Aminiya:
2025-11-21@10:48:26 GMT

’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja

Published: 21st, November 2025 GMT

’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba.

Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an yi awon gaba da ɗalibai da dama yayin harin da aka kai makarantar.

’Yan bindigar da suka sace masu ibada a cocin Kwara sun nemi a ba su N3bn kafin sakin su Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi

Wata majiya daga ɗaya daga cikin coci-cocin Katolika a jihar ta tabbatar da lamarin, tana mai cewa har yanzu makarantar na kan tattara bayananta a kan harin.

“Eh, gaskiya ne, amma ba ni da ikon bayar da cikakkun bayani. Coci za ta fitar da sanarwa a hukumance daga baya a yau,” in ji shi.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai bayar da cikakkun bayanai daga baya.

Sai dai shugaban sashen bayar da agaji na ƙaramar hukumar Agwara, Ahmed Abdullahi Rofia, ya tabbatar da harin ta wayar salula.

Ya ce ’yan ta’addan sun kai hari kan makarantar ne tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na dare, yana mai cewa ba a kai ga tabbatar da adadin ɗalibai da malaman da aka sace ba tukuna, domin har yanzu hukumomi na ci gaba da tantancewa.

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan irin wannan hari a Maga, Jihar Kebbi, inda aka yi garkuwa da ɗalibai mata 25, abin da ya ƙara tayar da hankula kan tabarbarewar tsaro a makarantu a yankin.

Ko a ranar Alhamis, sama da makarantu 50 aka rufe a Jihar Kwara sakamakon barazanar ta’addancin ’yan bindiga.

Shugaba Bola Tinubu ya soke tafiyarsa zuwa kasashen Afirka ta Kudu da Angola domin jagorantar dakile matsalolin tsaron.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas Tayi Gargadi Game Da Kara Dagulewar Al’amura Bayan Harin Isra’ila A Gaza

a

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar gwagwarmaya Ta hamas ta yi gargadi game karuwar hadari bayan mutuwar falasdinawa guda 28 sakamakon harin da sojojin HKI suka kai a yankin Gaza, da hakan yake kara lalata yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakani.

Akwai yara guda 9 daga cikin wanda harin na isra’ila ya kashe a harin na jiya laraba, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta bayyana bayan mutane akalla 77 da suka jikkata,

Hamas ta karyata zargin cewa dakarunta ne suka fara bude wa sojojin Isra’ila wuta da ya kai ga sun kai harin, kungiyar ta bayyana zargin a matsayin shaci fadi, kuma isra’ila tana son fakewa da shi ne don kare hare haren da take kaiwa da ya ketar yarjejeniyar dakatar da bude wuta.

Dakarun sa kai na yankin gaza sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun kaddamar da hari a yankin Zaytun dake gabashin garin Gaza inda falasdinawa 10 suka mutu da suka hada da yara da mata. Haka shi ma ginin hukumar bada agaji ta majalisar dinkin duniya UNRWA dake kusa da gabashi shi ma ya fuskancin harin na isra’ila.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Labanon Ta Bukaci Gudanar Da Taron Kwamitin Tsaro Na MDD Cikin Gaggawa November 20, 2025 Achraf Hakimi Ya Zama Gwarzon Wasan Kwallon Kafar Afirka Na Shekara Ta 2025 November 20, 2025 Kasashen Iran Da Malesiya Sun Rattaba Hannu Kan Jarjejeniyar Fadada Dangantakar Addini November 20, 2025 Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 27 a wani sabon harin bam November 20, 2025 Iran : daftarin kudurin da Canada ta gabatar, siyasa ce da kin jininmu November 20, 2025 AU ta yi Allah-wadai da tsoma bakin kasashen waje a harkokin tsaron Afirka November 20, 2025 Amurka ta Shawarci Ukraine ta amince da yankunan da Rasha ta mamaye mata November 20, 2025 Sudan ta yaba da kokarin Amurka da Saudiyya na kawo karshen rikicin kasar November 20, 2025 Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar Iran Ta Ce: A Yanzu Babu Wata Tattaunawa Tsakanin Iran Da Amurka November 19, 2025 Sojojin Yemen Suna Da Makami Mai Linzami Da Babu Mai Makamancinsa Sai Iran November 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi
  • Hamas Tayi Gargadi Game Da Kara Dagulewar Al’amura Bayan Harin Isra’ila A Gaza
  • Cibiyar fasaha ta kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin ’yan kasuwa mata a Jihohi 3
  • Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya
  • ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’
  • DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace
  • Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi
  • Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa
  • Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi