Shugaban EFCC ya bayyana a Aso Rock yayin da Tinubu ya gana da Ibas
Published: 25th, September 2025 GMT
Shugaban Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin da Shugaba Bola Tinubu, ya gana da tsohon shugaban riƙo na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok Ete Ibas (mai ritaya).
Ya fadar ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya gana da Ibas.
Tinubu, ya naɗa Ibas a watan Maris domin jagorantar jihar bayan rikicin siyasa da ya ɓarke tsakanin tsohon gwamna Nyesom Wike da wanda ya gaje shi, Siminalayi Fubara.
Domin shawo kan rikicin, Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a ranar 18 ga watan Maris, inda aka dakatar da Fubara, mataimakiyarsa da ’yan majalisar dokokin jihar.
Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun goyi bayan matakin a ranar 20 ga watan Maris.
Ibas, ya bar ofis a makon da ya gabata, yayin da Fubara da sauran masu muƙamai suka koma kan kujerunsu.
Sai dai wasu sun zargi Ibas da rashin kawo ci gaba a lokacin da ya jagoranci jihar na tsawon watanni shida.
Majalisar Dokokin Jihar Ribas, ta ce za ta binciki yadda ya kashe kuɗaɗen jihar a lokacin dokar ta-ɓaci.
Rahotanni sun nuna cewa jihar ta samu kusan Naira biliyan 254.37 daga asusun ƙasa daga tsakanin watan Maris zuwa Agustan 2025.
Haka kuma, an hangi Ministan Kuɗi, Wale Edun, a fadar shugaban ƙasa.
Sai dai babu tabbacin ko zuwan Olukoyede da Edun, na da nasaba da batun Jihar Ribas.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dokar Ta Ɓaci Fadar Shugaban Ƙasa Fubara Ganawa Siyasa watan Maris
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA