Matasan Kauru Sun zargin Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin tabuka komai
Published: 7th, August 2025 GMT
Matasan Kauru Sun zargin Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin tabuka komai
Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai taken daga ‘Daga Fata zuwa Yaudara’ wanda kuma Junaidu Ishaq Maisalati, ya sanyawa hannu, kungiyar ta caccaki dan majalisar kan abin da ta bayyana a matsayin mai dimama kujera kuma ɗan siyasar da ya gaza wajen gudanar da ayukka a mazabar da kuma aikin da zai amfani al’umma.
Sanarwar ta koka da yadda al’ummar Kauru suka sanya kyakkyawan fata a shugabancin Danmaigona, amma a maimakon haka, ya kasa ba marada kunya.
Har ila yau, ta yi Allah-wadai da kawancen siyasarsa da Mukhtar Chawai, wani dan siyasa da aka ce ko ake zargin baya tabuka komai a mazabarsa ba, tare da bayyana cewa irin wannan kawancen yana kashe musu gwiwa matukar gaske.
KYA ta bayyana rashin jin dadin ta a kan abin da suka kira wasu ‘yan kudaden da basu gaza dubu 5 zuwa 10 da yake rabawa jama’a a matsayin yankawa kare ciyawa domin wannan ba abin da suke tsinanawa al’ummar da yake wakilta
Saboda haka Kungiyar ta bukaci al’ummar mazabar Kauru da su tashi tsaye akan nuna halin ko-in-kula a siyasance, su nemi wakilcin da ya dace, sannan su ki yarda a ba su kyauta irin wannan da bata tsinana musu komai.
Sun yi nuni da ‘yan majalisa irin su Hon. Shehu Yunusa na Kubau, wanda rahotanni suka ce ya ba da fifiko wajen hada kai da ci gaba, a matsayin misalan yadda wakilci na gaskiya ya kasance.
Da take kira da a wayar da kan ‘yan siyasa da kuma daukar matakin gama gari, sanarwar ta kalubalanci matasa da masu kada kuri’a a Kauru da su yi wa shugabanninsu hisabi, inda ta dage cewa zabe aiki ne..
KYA ta bayyana cewa Hon. Danmaigona ya samu damarsa, kuma har yanzu jama’a na nan suna jira, ba wai kawai alkawura ba, a’a, a samu canji na zahiri.
Rel/Yusuf Zubairu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp