Leadership News Hausa:
2025-11-08@12:24:26 GMT

Kashim Shettima Ya Isa New York Halartar Taron UNGA Na 80

Published: 22nd, September 2025 GMT

Kashim Shettima Ya Isa New York Halartar Taron UNGA Na 80

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya isa birnin New York, Amurka, domin halartar taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 wanda zai gudana daga ranar Litinin 22 ga Satumba zuwa Lahadi 28, 2025. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu, zai gabatar da jawabin Nijeriya a gaban zauren, tare da shiga wasu tattaunawa da tarukan a gefe da dama.

Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya za ta ci gaba da mara baya ga tsarin haɗin gwuiwa tsakanin ƙasashe, ciki har da yunƙurin samun kujerar dindindin a Majalisar Tsaron MDD bisa matsayar haɗin kan Afrika, wato Ezulwini Consensus. Ya ce Shettima zai kuma bayyana sabbin manufofin Nijeriya na rage hayaƙin da ke gurbata muhalli bisa yarjejeniyar Paris.

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi Shettima Ya Bada Umarnin Gaggauta Raba Lamunin Naira Biliyan 250 Ga Ƙananan Manoma 

A yayin da aka tarɓe shi, Shettima ya samu rakiyar ministoci da gwamnoni ciki har da na Kaduna, Uba Sani, wanda ya ce halartar Nijeriya a UNGA zai ƙara jawo masu zuba hannun jari ga tattalin arzikin ƙasar, musamman a fannin ma’adanai, da noma da ilimin sana’o’in dogaro da kai. Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Dr Olajumoke Oduwole, ta ce Nijeriya za ta yi amfani da taron wajen tallata shirin Nigeria Investment Day, da zai mayar da hankali kan ma’adanai, da sadarwa da kuma fasaha.

Rahotanni sun nuna cewa Shettima zai kuma shiga taron kwamitin zaman lafiya na Tarayyar Afrika, tare da ganawa da shugaban gwamnatin Sudan da sauran manyan jami’ai, domin jaddada matsayar Nijeriya kan rikicin Gabas ta Tsakiya, Sudan da gabashin Kongo. Wannan dai na nuna yunƙurin Nijeriya na ƙara taka rawar gani a harkokin diflomasiyya da ci gaban nahiyar Afrika.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Nijeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro November 6, 2025 Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu  November 5, 2025 Manyan Labarai ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya November 5, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa
  • Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
  • Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil
  • An Kaddamar Da Taron Kolin Wuzhen Na Ayyuka Masu Nasaba Da Yanar Gizo
  • Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
  • An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an
  • Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama
  • Iran, China da Rasha sun tattauna gabanin taron Kwamitin Gwamnonin IAEA
  • Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE