Abbas Tajuddeen, ne ya sanar da hakan bayan dawowar majalisar daga hutu a ranar Talata. Shugaban Majalisar ya bayyana cewa ’yan majalisar sun yanke shawarar sauya sheka ne sakamakon rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyun nasu a matakin jiha da kuma kasa. Wadanda sauka sauya sheka zuwa APC su ne: Victor Nwokolo,  Julius Pondi, Thomas Ereyitomi, Nicholas Mutu, Okodiko Jonathan, da kuma Nnamdi Ezechi. Wadanda suka bar LP zuwa PPD su ne Mark Obetta da kuma Dennis Nnamdi. Idan ba ma manta ba a kwanakin baya...
    Saleh ya ce, kaddamar da injin kyankyasar, musamman saboda jajircewar ma’aikatan sashen kan wannan aiki, tuni Jami’ar ta fara ganin sakamako mai kyau.   Ya kara da cewa, samar da wannan inji, ya kara nuna irin mayar da hankali da Jami’ar ta yi, wajen habaka fannin aikin noma ta hanyar amfani da kimiyyar zamani da kuma samar wa daliban fannin kimiyyar Jami’ar kayan aikin zamani da za su rika gudanar da ilimin yin gwaje-gwaje da kuma bayar da gudunmawa wajen kara samar da wadataccen abinci a kasar.   Kazalika, wannan nasara ta kuma nuna a zahiri irin kyakkyawan shugabancin Shugabar Jami’ar, Farfesa Maimuna Waziri, duba da irin kokarinta na dora Jami’ar a kan turba mai dorewa, musamman a bangaren samar...
    Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata,  jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National  ”  bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
    Shi dai filin jirgin saman, wanda gwamnatin Umaru Bago ta gina a Jihar Neja, an raɗa masa sunan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.   Jirgin kasuwancin na farko mallakin kamfanin Overland Air mai lamba 5N-CCN ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:32 na rana.   Cikin fasinjojin akwai Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, Minista Mohammed Idris, tsohon Gwamnan Neja Dakta Babangida Aliyu, Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, da wasu manyan jami’an gwamnati.   Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda samar da yanayin da ya bai wa filin jirgin damar fara aiki, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar Shugaban Ƙasa wajen inganta ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.   Haka kuma, Ministan...
    ’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya. Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje. Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin...
    “Amma gwamnoin sun ce a’a. Ba sa son hakan. Sun ce idan kudaden n ya kai ga CBN, ya nuna cewa gwamnatin tarayya ce take kulawa da komi.” Majiyar ta ce tattaunawar Tinubu da gwamnoni ya bayyana cewa, gwamnonin na bukatar a kai kudaden zuwa bankunan kasuwanci nan take. “Daya daga cikin gwamnonin ya ce idan har CBN ke kula da asusun, za su bukaci amincewa daga wurin akanta janar na Nijeriya. Wannan yana nufin cewa har yanzu yana karkashin ikon gwamnatin tarayya ne kuma ba su bukatar hakan ya faru. Suna son a kai shi ga banki na kasuwanci. Amma gwamnatin tarayya ta ki amincewa,” in ji majiyar. Game da sakamakon ganawar, majiyar ta ce, “Sun ce ganawar ta...
    ’Yan sanda sun kama gungun wasu makiyaya 47 ɗauke da makamai kan zargin kutse da yunƙurin aikata kisa a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya ta Umaru Waziri da ke Shinkafi a Jihar Kebbi. Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar ya ce makiyayan sun haɗa baki ne da wani mutum wajen rusa katangar makarantar suka kutsa cikinta da garken shanu sama da 300. Ya ce da shigarsu ke da wuya. sai suka zarce zuwa ɓangaren gidajen ma’aikata suka lalata musu haki. Ya ƙara da cewa makiyayan sun kuma sari wani jami’in tsaron makarantar da adda a ƙafarsa ta dama a hannunsa na dama. Dalibai 179 sun kammala Dirigi da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero Gwamnan Zamfara ya...
    ’Yan sanda a Babban Birnin Tarayya Abuja sun buƙaci al’umma su kawo musu rahoton duk wanda aka ga yana sana’ar bola-jari a cikin gari. Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, Disu Olatunji, ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar Tsaro ta Babban Birnin Tarayya wanda Minista Ezenwo Nyesom Wike ya jagoranta. Idan ba a manta ba, a ranar 13 ga watan Janairu, 2025 ne Hukumar Babban Birnin Tarayya ta haramta ayyukan ’yan bola-jari a cikin faɗin birnin. Umarnin ya taƙaita ayyukansu ga kan juji da ke ya yankunan da suke wajen birnin. A lokacin zaman ne aka dakatar da ayyukan ’yan gwangwan na tsawon makonni biyu, saboda zargin alaƙarsu da ’yan bola-jari. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu...
    Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu varna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya. “Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu. “Haka zalika za a bukaci masu gudanar...
    Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu barna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya. “Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu. “Haka zalika za a bukaci masu gudanar...
۱