CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI
Published: 22nd, September 2025 GMT
Hukumar da ke kula da yi wa Kamfanoni Rajista ta Najeriya (CAC) ta ƙaddamar da sabon shafin intanet mai amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira wato AI domin sauƙaƙa rajistar harkokin kasuwanci da kamfanoni a Najeriya.
Shugaban Hukumar, Hussaini Ishaq Magaji (SAN), ne ya bayyana a yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Kano ranar Litinin.
Ya kuma ce hukumar ta kawo sabbin sauye-sauye da za su inganta ayyukanta da kuma sauƙaƙa wa ’yan kasuwa yin rajista da ita.
Magaji ya ce, “Ko ina kake, daga dakinka, ba tare da ka san kowa a CAC ba, kuma ba tare da biyan kowa komai ba, za ka iya yin rajistar sunan kasuwancinka ka samu takardar shaidarka cikin ƙasa da minti 10.”
“Adadin bayanan da shafinmu na intanet ke ɗauka ya tashi daga 3.5TB zuwa kusan 12TB cikin watanni uku da fara jagorancin hukumar,” in ji shi.
Shugaban ya kuma ce hukumar na karɓar saƙon imel sama da 3,000 a kullum, yayin da ma’aikata ƙasa da 100 ke kula da su da kuma bayar da amsa.
Sai dai ya ce sabon shafin da aka ƙaddamar, zai karanta kuma ya rarraba tare da bayar da amsa ga dubban sakonnin na imel cikin daƙiƙa daya.
Ya kuma ce karfin aikin shafin wanda aka fara amfani da shi a watan Yuni ba shi da iyaka.
Hussaini ya ce, “Babu inda a duniya ake yin rajistar sunan kasuwanci cikin ƙasa da minti 10. Mu ne muka fara, sauran su biyo baya.
“A yau kaɗai, akwai aƙalla kamfanoni 7,000 da ke buƙatar a yi musu rijista, yayin da ma’aikata 63 ne kawai ke aikin. Wannan ne ya sa dole mu fara amfani da wannan fasahar domin inganta ayyukanmu,” in ji shi.
Ana sa ran shugaban hukumar zai gabatar da jawabi kan nasarorin da hukumar ta samu a fasahar a yayin taron hukumomin da ke kula da yi wa kamfanoni rajista na duniya da za a yi a ƙasar Tunisia wata mai zuwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano Kasuwanci
এছাড়াও পড়ুন:
Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe
Cin zarafin da Babban Jami’an tsaro (CSO) na Gwamnan Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba ya yi ga wakilin Talabijin NTA da ke Damaturu, Babagana Kolo a harabar Majalisar Dokokin Yobe da ke Damaturu a ranar Alhamis ya tada ƙura.
Lamarin ya faru ne yayin da wasu ’yan jarida ke jiran a shigar da su cikin zauren domin su bayar da rahoto kan gabatar da kasafin kuɗin 2026 da Gwamna Mai Mala Buni ya yi a gaban Majalisar Dokokin.
An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8 Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSCShaidu sun ce Babban Jami’in tsaro (CSO) na fadar gwamnatin Yobe, CSP Yakubu Zakari Deba, ya afka wa Kolo ya buge shi a fuska, lamarin da ya yi sanadiyyar raunuka a bakinsa da wasu ɓangarorin jikinsa.
An ruwaito cewa, lamarin ya kawo cikas ga yadda kafofin yaɗa labarai ke yaɗa labaran taron yayin da ‘yan jarida ke barazanar ƙauracewa gabatar da kasafin kuɗin.
Sai da Kwamishinan Yaɗa labarai, Alhaji Abdullahi Bego ya sa baki kafin ‘yan jaridar su ci gaba da ayyukansu.