HausaTv:
2025-11-20@19:38:27 GMT

Nigeria: An Rufe Makarantun Kwana A Jahar Kwara Saboda Matsalar Tsaro

Published: 20th, November 2025 GMT

Mahukunta a Jahar Kwara sun sanar da rufe makarantu a garuruwan Ifelodun,Ekiti, Irepodun, Isis, da Oke Ero, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta

Kwamishinan ilimi na Jahar ta Kwara Lawal Olohungabebe ne ya sanar da daukar wannan matakin saboda abinda ya kira bayar da kariya ga rayuwar daliban da suke fuskantar barazanar masu dauke da makamai da suke karakaina a yankin.

Gwamnatin ta Kwara ta dauki wannan matakin ne bayan wani lokaci kadan daga kustawa cikin wata majama’a da masu dauke da makamai su ka yi a Eruku dake karamar hukumar Ekiti.

Mazauna yankin dai sun fada cikin frigici da razana haka nan kanan hukumomin da suke makwabtaka. An bayar da umarnin a rufe makarantun kwana na Irepodun saboda rahotanni na sirri da ake da su cewa za su iya zama wuri na gaba da za a kai wa hari.

Arewacin Najeriya dai yana fuskantar matsalolin tsaro da a farkon wannan makwan aka sace dalibai 25 a makarantrar Maga ta ‘yan mata a jihar Kebbi. A yayin harin da masu dauke da makamai su ka kai sun kashe malami da kuma mai gadi.

A Jahar ta Kwara mahukunta sun ce ba za a bude makarantun ba har sai idan jami’an tsaro sun sanar da samun yanayin da ya dace a yi hakan.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah: Ba Za Mu Taba Ajiye Makamanmu Ba November 20, 2025 Ribadu Ya Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Amurka Kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla November 20, 2025 Hukumar Kula Da Jiragen Sama Ta Najeriya Ta ci Tarar Kamfanin Jiragen Sama Na Qatar November 20, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Kara Dagulewar Al’amura Bayan Harin Isra’ila A Gaza November 20, 2025 Labanon Ta Bukaci Gudanar Da Taron Kwamitin Tsaro Na MDD Cikin Gaggawa November 20, 2025 Achraf Hakimi Ya Zama Gwarzon Wasan Kwallon Kafar Afirka Na Shekara Ta 2025 November 20, 2025 Kasashen Iran Da Malesiya Sun Rattaba Hannu Kan Jarjejeniyar Fadada Dangantakar Addini November 20, 2025 Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 27 a wani sabon harin bam November 20, 2025 Iran : daftarin kudurin da Canada ta gabatar, siyasa ce da kin jininmu November 20, 2025 AU ta yi Allah-wadai da tsoma bakin kasashen waje a harkokin tsaron Afirka November 20, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a Zirin Gaza.

Mambobi 13 daga cikin 15 na Majalisar sun amince da kudurin, inda Rasha da China suka kaurace wa kada kuri’ar.

Kudurin yana da nufin tura sojojin kasashen waje na wucin gadi don kula da tsaro, tallafawa sake ginawa da kuma kiyaye tsari a yankin. Daftarin ya yi kira ga rundunar ta yi aiki na tsawon shekaru biyu, tare da yiwuwar kara sabunta wa’adin aikinta wanda ya danganta ne da ci gaban da ake samu a kasa.

Kudurin ya kunshi abubuwa da yawa,  ciki har da kare iyakokin Gaza, kare fararen hula, kare hanyoyin jin kai, da kuma horar da sabbin ‘yan sandan Falasdinu da aka tantance. Hakanan ya ba da izinin amfani da “dukkan matakan da suka wajaba” don cimma wadannan manufofi, gami da wargaza kungiyoyi masu dauke da makamai da kwace makamai marasa lasisi.

Muhimmin fasali na kudurin shine ƙirƙirar hukumar wucin gadi, wacce wani lokacin ake kira “Hukumar Zaman Lafiya,” wacce za ta yi aiki tare da rundunar kasa da kasa don taimakawa wajen gudanar da harkokin Gaza. Shirin ya kuma yi kira da a shigar da cibiyoyin kuɗi na duniya, kamar Bankin Duniya, don ba da kuɗaɗen ayyukan sake ginawa da kuma kula da gudanar da asusun tallafi na musamman.

Daftarin kudurin ya jawo suka daga ƙungiyoyin Falasɗinawa, waɗanda ke bayayya cewa ya ƙunshi wani nau’i na mulkin mallaka da Rashin ‘yancin kai, daga cikin kungyoyin da suka nuna damuwa kan kudirin har da kungiyar Hamas.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Congo ta tsawaita haramcin fataucin ma’adinai a gabashin kasar November 18, 2025 Rasha: An dakile wani yunkurin kisan gilla kan Sakataren Majalisar Tsaron kasa November 18, 2025 Aref: Iran Tana Da Kyakkyawar Alaka Da Mambobin Kungiyar Hadin Gwiwa Ta Shanghai {SCO} November 17, 2025 Na’ini: Jagora Ne Da Kansa Ya Jagoranci Lamurra A Lokacin Yakin Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran November 17, 2025 Mahukuntan Gaza Sun Yi Gargadin Bullar Bala’in Jin Kai A Yankin Da Ba A Taba Ganin Irinsa Ba November 17, 2025 Sheikh Na’im: Gwamnatin Lebanon Zata Yi Babban Kuskure Matukar Tabi Hanyar Sassauci November 17, 2025 Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango November 17, 2025 Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro
  • Labanon Ta Bukaci Gudanar Da Taron Kwamitin Tsaro Na MDD Cikin Gaggawa
  • Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya
  • Shugaban gwamnatin Togo zai gana da Shugaba Putin na Rasha
  • Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi
  • Nijar: An Dakatar Da Ayyukan Kungiyoyin Agaji Da Dama
  • Hamas Ta yi Watsi Da Amincewa Da Kudurin Amurka Da Kwamitin Tsaro Ya yi Kan Gaza
  • Ministan tsaron Iran na Ziyara a UAE don karfafa dangantakar tsaro tsakanin kasashen yankin
  • MDD ta amince da kudurin tura dakarun kasa da kasa zuwa Gaza