Tankin ruwa ya kashe mutum 4, wasu sun jikkata a Jigawa
Published: 19th, November 2025 GMT
An shiga jimami a garin Zugai da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare yin sanadin rasuwar mutum da jikkata wasu.
Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu.
An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya auku ne kwana uku bayan shugaban Ƙaramar Hukumar, ya raba ruwa ga masu sana’r sayar da ruwa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu mutane.
Tankin ruwa, wanda ke amfani da hasken rana wajen samar da ruwa, ya fashe yayin da mutane da yawa suka taru a ƙasa domin ɗibar ruwa.
Shaidu sun ce tankin ya rushe ba zato ba tsammani, inda mutum uku suka mutu nan take, waɗanda suka jikkata aka garzaya da su asibiti.
Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Roni, Dokta Abba Ya’u Roni, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya tabbatar da mutuwar mutum huɗu.
Dokta Abba, ya ce fashewar tankin ta faru ne sakamakon iska mai ƙarfi wadda ta turo tankin ya faɗo kan mutane.
Ya ƙara da cewa: “Na umarci mataimakina da jami’an majalisa su kai ziyara ƙauyen don tabbatar da cewa duk waɗanda suka ji rauni an kula da su.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jigawa ruwa Tankin Ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Rushewar Ramukan Hako Ma’adinai Ta Kashe Mutane 32 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango
Rushewar ramukan hako ma’adinai ta kashe ma’aikata 32 a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 32 ne suka mutu a ranar Asabar sakamakon zaftarewar ƙasa a wani ma’adinan cobalt a kudancin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, yayin da ake ci gaba da neman waɗanda har yanzu ba a same su ba a yankin.
Zaftarewar ƙasa ta faru ne a wurin Kalandu da ke cikin ma’adinan Mulundu kusa da Kolwezi, wani wuri da kamfanin Bajiklem ke gudanar da shi a hukumance.
Ministan harkokin cikin gida na lardin, Rui Kawumba Mayondi, ya ce “masu hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba sun kai hari kan wurin duk da haramcin da aka sanya saboda ruwan sama mai ƙarfi da kuma haɗarin zaftarewar ƙasa,” ya ƙara da cewa “hawa da suka yi cikin gaggawa ya sa gadar da suka gina a kan wani rami da ambaliyar ruwa ta mamaye ta ruguje.”
Jami’in ya bayyana cewa zuwa yanzu ƙungiyoyin ceto sun gano gawawwaki 32 daga cikin tarkacen, kuma ana sa ran adadin waɗanda suka mutu zai ƙaru.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Alummar Kasar Ecodo Sun yi Watsi Da Batun Sake Dawo Da Sansanin Sojin Amurka A Kasar November 17, 2025 Sojojin HKi Sun Kashe Wasu Falasdinawa Guda 2 A Sansanin Yan Gudun Hijira November 17, 2025 Tawagar Wasan Wushu Ta Kasar Iran Ta Samu Lambobin Yabo 4 A Saudiya November 17, 2025 Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari November 17, 2025 Hamas Da Sauran Bangarorin Falasdinawa Sun yi Watsi Da Shirin Aikewa Da Dakarun Kasashen Waje A Yankin Gaza November 17, 2025 Nukiliya : Iran zata sake duba huldarta da IAEA idan aka dauki wani sabon mataki kanta November 17, 2025 Kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan daftarin kudirin Trump kan Gaza November 17, 2025 Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen November 17, 2025 Afirka ta Kudu na Binciken shigar wasu ‘yan gudun hijirar Falasdinu 153 cikin kasar November 17, 2025 Najeriya ba za ta buga kofin duniya ba karo na biyu a jere November 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci