Matsalar tsaro a Arewa na damuna matuƙa — Tinubu
Published: 23rd, November 2025 GMT
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce matsalar tsaro a yankin Arewa na damunsa matuƙa saboda tana kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya.
Ya bayyana haka ne a Jihar Kaduna, yayin bikin cikar Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), wanda Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya wakilce shi.
’Yan sanda sun daƙile harin ’yan bindiga, sun ceto mutum 25 a Zamfara Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin NajeriyaTinubu, ya ce gwamnatinsa ta gaji matsalolin tsaro masu yawan gaske, amma tana aiki tuƙuru don magance su.
Ya yi gargaɗin cewa Najeriya ba za ta ci gaba ba idan al’ummarta suka ci gaba da fuskantar hare-hare, talauci, da tsoro.
“Ba abin da ke damuna kamar matsalar tsaro a Najeriya, musamman a Arewa. Ba za mu ci gaba ba idan wani yanki yana cikin matsala.”
Ya yi kira ga shugabannin Arewa da su zama masu gaskiya da jarumta wajen nemo mafita.
Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta kawo ƙarshen ’yan ta’adda da ’yan fashi, tare da farfaɗo da tattalin arziƙin yankin.
“Mun gaza daga ranar da muka yi bacci lafiya alhali miliyoyin jama’a suna kwana cikin yunwa, matafiya suna tsoron yin tafiya.”
Tinubu ya ce yana fatan ganin Arewa mai aminci, ciki har da samar da man fetur daga yankunan Arewa da manyan ayyuka kamar sabon titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
Shugaban kwamitin amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, ya yi Allah-wadai da kashe-kashe da garkuwa da ɗalibai da malamai a jihohin Neja da Kebbi.
Ya roƙi gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen tashin hankali.
“Kashe-kashe, sace ɗalibai, da hare-haren da ake kai wa jami’an tsaro ba za su ci gaba da aukuwa ba. Gwamnati dole ta nemo hanyar kawo ƙarshen wannan lamari.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arewa Rashin Tsaro Sace Ɗalibai Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar
Gwamnatin Jihar Yobe, ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana a jihar domin kare ɗalibai, biyo bayan taɓarɓarewar rashin tsaro a wasu jihohin ƙasar nan.
Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Asabar.
Matsalar tsaro a Arewa na damuna matuƙa — Tinubu Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a NajeriyaYa bayyana cewa an yanke wannan mataki ne bayan taro kan sha’anin tsaro da Gwamna Mai Mala Buni ya yi tare da hukumomin tsaro, inda suka yi nazari kan barazanar da makarantu ke fuskanta a jihar.
Sanarwar, wacce sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi, Dokta Bukar, ya sanya wa hannu, ta ce an rufe makarantun kwana nan take har sai al’amura sun daidaita.
Gwamna Buni, ya roki jama’ar jihar da su ci gaba da yin addu’a domin samun zaman lafiya, inda kuma ya tabbatar da cewa gwamnati tana ɗaukar matakai don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan mataki na zuwa ne biyo bayan sace ɗalibai da ’yan bindiga suka yi a jihohin Kebbi da Neja.
Yanzu dai matsalar na ci gaba da tayar da hankalin jama’a a Najeriya, inda mutane da dama ke kiran gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.