Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan Amurka
Published: 20th, November 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya da “kisan kiyasin Kiristoci” tare da barazanar tura sojojin kasarsa, sun kara wa wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda kaimin kai hare-hare.
“Kalaman da Amurka ta yi kwanan nan sun kara wa wasu ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke son amfani da labaran ƙasashen waje kai hare-hare kan wuraren da ba su da kariya kaimi,” in ji Akume a ranar Laraba.
Yayin da yake magana kan yadda ta’addanci, hare-haren ’yan bindiga da matsalolin tsaro ke ci gaba da sauyawa a ƙasar, Sakataren Gwamnatin ya ƙara da cewa: “Kafin waɗannan kalaman, an riga an raunana ƙungiyoyin ta’addanci sosai, kuma sun rage kai kananan hare-haren daji. Wannan dawowa ya nuna muhimmancin haɗin gwiwa, ba wai Magana kawai ba, tsakanin Najeriya da Amurka.”
Trump, a jerin sakonnin da ya wallafa a shafin X tsakanin 30 ga watan Oktoba da 1 ga Nuwamba, 2025, ya ayyana Najeriya a matsayin “Ƙasa mai Matsala ta Musamman” saboda zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi.
Shugaban Amurka ya yi gargadin cewa zai iya tura sojojin Amurka zuwa Najeriya idan kisan da ake zargin bai tsaya ba.
Ya ce tuni ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta kasar da ta fara shirin yiwuwar daukar matakin soja idan tashin hankali ya ci gaba.
Trump ya kuma yi barazanar dakatar da dukkan taimakon Amurka ga Najeriya idan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kasa magance abin da ya kira zaluntar Kiristoci.
A cikin jawabin da SGF ya yi a ranar Laraba, ya ce an riga an raunana cibiyoyin ta’addanci sosai kuma sun rage zuwa kananan hare-haren daji kafin waɗannan kalaman.
“Wasu ƙungiyoyi yanzu suna ƙoƙarin amfani da waɗannan kalaman don samun suna,” in ji shi.
Idan za a iya tunawa a cikin makon nan ne dai wasu ’yan bindiga suka sace dalibai 25 a makarantar sakandaren kwana ta GCGSS Maga da ke jihar Kebbi.
Kazalika, a cikin makon kuma ta wasu maharani sun farmaki wasu masu ibada a wani coci da ke Eruku a jihar Kwara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: matsalar tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Cibiyar fasaha ta kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin ’yan kasuwa mata a Jihohi 3
Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya.
Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano, tare da tallafin Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU).
Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’Da take jawabi a wajen kaddamarwar a Kano ranar Talata, shugabar cibiyar, Maryam Lawan Gwadabe, ta ce an kirkiro shirin ne domin samar wa mata amintaccen muhallin da za su yi amfani da shi wajen bunƙasa kasuwancinsu.
Ta ce shirin zai gudana a jihohin Kano, Katsina da Sakkwato domin ƙarfafa tattalin arzikin mata da kuma tabbatar da sun samu dogaro da kai.
“Mun sanya wa shirin suna Women Venture Studio domin tabbatar da cewa mata za su ji daɗin kasancewa a cikin muhalli mai tsaro. Masu ba da shawara a nan su ne ’yan kasuwa da matan da suka yi nasara, waɗanda za su saurara, su jagoranta, kuma su tallafa wa mahalarta shirin,” in ji ta.
Maryam ta ƙara da cewa cibiyar tana bayar da wuraren yin aiki na zahiri da na intanet, domin tabbatar da cewa ana damawa da mat aba tare da an ware su ba.
Shugabar cibiyar ta kuma ce matakin farko na shirin zai haɗa da horar da mata 150, wato mata 50 daga kowacce jiha.
Ita ma da take jawabi, Shugabar ANWE, Hafsat Sahabi Dange, ta ce shirin ya fi mayar da hankali kan mata a fannin kirkira, musamman a harkar dinka kaya, sana’o’in hannu da fasaha.
“Manufarmu ita ce mu sauya waɗannan kasuwancin zuwa tsarin zamani domin mata su iya yin gogayya, ba kawai a Najeriya ba, har ma a duniya. Wannan shiri zai shafi ’ya’ya mata da kuma mata ta hanyar amfani da kirkirarsu da kuma ƙarfafa musu tsarin kasuwanci a Arewacin Najeriya,” in ji ta.
A nata bangaren, wakiliyar Tarayyar Turai a Najeriya da ECOWAS, Inga Stefanovic, ta ce EU ta ware sama da Yuro miliyan 700 a matsayin tallafi domin tallafa wa ayyuka daban-daban a fadin Najeriya.
Ta jaddada cewa haɗin gwiwar EU da Najeriya ya shafi fannoni da dama ciki har da fasahar zamani, bunkasa tattalin arziki, dimokuraɗiyya, zaman lafiya da tsaro, lafiya, ilimi, samar da makamashi da kuma noma.