Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba
Published: 22nd, November 2025 GMT
Gwamnatocin jihohin Katsina da Taraba sun ba da umarnin rufe makarantu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka sace daruruwan ɗalibai a makarantu a cikin mako guda a jihohin Kebbi da Neja.
Gwamnatin Jihar Taraba ta rufe makarantun kwana a fadin jihar, inda ta ba da umarnin a koma tsarin jeka-ka-dawo sakamakon tabarbarewar tsaro.
Gwamnan Agbu Kefas, ya umarci duk makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da dalibai su daina kwana a makarantu saboda fargabar tsaro a faɗin ƙasar.
Sanarwar da kwamishinar ilimi ta jihar, Augustina Godwin, ya fitar ta ce garkuwa da ɗalibai a Kebbi da Neja ta sanya daliban makarantun kwana zama cikin hadari.
Don haka gwamnati ta umarci komawa tsarin jeka-ka-dawo har sai tsaro ya inganta.
Hakan na zuwa ne a yayin da Gwamnatin Jihar Katsina ta bayar da sanarwar rufe dukkan makarantun gwamnatin, har sai abin da hali yayi.
Sanarwar da ta fito daga Hukumar Ilimin Firamare da Sakandaren jihar a ranar juma’a ta ce, ya ce makarantun za su kasance a rufe har sai an ga ci-gaban da aka samu na yanayin matsalar tsaron da ake fuskanta.
Gwamnatin tace tana nan tana bibiyar yadda sha’anin tsaron yake gudana kafin ɗaukar mataki na gaba.
Waɗannan matakai na zuwa ne bayan ’yan bindiga sun sace ɗalibai kimanin 340 a cikin mako guda a makarantun kwana a jihohin Kebbi da Neja.
A ranar Juma’a aka sace ɗalibai da malamai 315 a makarantar kwana ta St Mary da ke Jihar Neja, kwana huɗu bayan a ranar Litinin sun sace dalibai mata 26 suka kashe jami’an tsaro biyu a makarantar ’yan Mata ta Gwamanti GGCSS da ke yankin Maga a Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu ta Jihar Kebbi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai garkuwa da ɗalibai makarantu
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja
’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba.
Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an yi awon gaba da ɗalibai da dama yayin harin da aka kai makarantar.
’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a KebbiWata majiya daga ɗaya daga cikin coci-cocin Katolika a jihar ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa har yanzu makarantar na kan tattara bayananta a kan harin.
“Eh, gaskiya ne, amma ba ni da ikon bayar da cikakkun bayani. Coci za ta fitar da sanarwa a hukumance daga baya a yau,” in ji shi.
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai bayar da cikakkun bayanai daga baya.
Sai dai shugaban sashen bayar da agaji na ƙaramar hukumar Agwara, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da harin ta wayar salula.
Ya ce ’yan ta’addan sun kai hari kan makarantar ne tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na dare, yana mai cewa ba a kai ga tabbatar da adadin ɗalibai da malaman da aka sace ba tukuna, domin har yanzu hukumomi na ci gaba da tantancewa.
Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan irin wannan hari a Maga, Jihar Kebbi, inda aka yi garkuwa da ɗalibai mata 25, abin da ya ƙara tayar da hankula kan tabarbarewar tsaro a makarantu a yankin.
Ko a ranar Alhamis, sama da makarantu 50 aka rufe a Jihar Kwara sakamakon barazanar ta’addancin ’yan bindiga.
Shugaba Bola Tinubu ya soke tafiyarsa zuwa kasashen Afirka ta Kudu da Angola domin jagorantar dakile matsalolin tsaron.