Hajjin 2025: Mun samu nasarori a Yobe — Mai Aliyu Biriri
Published: 25th, September 2025 GMT
Shugaban Hukumar Alhazzan Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya bayyana cewar sun gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin nasara da kwanciyar hankali.
Mai Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Laraba a tattaunawarsa da manema labarai a babban ɗakin taron Hukumar da ke garin Damaturu dangane da yadda suka gudanar da aikin hajjin bara.
Shugaban ya ƙara da cewa, duk da cewar sakamakon yanayin yadda lamurran rayuwa suke ga al’umma wadda ya kai da ba su samu damar cika yawan kujerun da aka bai wa Jihar ba, amma duk da haka kusan mahajjata 1098 ne suka samu damar sauke farali a Jihar cikin kujeru aƙalla 1960 da aka bai wa Jihar.
“A cewarsa dukkannin Alhazzan Jihar da suka je don sauke farali dukkannin su sun dawo gida cikin halin lafiya ba tare da an rasa Alhaji ko da ɗaya ba cikin ikon Allah, wadda wannan babbar nasara ce a gare mu.”
Ya yi kira ga dukkan al’ummar Jihar da ke da ƙudirin sauke farali a shekarar ta 2026 da su yi ƙoƙarin don zuwa fara ajiye kuɗaɗensu domin kuwa hukumar alhazzan ta ƙasa NAHCON ta sanar da ranar fara aika mata kuɗaɗen maniyyata zuwa ranar 8 ga watan wannan Oktoba da ke tafe wadda akwai buƙatar da masu ƙudirin da su ƙoƙarta don biyan kuɗaɗen su kafin ma lokacin, tunda ya zuwa yanzu akwai maniyyata sama da 100 da suka fara ajiye kuɗaɗen su.
Shugaban ya kuma miƙa godiyar su ga Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni bisa ga yadda yake jajircewa don ganin hukumar ta kai ga samun nasarar ayyukanta, da kuma yadda Gwamnan yake tallafawa maniyyata musamman wajen ba su kuɗaɗen hadaya kimanin Riyal 300 ga kowane maniyyacin Jihar da sauran buƙatu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An Wallafa Ra’ayoyin Shugaba Xi Kan Batutuwan Da Suka Shafi Mata Da Yara Cikin Karin Harsunan Waje
An wallafa wasu kundi 2 masu kunshe da ra’ayoyin shugaba Xi Jinping na kasar Sin kan batutuwan da suka shafi mata da yara da kungiyar mata ta kasar, da kuma ra’ayoyinsa kan karfafa zumunci da akidu da al’adun iyali, cikin harsunan Rashanci da Faransanci da Spaniyanci da Larabci, bayan irinsu da aka wallafa cikin harsunan Ingilishi.
Madabba’ar tattara bayanai da fassara ta kwamitin tsakiyar JKS ce ta wallafa kundin, wadanda ake sa ran za su taimakawa masu karatu na kasa da kasa kara fahimtar ra’ayoyin shugaba Xi da dabaru da shawarwarin da Sin ta gabatar game da daukaka daidaiton jinsi da raya dukkan harkokin da suka shafi mata a fadin duniya. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA