Wannan domar dai an dogara da kundin tsarin aikin gwamnatin Tarayya bisa ga sashe na 10(1) na dokar Ilimi ta (National Minimum Standards and Establishment of Institutions) ta shekarar 1985.

 

A baya-bayan nan, an gano cewa sama da mutum 22,500 sun yi amfani da takardun bogi daga jami’o’i marasa izini a Benin da Togo daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta nemi hukumomin tsaro su gaggauta bincikar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan zarginsa da kalaman tayar da hankali.

Wannan na zuwa ne bayan kammala zaman majalisar zartarwa na 34 da aka yi ranar Alhamis a Fadar Gwamnatin Kano.

Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi CAF Tayi Watsi Da Alƙalan Wasan Nijeriya a Kofin Afrika Na 2025

Zaman ya mayar da hankali kan maganganun da Ganduje da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin suka yi, inda suka ce Kano na ƙara fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga.

Ganduje ya bayyana aniyar ɗaukar mutum 12,000 aiki wanda hukumar Hisbah ta sallama daga aiki, a wata ƙungiya mai alaka da ake kira da “Khairul Nas”.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce waɗannan maganganu na iya kawo koma baya ga harkar tsaro da ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi.

Majalisar ta kuma nuna damuwarta cewa ƙasa da awanni 48 bayan yin waɗannan maganganu, aka sake kai hari wasu yankuna na jihar.

Gwamnatin jihar ta sake godewa Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro kan goyon bayan da suke bayarwa wajen yaƙi da matsalolin tsaro.

Haka kuma ta yi gargaɗin cewa ba za ta bari wani ko wata ƙungiya ta kafa haramtacciyar rundunar tsaro ba a Jihar Kano.

A ƙarshe, gwamnatin ta roƙi jami’an gwamnati da’yan siyasa su guji yin maganganun da ka iya tayar da hankali.

Ta kuma tabbatar wa mazauna jihar cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da doka a faɗin Kano.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 163
  • Barau ya musanta zargin gwamnatin Kano, ya soki gwamna Abba
  • AU ta dakatar da Guinea-Bissau daga zama mamba a cikinta bayan juyin mulkin sojoji
  • Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano
  • Yadda ’yan mata ke kufancewa da kasuwancin fara a Kano
  • CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika
  • Portugal ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 a karon farko
  • Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali